Ticker

6/recent/ticker-posts

Annabawa Suna Iya Aikata Zunubai?

 Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Tambayoyi Da Amsoshi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam, na yi imani da kasancewar Annabawa dukkansu ma'asumai ne. Amma ga shi muna gani a Ƙur'ani Annabi Yunus (A.S.) ya yi laifi har Allah (S.W.T.) ya hukunta shi, haka nan Annabi Adam (A.S.). Tambaya ta a nan shi ne, ƙarin bayani a kan hakan?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Annabawa ma'asumai ne wajan kuskure a isar da manzanci, amma suna iya aikata ƙananan zunubai da kuskure. Sai dai Allah yana faɗakar da su take, ya kuma gafarta musu, kamar yadda ya faru lokacin da Annabi (S.A.W.) ya ce: A amshi fansa daga ribatattun Badar, daga baya Allah ya bayyana hakan kuskure ne, a Suratul Anfaal.

 

Aya ta biyu a Suratul Fatahi, ta tabbatar da cewa Allah ya gafartawa Annabi (S.A.W.) zunubansa waɗanda suka gabata da waɗanda za su zo nan gaba, sannan Allah ya zargi Annabi (S.A.W.) wajan aikata wasu abubuwan a wurare a cikin Alƙur'ani. Hakan sai ya nuna Annabawa suna iya faɗawa cikin ƙananan zunubai, amma Allah yana faɗakar da su a lokacin da abin ya faru, ya kuma gatarta musu.

Annabawa ma'asumai ne, ba sa aikata manyan laifuka

 

Allah ne mafi sani

 

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

 

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BD0aB20SWTB9hgHahFHb9M

 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments