Ticker

6/recent/ticker-posts

Tik-Tok Da Rayuar Hausawa: Samu Ko Rashi

Muƙalar da aka gabatar a ajin ALH 400 (Seminar), a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau, Jahar Zamfara, Nijeriya, (Disamba 2022 - Janairu, 2023).

AMINU ISMAIL ADAM

07082704202
ismailaminu180@gmail.com

Tik-Tok Da Rayuar Hausawa: Samu Ko Rashi

Tsakure

Hankalin wannan aikin za ta karkata ne a kan manhajar TikTok. Kasancewar TikTok wata kafa ce ta zamani dake taka muhimmiyar rawa a rayuwar al’ummomi dabandaban a faɗin Duniya. Haka suma Hausawa ba a bar su a baya ba wajan amfani da wannan manhaja domin suma su baje hajojinsu kamar sauran al’ummomin Duniya. Wannan dalilin ne yasa wannan aikin zai dubi amfani da rashin amfani, cigaba ko cibaya da al´ummar Hausawa ta samu a cikin wannan manhajar. A yayin gudanar da wannan aikin, an yi amfani da wasu hanyoyi tattara bayanai da suka haɗa da: karance-karancen maƙalu, bincike a yanar gizo, buɗe shafi a manhajar domin lura ta hanyar gani da ido.        

1.0 Gabatarwa

Al’ummar Hausawa al‘ummac ce dake zaune a arewa maso yammacin tarayyar nijeriya da kuma kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Haka kuma al‘umma ce mai dimbin yawa, sun bazu cikin ƙasashen Afrika ƙasashen larabawa da kuma sauran sassan Duniya baki daya.Haka kuma Hausawa ba a barsu a baya ba wajan tafiya da zamani domin su na amfani da intanet musamman kafafan sada zumunta wato (soshal midiya) wajan fito tare da yaɗa abun da ya shafi al‘adunsu da ma abin da ya shafi rayuwarsu baki daya.

Manhaja ‘’TIKTOK’’ na daya daga cikin jerin manhajojin da Hausawa suke amfani da shi a wannan lokacin da muke ciki hasalima yana ɗaya daga cikin manhajojin da tauraron su ke haskawa a Duniyar intanet.Wannan ne yasa aikin zai yi duba da me ake nufi da tiktok amfanin sa da matsalolin sa tare da gano cewa shin tiktok a gurbin rayuwar Bahaushe samu ne ko kuma rashi.

 

1.1     Ra’in Binike

An ɗora wannan aiki ne akan ra’in ‘’Cultural Sustainability Theory’’ (Ra’in Adana A’ladu da Ci Gaban Al’umma). Wannan ra’in yana bayani ne kan hanyoyin adana ko inganta al’ada domin ci gaban al’umma.

Gusau (2015:55) ya kira makarantar da ta fito da irin wannan ra’in da suna ‘’Mazhabar Adana Al’adu’’. Shi kuwa Shu’aibu (2013:78) ya kira makarantar da ke da da’awar irin wannan ra’in na adana al’adu da sunan ‘’Mazhabar Muhafaza’’. Saboda haka duba da irin manufofin wannan ra’in ne ya sa aka ɗora wannan aikin akan sa domin shima aikin ya danganci al’adu.

1.2     Dabarun Gudanar da Bincike

Dabarun binciken sun haɗa da: bincike a yanar gizo, amfani da bugaggun litattafai , bitar ayyukan da suka gabata (karance-karancen makalu), da kuma buɗe shafi acikin manhajar domin lura da ido na kai da kai.

2.0     Intanet

Kalmar intanet baƙuwa ce a fannin nazarin Hausa (Mukoshy, 2015:19).Asalin kalmara Ingilishi ita ce ‘’Internet’’. Masana da mazarnata da dama sun yi ƙoƙarin ba da maanar intanet da cewa:

Intanet kafa ce wadda ta haɗa bayanai dabandaban, kuma an sauƙaƙa hanyoyin amfani da waɗannan bayanai kowa zai iya miƙa hannanyansa a kowane lokaci a ko’ina (Umar, 2012:48).

Mukoshy, (2015:20) cewa yayi Intanet kafar sadarwa ce ta na’urorin zamani wadda ta game duk Duniya.Tana ba da damar sadar da bayanai kowaɗanne iri kuma zuwa ko’ina a Duniya ckin ɗan ƙanƙanin lokaci.

Falsafar intanet Intanet tana da muhimman ɓangarori cikin su akwai Imel (E-mail), shafukan yanar gizo (Web), shafukan sada zumunta (Social Networking Sites), wassani da shakatawa a yanar gizo (Online Gaming) da kuma software update. Amma duk cikin waɗannan ɓangarorin da intanet ke ɗauke da su, wannan aikin zai mayarda hankali ne a kan ɓangaren shafukan sada zumunta (social networking sites).

2.1     Shafukan Sada Zumunta (social networking sites)

A mahangar kimmiyar sadarwa na zamani, idan aka ce ‘’social networking’’ ana nufin dandalin shakatawa da yin abota. Amma Farfesa Kerric Harvey ya bada gamammen tarifi ya ce ‘’kalmar social media (SM), social networking sites (SNs), social media websites (SMWs) na nufin wasu shafuka ne ko manhajoji da ake amfani da su a yanar gizo domin sadarwa tsakanin mutane da musayar ra’ayoyi ta hanyar sauti (voice note), hotuna (images), da kuma bidiyo (video).

Nau’ika Da Rabe-raben Shafukan Sada Zumunta

A matakin farko zamu iya kasa shafukan sada zumunta kashi uku ta fuskar damarmakin da suke bayarwa su ne kamar haka:

1.     Akwai waɗanda suke tura saƙonni da dukkan nauinsa (post-based social

2.     media) kamar myspace, fesbuk (facebook) , tiwita (tiwitter) was’af (whatsapp).

3.     Akwai kuma waɗanda aka gina su akan karɓa da tura hotuna (image based social media) su ne kamar Instagram, snapchat, da kuma tumble.

4.     Akwai kuma waɗanda suka kamar Gidajen telebijin (video based social media) kamar TikTok, Youtube, Vimeo, Skype.

Haka kuma akwai wasu masu keɓantattun manufofi da aka ƙirƙira domin wasu buƙatu na musamman, kamar waɗanda aka ƙiƙira domin masu karatu da nazari kamar irin su Wattpad, Goodreads, Academia.edu da dai sauran su. Amma hankalin wannan aikin gaba ɗaya ya tattare ne akan ɗaya daga cikin waɗannan nau’ikan ne na soshal midiya wato TikTok.

3.0     TikTok

TikTok wata kafa ce ko manhaja da ake amfani da ita wajan yin bidiyoyi marasa tsawo wanda tsayinsu ba ya wuce daƙiƙa sha biyar ba zuwa minti daya. Haka kuma an ƙaddamar da wannan manhajar ne shekarar 2016 ƙarƙashin wani kamfanin fasaha da ke ƙasar Chana mai suna Byte Dance.Wanda yake tana nan a kasuwanni 150 na duniyar intanet. Haka kuma tana da ofisoshinta a garuruwa kamar su Beijin, Los Angeles, Moscowo, Mumbai, Seoul da kuma Tokyo.

Haka kuma manhajar ta kasace matattara ce da ake amfani da ita wajen yaɗa tallace-tallace, samar da nishaɗi da suka shafi wasanni da sauransu. Kuma tana da masu amfani da ita da ƙiyasinsu ya kai mutum biliyan ɗaya a faɗin Duniya.

Mafi yawa masu amfani da shafin TikTok matasa ne masu neman nishaɗi wato ko su nishaɗantar ko kuma su nishaɗantu. Shi ya sa ma kusan duka bidiyo da ya ke wannan shafin yana ɗauke da waƙa ko rawa ko kwaikwayo ko kuma duka.

3.1     Amafanin TikTok Ga Rayuwar Hauwa

Shafukan sada zumunta kamar takobi ce sai yadda aka sarrafata wajan alkhairi ko akasin haka, kowa da irin manufa da dalilinsa na amfani da wannan dandali.TikTok na ɗaya daga cikin dangi na dandalin sada zumunta kuma shima yana da irin nasa amfanin ga rayuwar al’umma. Kuma su ne kamar haka:

1.     Ilmantarwa: wannan yana nufin ta hanyar TikTok ana ilmantar da mutane karatun addini da na zamani domin akwai shafukan da ake amfani da su domin yaɗa karattukan mallamai na addini da kuma waɗanda ake amfani da su domin karantar da fasahar zamani da harshen Hausa domin karin fahinta.

2.     zamani. Tallace-tallace: wannan yana nufin ana amfani da wannan manhaja domin tallata hajojinsu na sha’anin kasuwanci wanada yake hankan yana haɓaka tattalin arzikin mutum da ma al’umma baki ɗaya.

3.     Isar da saƙo da wuri: ta hanyar wannan manhaja saƙon da ake buƙata mutane su sani kuma su yi amfani da shi nan ta ke yana isa ne da wuri sabila da cewa yanzu hankalin mutane gabaɗaya ya tattare ya koma kan wannan mahaja na TikTok domin kuwa shi vidiyo ne buɗewa kawai za su yi su saurara ba karantawa ba.

4.     Raya al’adun jama’a: Ta hanyar wannan manhaja ana bayyanar wa jama’a irin al’adun su kamar abincinsu, tufafinsu, da kuma harkokinsu na yau da kullum kamar kasuwancinsu yanayi abubuwan da ya shafi hidimominsu da ya shafi bukuwa na aure da kuma naɗin sarautu.Haka kuma yana adana su domin duk abin da aka saka matukar ba da gangan aka goge shi ba to zai zauna tsawon.

3.2 Matsalolin Ga Rayuwar Hausawa

Kasancewar akwai masu amfani da wawannan manhaja ta hanyar da bai ace da rayuwar Hausawa ba, hakan ya jawo wasu matsaloli kamar haka:

1.     Gurɓata tarbiyya: wannan yana nufin yadda wasu ke amfani da wannan kafa domin ɗura vidiyoyin ana rawa a bainar jama’a ko kuma vidiyoyin batsa da ake yaɗawa wanda yake yara ƙanana suke kalla batare da sanin iyayensu ba.

2        Ɓata lokaci: wannan yana nufin yadda mutane ke ɓata lokacinsu wajan kallon abin da bashi da amfani fiye da abubuwa masu amfanin misali idan mutum ya zo kan vidiyon da ake rawa ko waƙa yafi tsayawa ya mayar da hankali ya kalla fiye da vidiyon da ya danganci nasiha ne ko wa’azi ko kuma abun da shafi karatun zamani.

3        Yaɗuwan auren jinsi: ta hanyar wannan kafa ta TikTok masu yin maɗigo suke fitowa su yi tallan kansu wani lokaci ma su fito suna ciwa junansu mutunci a bainar jama’a wanda yake da mutane ba su san da su ba. Amma a sandiyar TikTok wannan ɗanyan aiki sai kara yaɗuwa yake yi a tsakanin al’umma , auren jinsi abu ne wanda ya saɓawa al’adar Hausawa da ma addininsu baki ɗaya.

4        Faɗace-faɗace: wannan yana nufin yadda zaka irin ƙa ganin mutane mussaman ‘yanmata suna fitowa suna faɗace-faɗace ko akan samari ko kuma wani abun Duniya wanda yake a Baushiyar al’ada ana son a sami mace da kamun kai ba hayaniya ba.

5        Gurɓata al’ada: wannan yana nufin irin shigar da ake yi kafin ayi wasu bidiyon da ake ɗurawa yasaɓa da yanayin shigar asali na al’adar bahaushe. Misali; maimakon mace ta saka kayan da ba zai nuna wani ɓangare na zamani wanda yake a haka wani lokaci za’a manta wasu sashen abincin da asalin al’umma ke da su.

6        Rashin kwaɓa: wannan yana nufin matasa sun mayar da wannan dandali wajan baje kolin duk wasu abubuwan rashin kunyarsu ba tare da wani yayi wa wani faɗa ba ko kuma kai ƙara (report) kamar yadda wasu kafafen sada zumunta suke yi donmin ɗaukar mataki idan karar mutum ko shafi yayiwa.

7        Izgili wa addini: wannan yana nufin yadda wasu ke amfani da wannan kafa jikintaba kafin tayi bidinyon da zata watsa sai kawai tayi shi wani lokaci ma kanta ko ɗankwali babu. Haka kuma wani lokaci mai makon a rinƙa nuna salon girke-girken iyaye da kakanni sai a fi mayar da hankali wajan koyar da ire-iren girke-girken suna yi wa mallaman addini izgilanci da cin mutuncinsu saboda ko sun yi maganar da bata yi musu daɗi ba ko kuma yadda za su yi wata magana daban amma kuma a juyar musu da ma’ana a koma zolaya da izgili wa wannan maganar ta su.

8        Yaɗuwar bidiyoyin batsa: Ta hanyar wannan manhajar an samu ƙarin yaɗuwar bidiyoyin batsa wanda hakan bai dace da tarbiyar Hausawa ba. A wannan ya biyo baya ne dalilin cewa manhajar asalin ta an ƙirƙire ta ne domin haɗa bidiyoyi da kuma yaɗa su.

9        Sabo da kallace-kallace: wannan yana nufin da mutane ke komawa su ta’allaƙa rayuwarsu da mayar da hankalinsu gabaɗaya da manhajar wanda hakan yana taimakawa wajan hana su gudanar da wasu abubuwa muhimmai. Hakan yafi zama ila ko barazana ga rayuwar matasa domin yana hana su mayar da hankali ga muhimman abubuwa kamar karatun da sana’o’in su, haka kuma yana iya zama barazan ga lafiyar idanu.

4.0     Sakamakon Bincike

Sakamakwan wannan bincike ya tabbatar da cewa TikTok a gurbin rayuwar Hausawa rashi ne dalili kuwa shi ne a binciken aka gudanar ya nuna cewa yawan matsalolin da yake haifarwa ya fi alfanunsa yawa a rayuwar Hausawa. Sabila da haka ne wannan bincike yake ganin cewa akwai wasu hanyoyin da idan aka bi su to za a samu nasarar kawo gyara, kuma waɗannan hanyoyi su ne kamar haka:

1        Iyaye su rinƙa lura da irin abubuwan da yayansu ke kallo a wannan kafar da ma ire-irenta.

2        Mallamai su cigaba da yin nasiha wa al’uma iyakar iyawansu.

3        Tabbatar da labari kafin cigaba da yaɗa shi domin kaucewa rigima ko faɗace-faɗace.

4        Zama jakadan musulunci a duk inda mutum ya tsinci kansa.

5        Hukumomi su rinƙa lura da saka ido kan irin abubuwan da ake yaɗawa domin su dakatar idan kuma bai tsaya ba sai aje matakin saka takunkumi kamar yadda wasu ƙasashe sukayi kamar ƙasar Bangladesh.

Matuƙar an bi irin waɗannan hanyoyin da ma wasunsu ana sa ran samun cin muriyar wannan manhajar da samar da cigaba wa al’umma da al’adunta baki ɗaya.

4.1     Naɗewa

TikTok na ɗaya daga cikin shafukan sada zumunta wanada yake yana iya zama ni’ima ga wasu kamar yadda yake halaka ga wasu. Cikin wannan aiki da ya gabata an tattauna ma’anar Intanet da ɓangarorinsa, haka kuma an kawo maganar shafukan sada zumunta da ire-irensa wanda yake acikinsu ne aka ɗauki manhajar TikTok aka yi bayani akan sa tare da fito da irin alfanunsa ga rayuwar Hausawa da kuma matsalolinsa da kuma bayar da shawarwarin hanyoyin da ake ganin za su taimaka wajan magance waɗannan matsalolin.

 

Manazarta

https:\\wikihausa.com.ng/amfanin da haɗurran shafukan sada zumunta

https://www.investopedia.com/what is titok

BBC (British Broadcasting Company)/ ‘Yan matan TikTok: Matasan da aka tsare saboda bidiyon rashin kamun kai rahoton 17 aguta 2020

Sani, A-U (2021). Zamani Zo Mu Tafi: Al’adun Hausawa A Duniyar Intanet.

Cell Dilon: TikTok Influences On Teenagers Young Adults Students.

Post a Comment

0 Comments