Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Da Ta Sha Azumi Saboda Juna-Biyu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu

Mallam. Allah yaƙara maka lafiya da imani yakarɓi ayyukan ka yajiƙan mahaifanka. Malam matatace tasamu junabiyu a cikin azumin da yagaba ta Tasha azumi takwas sakamakon wahalar datasha Saboda na farkone batasamu ta ramaba haryanzu gashi ta haihu ga shayarwa. Yanzu ya za ta yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Idan mai ciki ko mai shayarwa ta ajiye azumi saboda tsoro bisa kanta ko tsoro bisa abin da take dauke da shi ko take shayarwa, to Imamuna Malik ya ce mai ciki za ta rama azumin ne duk sanda ta samu damar ramawar bayan ta haihu. Ita kuma mai shayarwa za ta haɗa da ramuko da ciyarwa.

 

Amma akwai wata fatwar daga Sayyiduna Abdullahi bn Abbas da Abdullahi dan Umar sun ce mai ciki ko mai shayarwa za ta ciyar da miskini guda ne bisa kowacce ranar da tasha azumin, wato ciyarwa za ta yi ba sai ta rama ba.

Don Ƙarin bayani aduba Rahmatul Ummah shafi na 113 a cikin Kitabus Siyam.

WALLAHU A'ALAM.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments