Ticker

6/recent/ticker-posts

Hani Game Da Yin Azumin Nafila Daf Da Shigowar Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Aslm Alaikum Mlm na kasance ina yin Azumin litinin da Alhamis duk sati. Jiya litinin bayan na sha ruwa sai yarinyata take cemin wai ba kyau yin Azumi idan Ramadan ya kusa sai na ce mata har na Nafila sai ta ce min wai eh. Dan Allah meye gaskiyar wannan maganar. Bissalam ALLAH ya taimaki mlm.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu

Manzon Allah S.A.W Ya ce: "Kada Dayan ku ya yi Azumin Kwana Ɗaya Ko Biyu, Idan Ya zama Daf Da Ramadana, Sai dai Idan Mutum Ya Saba Yana Yin Wani Azimin sa, To Shi Ya Halatta ya yi.

Bukhari.

 ➡️Ma'ana Sai Idan Ya Dace Da Wani Azumi Mutum Ya Saba Yi, Kamar Azumin Nafila, Ko Litinin Da Alhamis Da Azumin Annabi Dawud, ka yi Yau, Gobe Ka Huta, Ko Azim Kwana 3 A Kowanne Wata, Dan Haka Hanin Ya Shafi Wanda Ba Ya Yin Waɗannan Ne.

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BD0aB20SWTB9hgHahFHb9M

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments