Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Salam shin ya alatta mutum ya ringa skipping ya yin
yin rankon azummi? Misali kana yin shi Litinin da alhamis kuma ranko ne?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumussalaam Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh.
Babu laifi a kan hakan shi ne abin da mafi yawancin mallamai suka
tafi a kai wanda yake da ramuwa na azumin Ramadan ya yin da zai rama su, ba
dole sai ya yi su a jere ba, saboda faɗin Allah (SWT):
(فمن كان منكم مريضا أو على سفر فعدة من أيام أخر)
Wanda ya kasance daga cikin ku bashi da lafiya ko a
hali na tafiya to sai ya biya adadin a cikin wasu kwanuka na dabam.
-Haka an ruwaito daga Aisha Allah Ya kara mata yadda
tace da an saukar da àyar
(فعدة من أيام أخر متتابعات)
Sai aka goge kalmar (متتابعات)
-Haka an ruwaito hadisi daga Abdullahi binu Umar (RTA)
Ya ce manzon Allah(SAW) yace:
(أن النبي صلى الله عليه وسلم قال في قضاء رمضان إن شاء فرق وإن تابع)سنن الدارقطني.
Manzon Allah(SAW) ya ce: Wanda yake da ramuwa na azumi
idan ya so ya yi su a jere idan ya so ya yi su a rarrabe.
والله تعالى أعلم.
DR, NASIR YAHYA ABUBAKAR BIRNIN GWARI
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Fadakarwa a Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BJikpGm7VXV1vEVVGcNH5J
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.