Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mai Jegon Da Ake Bin Ta Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salamun alaikum. Allah shi gafarta Malam ina da tambaya kamar haka wato iyalina ne ake binta azumi guda goma sha takwas na azumin bara da ya wuce saboda larurin samun sabon juna da ta yi a wancan lokacin. Yanzu kuma gashi ta haihu tana shayarwa, kuma tana so ta rama azumin, shin ko za ta iya ciyarwa a madadin azumin? Idan za ta iya ciyarwa kuma ta yaya za ta ciyar? Wassalam na gode Malam.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Idan har za ta iya ramawa yanzu, ba tare da ta chutar da kanta ko jaririnta ba, to ta rama ɗin shi ne zai fi.

Idan kuma har yanzu tana tsoron ramawar saboda yanayin shayarwa, to za ta jira har lokacin da jikinta zai yi karfi sannan ta rama ko da bayan wucewar wannan Ramadan ɗin mai zuwa ne.

 

Kuma Bisa Mazhabin Imamu Malik (rah) duk mutumin da azumi ya shekara akansa bai rama ba, har wani Ramadan ɗin ya zo ya wuce, to idan ya tashi ramawa sai ya haɗa tare da ciyarwa.

WALLAHU A'ALAM.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments