Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Jan Carbi A Musulunci

Jan carbi ba bidi'a ba ne, saboda duk da cewa babu shi a zamanin Manzon ALLAH {s.a.w} hakan ba zai sa ya zama bidi'a ba. Saboda wanda yake amfani da shi ba yana nufin cewa ibada ce mai zaman kanta, mai jan carbin yana amfani da shi ne, don ya kiyaye adadin zikirinsa.

 Yin amfani da 'yan yatsu shi ne ya fi, saboda hadisi ya yi nuni cewa: za a basu dama su yi magana, ranar alƙiyama, kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: 3486.

 Don haka za su yi maka shaidar abin da ka yi na alkhairi dasu, saɓanin carbi.

 Sannan sauda yawa za ka ga mutum yana jan carbi amma hankalinsa yana wani wajen saɓanin idan da hannu yakeyi.

Jan carbi yakan iya sanya wasu su yi riya, saboda wasu suna ratayawa ne a wuya don a gane su zakirai ne.

 Manzon ALLAH {s.a.w} yana yin tasbihi da hannunsa na dama kamar yadda ya tabbata a hadisin Abu Dawud mai lamba ta: 1286, wanda Albani ya inganta.

 Sai dai wasu malaman suna cewa inya yi da hagu ma ya yi, tare da cewa yi da dama shi ne yafi.

 Sai dai duk da dalilan da suka gabata, mutum zai iya jan carbinsa, tun da jan carbi ba ibada ce mai zaman kanta ba, balle

ace ya zama bidi'a tare da cewa yi da hannu shi ne yafi.

 Don neman ƙarin bayani duba: Majmu'ul fatawa 22\187.

Ko Lika'ul maftuh na Ibnu-uthaimin 3\30.

ALLAH ne mafi sani.

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments