Ticker

6/recent/ticker-posts

Liman Zai Iya Tambayar Mamu a Cikin Salla?

 Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Na ji wani Malami yana cewa Liman ze iya tambayan mamu cikin Sallah a kan abin da ya faru shi ne nake son ƙarin bayani??

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Hakane domin malaman fiqhu suna cewa aiki ƙarami baya ɓata sallah, hakama maganarda aka yita don gyaran sallah ita ma ba ta ɓata sallah. Akwai hadisin Zulyadaini wanda yana cikin Sahihul Bukhari da Muslim Annabi (s.a.w) ya yi sallar la'asar raka'a biyu se ya yi sallama se wani Mutum yai masa magana a kan cewa raka'a biyu ya yi. Annabi ya tambayi sauran sahabbai shin dagaske raka'a biyu nayi? Suka ce Eh, se yadawo yakara wasu raka'a biyun ya yi sujuda qabliyya 

To ka ga a nan ga shi an yi maganganu amma sallar kuma ba ta ɓaci ba shi ne wancan karatun da akai maka. Indai maganarda za'ayi tana cikin gyaran sallah ne ko kuma wata maganace kaɗan ba ma cikin gyaran sallar take ba kamar ka ga makaho ze faɗama abun da ze cutar da shi sekai masa magana ka ankarar da shi kuma ka ci gaba da sallarka sedai sujuda ba adi ta kamaka amma sallar taka lafiya lau.

Allah ya sa mu dace

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BJikpGm7VXV1vEVVGcNH5J

 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments