Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Za Ta Rama Azumin Da Ke Kanta Saboda Jinya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam fatan an wayi gari lafiya, ya akaji da jama'a? Allah ya taimaka.

Malam don Allah a taimaka amin Ƙarin haske game da lamarin nan. Nice nasha azumin Ramadan na shekara biyu ma'ana na farko nasha guda tara sanadin juna biyu da nake dauke da shi lokacin na kusa haihuwa sai yake bani wahala shi ne nasha guda tara da niyyar idan Allah ya saukeni lfy sai na biya. To bayan na haihu sai Allah ya jarrabeni da wata irin jinya mai wahala nakai tsawon lokaci a cikin wannan hali to Malam har wata ramadan din ta dawo ban iya biya ba. A cikin azumin bara sai abun ya ƙara tabani sosai ban samu na yi azumi ko daya ba, to har zuwa yanzu Malam lafiyar dai sai a hankali ce. shi ne nake so amin cikakken bayani game da wadannan azumi da suke kaina ta yaya zan biyasu?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuh.

Da farko ina fatan Allah shi baki lafiya, ya sa kaffarah gareki cikin jinyar da ke damunki.

1. Akwai saɓanin malamai game da hukuncin matar da tasha azumi sanadiyyar goyon ciki. Amma saboda larurar da kike ciki sai ki dauki fatawar Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (Allah ya yarda dashi) shi awajensa idan mace mai jun biyu tasha azumi, za ta ciyar da miskini guda ne bisa kowanne azumin da tasha. Don haka za ki ciyar da miskinai tara ke nan.

 

2. Azumin da aka sha ta dalilin zafin jinya, babu makawa sai an ramashi da zarar an samu lafiya. Sai dai idan likitoci masanan jinyar sun duba sun tabbatar da cewa majinyacin ba zai warke ba (wato ba a tsammanin warkewarsa) to shi ke nan wajibcin yin ramukon ya sauka daga kansa. Sai a ciyar da miskini maimakon kowanne wuni guda da aka sha.

 

Don haka za ki jira duk lokacin da Allah ya baki lafiya sai ki rama. Idan kuma likitocinki sun tabbatar miki da cewa ba sa tsammanin warkewar jinyar, to ciyar da miskini za ki yi bisa kowanne azumi guda. Wato miskinai talatin ke nan.

 

WALLAHU A'ALAM.

 

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments