Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Ka Ƙi Yin Zaɓe Wa Ka Cuta

Sheikh Dr. Isa Garba Nayaya

Ya yaɗu tsakanin jama’armu a nan Arewa “Ni zaben ma ba zan yi ba”, za ka ji mutum ya na fadan haka da zimmar bawa wasu haushi ko huce haushi, amma shi wawan naka bai san cewa hakan da ya ke fada yana daɓawa kansa wuka ba ne.

Na’am lallai yana daɓawa kansa wuƙa, amma bai sani ba, kaito zai fahimci abubuwa masu zuwa:

- Samar da shugaba wajibi ne a addinance, da lalura ta rayuwa, a addinance Manzo SAW ya tabbatar mana cewa: “Duk wanda ya mutu ba shi da shugaba da ya yi masa mubaya’a, ya mutu mutuwa irin ta jahiliyya”, domin kuwa su ne suke fariyar tafiya babu jagoranci.

Kamar yadda ya umarci matafiya idan sun kai uku da su nada jagora a tsakaninsu; to, yaya idan lamari da ya shafi dubunnan jama’a!? A'a, miliyoyin ake magana, haka nan buƙatar rayuwa ta buƙaci haka.

A duniyar mu ta yau: kowa ya na da damar zaɓowa kansa shugaba cikin tsarin da shi ne abin da ya iya sauwaƙa ga Musulmi; a yanayi na rauni da yake rayuwa a yau, don haka ko mutum ya yunƙura ya yi amfani da damarsa, ko a zabo masa wanda zai iya danne masa wasu haƙƙoƙinsa, wanda da ya motsa ya iya samuwa ko kuma wasu daga ciki.

- Quri’a a yau makami ce na yaƙi da tafi bakin bindiga a duniyar yau, da ita za ka ƙwatowa kanka ƴanci. Yaƙi kuwa idan ya zama dole ba za ka zauna a ɗaka ka na zaton za ka tsira ba; domin har cikin ɗaka (ɗaki) za a cimma-domin ka kare kanka da al’ummarka da addininka, dole ka futo ka yi abin da za ka iya, sai Allah SB Ya dubi gazawarka, Ya ba ka nasara ko faduwa mai dauke da izna.

- A addinance duk yayin da shugaba ya shelanta yaƙi a kan kowa da kowa, babu mai uzuri ko iyaye ba su da damar hana wanda ya isa futa fagan fama, idan lamarin haka yake, lallai ko a yau zabe yaƙi ne na ƙuri’a, kuma shugabanni sun shelanta, kuma maslahar addini ya na wajabta maka ka futo ka yi zabe, musamman idan ka duba yadda abokan zamanka su ka ɗau himma, suke ƙoƙarin haɗewa waje daya a lokacin da muke a tarwatse.

- Zabe alƙalanci ne, don haka kai mai zaɓe raba gardama za ka yi da abin da ka sani na zahiri tsakanin mutanen da suke rigima na cewa su suka cancanci jagorantar ka, abin da ke baɗini kuwa sai ka barwa Allah.

- Zabe sheda ce, sheda kuwa idan an nemi mutumin da ya ɗauke da ita, ya zama wajibi ya isar da ita, domin ba ya halatta a musulunci ka san abu, kuma a neme ka ka zo ka bada sheda sai ka ƙiya kamar yadda Allah SB Ya hane ka.

- Don haka idan ka ƙi yin zabe kanka da al’ummarka da addininka da ƴaƴanka ka cuta, kuma ka ha’inci makomarsu.

- Addu’a makami ce, don haka a yunƙura a yi addu’a, Annabi SAW zai futa yaƙi, kuma ka gan shi cikin filin daga ya dage da addu’a.

- Kada Allah Ya bar mu da wayonmu, ko dabarar mu, ko ƙarfinmu, ko aikatau na wawayen cikinmu, gare KA muke kai kukanmu, Ka zaɓa mana na-gari ba don halinmu ba, kuma Ka agaje shi da ludufin Ka da Ya Ladeefu. Amin.

Post a Comment

0 Comments