Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Auren Wacce Kishiyar Mamana Ta Shayar?

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Tambayoyi Da Amsoshi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Aslm' alkm. Ina yiwa malam fatan alkhairi, ina tambaya ne don Allah a kan idan matar mahaifina (Yadikkona) ta shayar da wata mata a gidanmu wanda ba ƴarta ba lokacin ma ni ba a auri mamata ba, toh zan iya auren wannan matar da aka shayar a gidan mu ko ta zama ƴar ƴar'uwata. Allah Ya kara basira da kuma Ikhlasi.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumus salam. Bai halatta ka aure ta ba, saboda da nonon mahaifinka aka shayar da ita, don haka ta zama 'yar'uwarka.

 

Allah Madaukakin Sarki ya haramta auran 'yar'uwa ta fuskar shayarwa a aya ta (22) a suratun Nisa'i.

 

Allah ne mafi sani.

 

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

 

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BD0aB20SWTB9hgHahFHb9M

 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments