Farko dai zina saɓon ALLAH ce da kuma yaɗa fasadi a doron ƙasa.
Aure kuwa sunnar Manzon ALLAH {s.a.w} ce da samar da zuriya mai albarka.
Kuma an kwaɗaitar damu yin sa.
Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi
zina da ita sai ta yi jini ɗaya wanda ake kira
Istibra’i, kafin a ɗaura mata aure domin a raba maniyyin zina da na aure.
Kuma idan har an ɗaura aure ba ta yi wannan jinin ba, to za a raba wannan auren ko da sun haifi `ya`ya, domin suna ganin an ɗaura auren ne a cikin idda, kuma
ALLAH Ya hana ɗaura aure a cikin idda.
Saboda haka, a wurinsu wannan auren ɓatacce ne kuma rusasshe ne.
Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam Shafi`i suna ganin macen
da ta yi zina, anso ta yi istibra’i kafin ta yi aure,
amma idan har an ɗaura auren ba ta yi istibra’i ba, auren yana nan
daram, ba za a raba su ba.
Kuma suka ƙara da cewa ko da tana da cikin zina ne aka ɗaura mata aure, to auren yana nan.
Sai dai Imam Abu Hanifa ya ce:
Mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan
ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.
Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce: Duk wanda ya yi imani da ALLAH da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa.
[Abu Dawud:1847]
Don neman ƙarin bayani a duba:
AL-MUDAWWANNAH AL-KUBRAH 2\173.
Ko Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79.
Abin lura a nan
shi ne fatawar Malikiyya tafi inganci kafin a yi auren, saboda fita daga saɓanin malamai, sannan kuma za
a
kaucewa faɗawa haɗari,
Amma idan an
riga an yi auren to fatawar Hanafiyya abar lurace, saboda akwai banbanci
tsakanin zina da aure, sai dai ya wajaba su nisanci saduwa, kafin ta haihu
Saboda hadisin da ya gabata.
ALLAH shi ne mafi sani.
**************************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.