𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne hukuncin amfani da makilin din goge haƙora, da kuma madigin kunne (magani), dana hanci, dana ido, ga mai azumi? Kuma idan mai azumi ya ji dandanonsu a cikin maƙogoronsa me zai aikata?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Tsaftace haƙora da makilin baya karya azumin mai azumi, saboda hukuncinsa kamar yin aswaki ne, Sai dai kuma wajibi ne akansa ya kiyaye silalewan wani abu zuwa cikinsa, Amma inda wani abu zai rinjaye shi ya shiga cikin cikinsa ba tare da nufi ba to babu ramuko akansa.
Haka maganin digawa a ido da kunne azumi baya karyewa in an diga su a zancen da yafi inganci daga zantukan maluma guda biyu, Saidai kuma in har ya ji ɗanɗanon abubuwan da ya diga a makogoronsa to ya rama wannan azumin yafi tsentseni a gare shi, tare da cewa yin hakan ba wajibi ba ne a kansa, saboda kasancewar ido da hanci ba kafofi ne na shigar da abinci da abin sha ba.
Amma maganin da ake digawa ta hanci to shi kam baya halatta;
saboda kasancewar hanci mashiga ne na abinci, don haka ne Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ke cewa:
«وَبَالِغْ فِي الِاسْتِنْشَاقِ إِلَّا أَنْ تَكُونَ صَائِمًا».
Ma’ana: “Kuma ka kai maƙura wajen shaƙar ruwa a hanci saidai in ka kasance mai azumi”. Kuma wajibi ne ga mutumin da ya aikata hakan ya rama azumi, saboda wannan hadisin da wadanda suke da ma’ana irin tasa, matukar ya ji ɗanɗanon abun da ya diga a cikin makogoron nasa, Allah shi ne majibincin dacewa.
WALLAHU A'ALAM
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da
Fadakarwa a Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.