Ticker

6/recent/ticker-posts

Kada Ka Karaya Duk Yawan Zunubinka

Daga Anas (R.A) ya ce:

Na ji Manzon ALLAH {s.a.w} yana cewa:

 ALLAH Maɗaukakin Sarki ya ce:

Ya kai ɗan Adam, haƙiƙa muddin ka roƙeni, kuma ka ƙaunace ni, zan gafarta maka abin da yake kanka, kuma ban damu ba.

 Ya kai ɗan Adam da dai zunubinka ya kai tsats-tsakin sama sannan ka nemi na gafarata maka, zan gafarta maka.

 Ya kai ɗan Adam haƙiƙa da za ka zo min da zunubi cike da ƙasa sannan ka haɗu dani, baka yi shirka dani da kowa ba, to da nazo maka da gafara cike da ita.

[Tirmizi ne ya rawaito shi].

Wannan hadisi yana mana nuni da girman Rahmar ALLAH ga bayin sa.

 Yana kuma mana nuni da girman shirka da illarta ga ɗan Adam, domin ALLAH yana yafe ko wanne laifi ban da shirka, mutuƙar bawa bai mutu yana mai shirka ga ALLAH ba, to duk yawan zunubansa in ALLAH yaso sai ya gafarta masa ya sashi a Aljannah.

 Sannan kuma duk irin aiki da ka ga wani yana aikatawa kada ka yanke masa hukunci, ka jefa shi wuta, alhali kai ma bakasan naka ƙarshen yaya zai kasance ba.

 Saboda haka duk yawan zunubinka kada ka fitar da rai da Rahmar ALLAH, ka yawaita tuba, ka kuma yi ƙoƙari wajen nisantar zunubin domin bakasan a kan wanne aiki za ka mutu ba.

 Mu yawaita neman gafarar ALLAH a ko da yaushe lallai ALLAH mai gafara ne, komai girman zunubi ALLAH yana gafarta shi mutuƙar ba shirka bace.

ALLAH ka hani zuƙatanmu da saɓa maka, ka nesantamu da aikata ayyukan zunubi, ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments