Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'a Bayan Sallar La'asar A Ranar Juma'a

 Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalmu alaikum, malam  Allah ya karamaka lafiya da imani, tambaya ta shine adu'ar da akeyi bayan la'asar a ranar juma'a za'a iya lafila ne Sai ayi adu'ar ? na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ba'a yin sallar nafila bayan sallar la'asar har zuwa faduwar rana. Abin da mafi yawan mallamai suka fassara wannan hadisin Daga Abu Huraira (R), Manzon Allah (SAW) ya ambaci ranar Juma'ah, sai yace: "a cikinta akwai wata sa'a, ba wani bawa musulmi da zai dace da ita yana sallah yana rokon Allah wani abu face sai Allah Ya bashi shi",shine, Sallah da aka ambata a hadisin yana nufin: Zaman jiran sallah, kamar mutum ya zauna bayan la'asar yana jiran magriba tayi, manzon Allah (SAW) yace: Dayan ku ba zai gushe ba yana cikin sallah; matukar yana zaman jiran sallah" Bukhary

Ko kuma wanda ya shiga masallaci bayan sallar la'asar zaiyi tahiyyatul masjid (gaisuwar masallaci) kafin ya zauna shima sallah ne.

 

Ko kuma sallah a hadisin ana nufin ma'anarta ta lugar larabci, wato addu'a da kaskantar da kai ga Allah

والله أعلم.

SHAIKH NASIR ABUBAKAR SALIH

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DVpHjgfRdK9IRWvkB23lbE

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments