Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Hausar ‘Yan-Lakun A Garin Gusau Na Jihar Zamfara

Muƙalar da aka gabatar a ajin ALH 400 (Seminar), a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau, Jahar Zamfara, Nijeriya, (Disamba 2022 - Janairu, 2023).


SABITU SANI

Ƙibɗau: sabitusani01@gmail.com
Lambar Waya: 08038510879

Tsakure

Wannnan muƙala mai taken Nazarin Hausar ‘Yanlakum A Garin Gusau, muƙala ce da ta cike gurbin da aka bari na nazarin ilimin walwalar harshe, duk da cewa manazarta da masu bincike sun yi bincike a kan  Hausar rukunin jama’a daban-daban amma ba a ci karo da wadda ta yi magana a kan Hausar ‘yanlakum ba. Saboda haka wannan binciken ya yi ƙoƙarin zaƙulu ko fito da kalmomi da jumlolin da ‘Yanlakum ke anfani da su yayin sadarwa a tsakaninsu. Sannan ya gano hanyoyin da suke bi domin samar da kalmomi nasu. Yayin gudanar da wannan bincike an yi anfani da fitattu kuma sanannun hanyoyin gudanar da bincike da suka haɗa da: Bitar ayyukan da suka gabata, Hira ko zantawa da masu wannan harka, Ziyarar shafukan yanar gizo, da kuma Sa ido da  lura (observation). An ɗora wannan aiki akan ra’in fage (field  theory)  na  Lehrer  (1969).  Ana amfani da  wannan  ra’in  ne  domin  fayyace  irin  canje-canjen  da  ake  samu  a  cikin  harshe,  da yadda  ma’anar  kalma  kan  iya  canzawa  gaba  ɗaya  daga  ma’anar  da  aka  san  ta.

 

1.0 Gabatarwa

‘Yanlakum (masu wa’azin turmi) rukunin jama’a ne da ke wa’azi da sayar da maganin gargajiya ko na musulumci ko kuma wani laƙani bayan sun kammala wa’azi, galibi da safe ko da dare  a cikin unguwanni, wani loton kuma da rana a kasuwanni da wuraren taruwar jama’a, ta yin amfani da amsa-kuwa (speaker) wadda suke azawa a kan wani gini ko bishiya (itaciya) da ke kusa da su domin jiyar da mutane.

 

Wannan bincike ya shafi ɓangaren ilimin walwalar harshe ne, ta yadda shi kuma wannan ɓangaren ake nazarin harshe ta hanyoyi biyu, wato nazarin ilimin walwalar harshe dangane da nahiya da kuma nazarinsa dangane da rukunin al’umma. Wannan binciken ya mayar da hankali ne a ɓangaren nazarin karin harshen rukunin masu sana’ar lakum (wa’azin turmi) kasancewar su ɗaya daga cikin rikunonan jama’a da suke gudanar da al’amuransu a cikin Hausawa. Su masu sana’ar lakum tamkar sauran rukunonin al’umma masu gudanar da sana’o’i, su ma suna da nasu keɓantattun kalmomi da jumloli da suke sarrafawa domin gudanar da hulɗoɗinsu a tsakaninsu

 

Wannan bincike zai yi ƙoƙorin zaƙulo keɓantattun kalmomi da masu sana’ar lakum ke sarrafawa yayin gudanar da sana’arsu, sannan ya gano hikimomi da hanyoyin da masu wannan sana’ar ta lakum suke amfani da su wajen samar da sababbin ma’anoni ko kalmomi a rukuninsu, Zaƙulo sababbin jumloli da suka ƙirƙira kuma suke amfani da su yayin gudanar da sana’arsu.

Baya ga wannan binciken zai cike wani giɓi da aka bari a fagen nazarin ilimin walwalar harshe. Wannan giɓi kuwa shi ne kasancewar masu nazari da bincike sun yi nazarin Hausar rukunonin al’umma daban-daban kamar;

 

 • Hausar yaran mota,
 • Hausar masu sana’ar waya,
 • Hausar masu sana’ar kayan gwari,

Da makamantansu  amma har yanzu ba mu ci karo da binciken da ya yi magana a kan Hausar masu sana’ar lakum (wa’azin turmi) ba.

 

Kasancewar kusan kowane rukunonin al’umma sukan keɓanta da karin harshensu, domin sadarwa a tsakaninsu, Ta yuyu rukunin masu sana’ar lakum ya amsa sunansa na rukuni, ya zamana  suna da nasu karin  harshe da suke amfani da shi domin sadarwa a tsaninsu.

 

1.1 Karin Harshen Rukuni

Da yake wannan binciken yana ƙoƙarin nazari ne a kan karin harshen rukuni, to, a nan an kawo ma’anar karin harshe na rukuni a matsayin matashiya. Trudgill  (1974)  ya  yi  bayanin  cewa  karin  harshe  na  nufin  bambance-bambance  tsakanin nau’oin  magana  da  suke  da  bambanci  a  kalmomi  da  nahawu  da  kuma  furuci  ne.  Ya  kuma  yi tsokaci  a  kan  dalilai  da  dama  da  suka  sa  ake  amfani  da  karin  harshe  a  rukuni.  Ya  ce  duk  wani zance  ko  magana  tana  da  muhalli  da  dalilin  da  ya  sa  ake  yinta.  Idan  kuwa  haka  ne,  to  ashe amfani  da  karin  harshe  a  rukuni  na  wurare  na  musamman  ko  kuma  wani  yanayi  wanda  ke haifar  da  faɗar  wata  ko  wasu  kalmomi  masu  nufin  wata  ma’ana  ta  daban,  dalili  ne  mai haddasa  wanzuwar karin  harshen rukuni.

 

Stubbs  (1983)  na  ganin  akwai  abubuwa  da  dama  da  suka  shafi  yanayin  zaman  jama’a  da  suke da  tasiri  wajen  amfani  da  harshen  masu  magana.  Ya  ce  idan  masu  magana  suka  kasance  da karin  harshe  daban-daban,  ko  salon  magana  daban-daban,  sukan  karɓi  salon  da  zai  dace  da yanayin  da  ake  ciki  su  yi  amfani  da  shi.  Wanda  hakan  kan  haifar  da  samuwar  wani  nau’i  na harshe.

Fagge (2002) ya ɗauko daga Bargery (1934) da Asiru (1981) da Musa (1996) inda suka nuna cewa karin harshen Hausa yana da karekare na nahiya da kuma na rukuni, amma a nan za a yi dubi ne a kan karin harshe na rukuni. Karin harshen rukuni wani ɓangare ne na karin harshe da ya danganci wasu mutane masu halayyar zamantakewa da kuma hanyoyin sarrafa harshe iri ɗaya. Wato yanayin zamantakewarsu yana da nasaba da tsarin harshe da kuma yadda suke amfani da shi (Fagge 2002:97).

 

Masana irin su Hudson (1980:24) da Wales (1989:398) sun yi bayanin karin harshe a matsayin wani nau’i ne na yadda wasu mutane suke amfani da harshen domin isar da saƙo ta hanyar yin amfani da wasu kalmomi ko ginin jumla ko ƙirar kalma wanda wasu ɓangarorin ba su amfani da su duk da cewa harshe ɗaya suke magana da shi.

 

1.2 Ma’anar Harshe

Yakasai (2012:47) Ya bayyana harshe a matsayin hanyar furta ma’anoni da tunane-tunane da suke ran ɗan Adam. Wato  hanyar sadarwa tsakanin mutane.ita wannan hanya kuma ba ganin ta ake yi ba, jin ta ake yi kawai, wato hanyar sadarwa ta ɗan Adam (harshe) saututtuka ne masu ma’ana da ake furta su, kunnen mai sauraro ya ji, kana basirarsa ta kama, ta fahimta domin amfaninsa. Al’umma ta ɗan Adam tana da alfahari da buri. Alfaharin nan shi ne tarihi, buri kuma shi ne kokawar rayuwa domin yau da kullum. Saboda haka, a fafutuka ta wanzuwa ko zaman rayuwa, akwai buƙatar abubuwan nan da suka zama dole ga kowace al’umma, domin ita rayuwar ta tafi daidai.waxannan abubuwa sune: Mulki da shari’a da tattalin arziki da addini da kuma al’ada. Yakasai, (2012:51).

 

Zarruq da Wasu (1986: 1) sun bayyana harshe da cewa “Harshe magana ke nan, wadda ake ji a fahimta. Harshe shi ne abin da ya bambanta ɗan’adam da sauran dabbobi. Harshe a wurin ɗan’adam linzami ne na tunani. Sauran dabbobi sai dai su yi kuka, ko gurnani, ko haushi, ko haniniya, don su nuna fushinsu ko murnarsu, ko wuyarsu. Ko daɗinsu. Hatta aku, da yake iya kwaikwayon maganar ɗan’adam, yana yi ne ba tare da tunani ba”. Ka ga a nan za ka fahimci cewa mutum kaɗai ne yake iya riya abu a zuciyarsa, ko ya gani da idanunsa ko ya ji da kunnuwansa, sannan ya furta da bakinsa. Wannan ne dalilin da ya sa Chomsky (1972) yake cewa ana yin nazarin harshe domin cewa shi harshe shi ne madubin tunanin ɗan’adam.

 

Daga ma’anar harshe da aka kawo za a fahimci cewa harshe dai muryoyi ne da ake jerantawa bisa ƙyaƙƙyawan tsari mai ɗauke da ma’ana. Fitar da muryoyi masu ɗauke da wata ma’ana ko saƙo ya keɓanta ga harshen ɗan’adam. Domin mutum ne kaɗai yake gwada fasaharsa da nishaɗinsa ta hanyar amfani da harshe. Harshe kacokan baiwa ce da Allah ya ba wa ɗan’adam. Da harshe mutum yake sadarwa da yin mu’amala a tsarin zamantakewa.

 

1.3 Ra’in Bincike

Wannan  nazarin    an  ɗora  shi  ne  kan  ra’ain  da  ake  kira  (field  theory)  na  Lehrer  (1969).  Ana amfani  da  wannan  ra’in  ne  domin  fayyace  irin  canje-canjen  da  ake  samu  a  cikin  harshe,  da yadda  ma’anar  kalma  kan  iya  canzawa  gaba  ɗaya  daga  ma’anar  da  aka  san  ta.  A kan  yi amfani  da  wannan  ra’i    wajen  kwatancen  harsuna  kasanceawar  bambancin  da  ake  samu  a harsuna  a  sarari  suke  tun  daga  azuzuwan  kalmomi,  da    muhallin  da  ake  samun    kowace kalma.  Kamar  kalmomin  da  suka  danganci  yanayi  na  zafi,  da  muƙami,  da  kaloli,  da  sunayen sassan jiki, da  dabbobi da kayan marmari, da  sauransu.

Field theory by Lehrer (1969) stated that field theory  can be used  to illustrate language  change. The way  semantic  space   carved up  and realized in lexical items changes  constantly.   It can also be used in contrastive analysis of different   languages.  To illustrate how a given semantic area is sub-divided similarly or differently in different languages. Languages often differ even in apparently  quite  basic lexical division,  and field such as temperature  terms, kinship terms,   colour terms, part of  the  body  and divisions  of animal vegetable world will divide the  semantic  space  differently  and reflect this in the  vocabulary  items covering  those field.  Malmljar, K. (1991).

 Wato  wannan  ra’i  ne  na  rarrabe  ma’ana  a  tsakanin  kalmoni  domin  su  dace  da  muhallin  da  aka same  su  sannan  a  gano  irin  sauye-sauyen  da  aka  samu  a  cikin  harshe  da  kuma  yadda  suka taimaka  wajen  haɓaka  harshe.    Har  ila  yau  wannan  ra’i    na  nuna  dangantakar  da  ke  tsakanin kalmomi  ta  fuskar  ma’ana.  An  yi  amfani  da  wannan  ra’i    wajen  nazarin  Hausar  ‘yanlakum domin  a  ga  irin  canje-canjen  da  ake  samu  na  kalmomi  a  cikin  harshe  sakamakon  yunƙurin masu wannan sana’a  ta  Lakum. Har  ila  yau  wannan  ra’in  ya  samu  karɓuwa  da  kuma  waɗanda  suka  bi  wannan  ra’i  irin  su Gumperz,  (1962),  da  Lyons,  (1970),  da  Hudson  (1980),  da  Wales  (1989),  da  Ahmed  (2015). Har    aka  gangaro  zuwa  yanzu  da  wannan  bincike  ya  ɗauki  ra’in  domin  amfani  da  shi  wajen gudanar da  wannan bincike.

 

2.0 Man’anar Kalmar Hausa

Adamu (1997: 48) ya waiwayi tambayar cewa shin Hausa sunan ƙabila ne ko yare ne? Ga amsar da ya bayar kamar haka “Hausa suna ne na harshe, kuma masu wannan harshe su ake kira Hausawa, domin su al’ummar Hausawa ba su ɗauki kansu qabila ba, don kuwa a gurinsu duk wanda ba Bahaushe ne ba, to shi suke ce wa ƙabila, ko kuma bagwari, wato kamar yadda dai Larabawa suka ɗauki duk wanda ba Balarabe ba da cewa Ajami ne”.

 

Amfani (2012: 4) cewa ya yi “Hausa harshe ne, kuma tana ɗaya daga cikin harsunan ɗanadam waɗanda ake samu a nahiyar Afirka. A lissafin ko ƙididdiga irin ta masana ilimin kimiyyar harshe harshen Hausa yana cikin wani babban rukuni na kason harsunan duniya wanda ake kira Afro-asiatic. Shi ma wannan babban rukuni yana da ‘ya’ya kuma kowane ɗa, shi ma ƙaramin rukuni ne mai ɗauke da harsuna. Ƙaramin rukunin da Hausa ke cikinsa shi ake kira gidan harsunan Cadi. Wasu harsunan ‘yan gidan Cadi, waɗanda ‘yan’uwan Hausa ne, su ne Angas da Bole da Ron”.

 

2.1 Ma’anar Kalmar Lakum

 Kalmar ta samo asali ne daga kalmar larabci wato (لكم) mai ma’anar naku a zahiri, yayin da a wannan rukuni take da ma’anar malam saboda masu wannan sana’a sukan shiga rigar malanta su fake ta hanyar shiga irin ta malamai da kuma samun wasu addu’o’i da za a haddace, saboda yaudara barazana da kuma burga wani lokacin har da Ƙur’ani da Tazbaha, duk da ya ke akasarinsu suna da ilimin addinin Musulunci daidai gwalgwado.

 

Ma’ana ta isɗilahi kuwa tana nufin sana’ar wa’azi da sayar da magani da ba da laƙani da kuma duba (istihara) ta hanyar amfani da amsa kuwa (speaker) a cikin unguwannin birane da ƙauyuka, da safe ko da dare, ko kuma da rana a kasuwanni da wuraren taruwar jama’a.

 


2.3 Farfagiyar Binkike

Kasancewar harshen Hausa yana da manyan rassa uku na nazari waɗanda suka kunshi:

a. Adabi (literature),

b. Al’ada (culture)

c. Da kuma harshe (language).

 

Wannan bincike an gudanar da shi ne a ɓangaren harshe, sannan kuma ko a harshen a fannin ilimin walwalar harshe, sannan an keɓance binciken a kwaryar  garin Gusau kacokam musamman yankin birnin ruwa a gundumar mayana inda nan ne yawancin masu wannan sana’a ta lakum su ka fi yawaita.

 

2.4 Hanyoyin Gudanar da Bincike

A yayin gudanar da wannan bincike an yi amfani da manya kuma sanannun hanayoyin gudanar da bincike domin haƙa ta cimma ruwa, kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Waɗannan hanyoyi sun haɗa da:

a. Bitar ayyukan da suka gabata,

b. Ganawa ko zantawa da masu wannan harka,

c. Ziyarar shafukan yanar gizo,

d. Sa ido da kuma lura.

 

3.0 ‘YanLakum

‘Yanlakum ko lakumawa (masu wa’azin turmi) rukuni ne na jama’a da ke wa’azi da sayar da maganin gargajiya ko na musulunci da ba da laƙani ko laya sannan akwai masu cire iskoki(ruƙiya) da kuma masu duba (istihara), wannan rukuni na jama’a suna gudanar da wannan sana’a tasu da safe ko da dare a cikin unguwanni ko da rana a kasuwanni ko wuraren taruwar jama’a.

 

3.1 Kashe-Kashen ‘Yan Lakum

‘Yanlakum sun kasu zuwa gida uku manya kamar haka:

a. ’Yanɗaiɗai,

b. Sunƙuru,

c. Rufani.

 

‘Yan Ɗai-ɗai

Wannan kaso na ‘yanlakum shi ne kason da ke sayar da maganin lalurori iri daba-daban, ɗaya bayan ɗaya kamar matsalar sanyi, zahi, ciwon daji, olsa  da makamantansu, a nan bayan ɗanlakum ya gama addu’o’i da gabatarwa sai ya tsunduma cikin tallar magani daki-daki, wato bayan ya yi tallar maganin sanyi kimanin mintuna goma zuwa sha biyar sai ya koma na Basir daga nan kuma sai na olsa haka dai zai yi ta yi har lokacin da zai tashi, sannan yana yi yana rage farashin maganin. Sannan su ma sun kasu kashi biyu akwai ‘yan-siba wato masu aiki kasuwa-kasuwa da rana, sannan akwai masu aikin safe da dare a cikin unguwanni su kuma waɗannan ba su cin kasuwanni.

Sunƙuru

Wannan kaso na ‘yanlakum su ma suna sayar da magani amma su ba kamar ‘yan- ɗaiɗai ba, a nan marar lafiya zai zo ya yi masu bayanin duk abun da ke damunshi sai a haɗa masa magunguna a ce ya ba da naira kaza, sannan kuma suna ruƙiya domin fitar da iska a jikin mutum (marar lafiya).

 

Rufani

Wannan kaso na ‘yanlakum babban aikinsu shi ne duba wato istihara idan wani abu ya ɓace ko an sace shi za su yi istihara domin gano inda abun ya ke, ko kuma wanda ya sace shi, kuma suna amfani da rufanai dalilin da ya sa ake kiransu ruhani ke nan, daga cikinsu akwai masu ruhanai na gaskiya, akwai kuma na ƙarya, duk da yake kashi casa’in da tara cikin ɗari (99/100) su ne na ƙarya, kawai suna amfani da dubaru da hikimomi da kuma mamare ne.

 

3.2 Wasu Daga Cikin Dabarun ‘YanLakum

Kira da rike mutane kada su watse; A nan idan ɗanlakum zai fara sana’arshi ta lakum yana amfani da wasu dabaru domin jawo mutanen da ke nesa kusa, da kuma rike na kusa gare shi kada su watse, ta hanyar faɗar wasu kalamai kamar:

Duk  masoyin Annabi (s.a.w) da ke kusa ya samu wuri ya natsu, wanda ya ke nesa kuma ya matso kusa don jin maganar ɗangata Rasulullahi, Shi kuwa munafuki yanzu ka ga ya kakkaɓe rigarshi ya ƙara gaba.

 

Sannan wani lokaci za su ce za su nuna wani abin ban al’ajabi,  wanda faɗin hakan zai sa na nesa su matso, su haɗu da na kusa, su kasa su tsare, domin ganin wannan abu na ban al’ajabi, amma daga ƙarshe ba su nanu komai, dama sun yi ne kawai domin tara mutane da kuma hana su watsewa.

 

Badali

Idan an ce badali a nan ana nufin duk wata dabara da za su aiwatar yayin gudanar da sana’arsu da nufin baddalar da jama’a, wato su sauyar da tunanin jama’a idan sun aikata wani abu na ban al’ajabi sai jama’a su ɗauka da gaske ne, alhali ba gaskiya ba  ne, abu ne da kowa zai iya yi idan ya sa kansa ba wani abun mamaki ba ne wanda sai wane da wane, daga cikin dabarun na badali akwai:

 

Amayo Da Feto Allurai

‘Yanlakum sukan ɓoye allurai a cikin bakunansu ko a cikin  hantunansu a lokacin da za su gudanar da aiki, da nufin amayo su ko feto su a gaban jama’a a yayin da suke aiwatar da sana’arsu, idan hakan ta faru jama’ar da ke wurin za su yi tunanin cewar sun amayo su ne ko sun feto su ne daga cikin ciki ko kai, wanda a zahirin gaskiya sun boye su ne a cikin baki ko hanci.

Tayar da Hayaƙi

‘Yanlakum sukan yi amfani da fankon ashana  sai su ciro wurin da ake ƙyasta kan ashana sai su juya shi su goge shi ya koma lafai-lafai sai su shanya ya sha iska su  aza wannan abun da suka goge  a birkice a kan cokali, sai su kunna masa wuta idan ya ƙone zai bar maski akan cokalin, sai su shafo wannan maskin a kan yatsunsu, to da zarar sun murza yatsun sai hayaƙi ya tashi a kan yatsun.

Yanka Wuƙa a Jiki

A nan kuma ‘yanlakum sukan yi amfani da wuka mai kaifi biyu  sai su koɗa (wasa) ɗayan ɓangaren ya yi kaifi sosai, ɗayan bagaren kuma su dallasar (dakusarwa) da shi ta hanyar goga shi a kan kwalba. Sukan fito da wannan wuƙa a lokocin da suke gudanar da sana’arsu, su yanki wani abu  take ka ga ya rabe biyu, sannan sai ku ga kamar sun juya ɗayan ɓangaren wuƙar amma a zahiri ba su juya ba, su sake yankan abun sai kaga ya sake rabewa biyu, a ganin jama’a kowane gefe yana da kaifi amma a zahiri gefe ɗaya ne yake da kaifi, wato wanda suke amfani da shi yayin wankan wani abu, amma idan za su yi gwaji a kan jikinsu sai su yi amfani da gefen da ba ya da kaifin ma’ana dakusasshen ɓangaren. Sukan yi haka ne don nunawa jama’a cewa su ba haka nan suke kara zube ba, a shirye su ke, alhali kuma ba haka abun yake ba, dabaru ne da hikinkimu wanda kowa ma zai iya yi.

 

4.0 Hausar ‘YanLakum

Kasancewar ‘yanlakum rukuni na jama’a masu gudanar da hulɗoɗinsu da al’ amurransu na yau da kulln a cikin al’ummar Hausawa, sannan ga su da dubaru da hikinkimu na kaɓar kuɗi hannun mutane ya tilasta suka samar da nasu karin harshen rukuni wanda idan ba cikinsu ka ke ba, ko sun yi  magana a gabanka to da wahalar gaske ka iya fahintar abun da suke nufi. Sun ƙirƙiri kalmomi da jimloli masu tarin yawa domin sadarwa a tsakaninsu, ga   wasu daga cikin irin waɗannan kalmomin nasu tare da ma’anarsu a daidaitacciyayar Hausa.

 

4.1 Sunayen Kuɗi A Wajen ‘YanLakum

 1. Kalma                                   Ma’ana
 2. Kamsa                                  Biyar
 3. Gunza                                   Goma
 4. Muri                                      Ashirin
 5. Kamsuna                              Hamsin
 6. Ata                                        Ɗari
 7. Ataini                                    Ɗari biyu
 8. Ata kamsa                            Ɗari biyar
 9. Zugun                                    Dubu

 

4.2 Kalmomi Ta Hanyar Ƙirƙira

Kamar  sauran  hanyoyin samar  da  kalmomi, Zarruk  (1993)  ya  bayyana  ma’anar  ƙirƙirar kalma  da ƙago  wani  laƙabi  ko  wata  magana  don  bayyana  wata  baƙuwar  ma’ana.  Haka  kuma  ya  raba ƙirƙirar  kalma  zuwa  gida  biyu,  ƙirƙirar  bazata,  da  ƙirƙirar  takanas.  A  nan  za  a  yi  bayanin wasu  daga  cikin  kalmomin  da ‘yanlakum    ke  amfani  da  su  a  cikin  mu’amalarsu  ta  yau  da kullum  wadda  yanayin  sana’arsu  ce  ta  sa  suka  samar  da  kalmomin  kuma  suke  amfani  da  su  a cikin  harkokinsu.  Wato  ƙirƙirar  kalmomin  suka  yi,  sannan  alamu  sun  nuna  cewa  sun  samu kalmomin ne  ta hanyar  ƙirƙirar bazata. Waɗannan  kalmomin sun haɗa  da:

Kalma                                                Ma’ana

           1. Asawa                                             Mahaifi

2. Asawanya                                     Mahaifiya

3. Ɗarani                                            Mashin

4. Ɗan-gwabso                                  Ɗan-daga

5. Ɗan-tanko                                     Mai shan taba

6. Ɗanwara                                        Ɗangiya

7. Fari guza                                       Rago

8. Gulamin-ta-sulaiman                  Memori

9. Guza                                               Gaban namiji

          10. Kwasasshe                                     Maikuɗi

          11. Kanɗa                                             Sha

        12. Ƙiri                                                   Maikyau

           13. Mago                                             Magani

           14. Magori                                          Mai magani

15. Mai ƙafon tsumma                    Mai gari

16. Mani                                                Gaban mace

17. Natuta                                          Talaka

18. Nazauran                                   Bazawara

19. Sogaye                                         kaya

20. Sunƙi                                            Ɗaki

21.Sunƙin mai duka                         Masallaci

22. Sogan na sheɗan                         kayan kallo

23. Sogayen na kare                         Takalmi

24. Sogayen amalu                           Kayan aiki

25.Takaka                                         Bindiga

            26. Takakoki                                      ‘Yan bindiga

27. Sagin mai duka                          Hadari

28. Samaka                                       Mahaukaci

29. Ta-baba-alula                              Keke

30.Ta-sulaiman                                 Waya (hanset)

31.Watu                                            Abinci

32. Watun yarima                             Tuwon masara

33. Watun risi                                  Tuwan shinkafa

34. Watun kwoc                                Tuwon dawa

 

4.3 Kamomi Ta Hanyar Kwatance Ko Siffanatawa

A nan ‘yanlakum sukan yi amfani da dabarar kwantance ko siffantawa yayin  laƙaba wa wani abu suna a rukuninsu, ta hanyar danganta wannan abun da wata ɗabi’a ko halayya ko yanayin halitta ta wani mutum ko wata dabba ko wani abu da yake da wannan ɗabi’a ko kuma yake yawan aikata ta. Misali

Kalma                                        Ma’ana

1.Dage                                        Faɗa

2. Fara                                        Tunkiya

3. Jaa                                          Akuya

4. Kwata                                     Jini

5. Na-kasa                                  Barci

6. Na-shanshani                         Ƙafafu

7. Na-jaki                                   Duka/bugu

8. Na-tunku                                Kashi

9. Kwaɗo                                   Fitsari

          10. Na-auduga                            Dariya

          11. Na-maraya                            Kuka

          12. Na-amarya                            Kunya

          13. Na-zomo                               Gudu/Sauri

          14. Na-kura                                 Tsoro

       15. Na- lawan                              Rago

          16. Na-kahu                                Karatu/Ilimi

          17. Na-giwa                                Girma

          18. Na-giɗa                                 Fetur

          19. Na-kujeri                               Ɗuwawu

          20. Santal                                    Gaskiya/ Na ƙwarai

          21. Sansiro                                  Sanyi

          22. Ta-manzo                              Sadaka

          23. Ta talmizu                             Sadaka

          24. Yar gabas                              Sallah

 

4.5 Aro (Borrowing)

Rufa’i (1979) ya bayyana ma’anar aro a harshe da hanya ce da harshe ke aro kalmar wani harshe ya sauya ta zuwa harshensa. Wannan bincike ya lura da cewa akwai kalmomin da ‘yanlakum suka samo kuma suke amfani da su ta hanyar aro daga sauran harsuna musamman harshen larabci, da kuma kaɗan daga wasu harsuna. Misali

Kalma                                     Ma’ana

1.     Aƙalu                                 Hankali

2.     Ainu                                   Ido

3.     Badawi                               Gari

4.     Baɗalu                                Ciki

5.     Dari                                    Gida

6.     Gulami                               Yaro

7.     Istoma                                Ciwon olsa

8.     Ju’i                                     yunwa

9.     Ƙauli                                  Magana

10. Lahamu                             Nama

11. Lailu                                  Dare

12. Labanu                              Nono

13. Lasuwaki                          Kasuwa

14. La                                     Ba (nagation)

15. Maridanci                         Rashin lafiya

16. Ma’i                                  Ruwa

17. Rijalu                                Babban mutun

18. Ra’asu                               Hula

19. Sayyara                             Mota

20. Sariƙu                               Ɓarawo

21. Sariƙai                              Ɓarayi

22. Ta’allaƙa                          Laya

4.6 Kalmomi Ta Hanyar Gusar Da Ma’ana Da Juyar Da Gaɓoɓin Kalma

A nan ‘yanlakum suna ɗaukar wasu kalmaomi na Hausa sai su sauya ma’anarsu, wato su ba su wata sabuwar ma’ana koma bayan wadda aka san su da ita ta ainihi ko asali. Haka kuma sukan ɗauki kalma sai su juyar da furucinta wato gaɓar farko ta koma ƙarshe ita kuma ta ƙarshe ta dawo farko. Misali

Kalma                                                  Ma’ana

1.     Duƙowa                                   Zuwa

2.     Hita                                           Ƙyale

3.     Isa                                             Wanda bai jin Hausar

4.     Jewa                                         wani wuri

5.     Ƙashi                                         Ɗan-sanda

6.     Kattafawa                                Haɗawa

7.     Kafan                                        Fanka

8.     Katako                                      Soja

9.     Liman                                       Aure

10. Naɗewa                                   Kamawa

11. Saukewa                                  Yi

12. Saukewa                                  Ba da wani abu

13. Sirba                                         Basir

14. Turba                                        Batur

15. Tuta                                          Rashi/Babu

16. Tsamaku                                  Iskoki

17. ‘Yan kanɗe-kanɗe                   Shaye-shaye

18. Zubawa/Zubairu                    Tafiya

4.6.1 Jimlolin ‘YanLakum

Baya ga kalmomin da ‘yanlakum suka ƙirƙira sai kuma jimlolin da suka ƙirƙira kuma suke amfani da su a harkokinsu na yau da kullun, sun ƙirƙiri waɗannan jimloli ne ta hanyar harhaɗa waɗannan kalmomi nasu domin su tada jimla mai ma’ana, ga wasu daga cikinsu:

 

4.6.2 Hausar ‘YanLakum                    Daidaitacciyar Hausa

1.  Magon magorin nan santal ne              Maganin mai maganin nan na gaskiya ne.

2.  Zan zuba in sauke ‘yar gabas.           Zan tafi in yi Sallah

3.  Laja la ƙiri.                                        Ba kasuwa.

4.  La sauke gulami                                Ba haihuwa.

5.  Ana sauke gulamai suna bajewa.      Ana haihuwa yaran na mutuwa.

6.  Hita da shi.                                        ƙyale shi.

7.  Maridanci ya naɗe ni.                       Rashin lafiya ta kama ni.

8.  Ɗaranin asawana ne.                        Mashin ɗin mahaifina ne.

9.  Kattafa mani ta’allaƙa.                     Haɗa mani laya.

10. Tsamaku sun nake mata ga baɗalu. Aljanu sun mata kwance ga ciki.

11. Mu zuba kawai.                               Mu tafi kawai.

12. Ga ni nan duƙowa.                          Ga ni nan zuwa.

13. Kwata la duƙowa.                           Jini ba ya zuwa.

14. La na-kahu                                      Jahili

15. Jalabce.                                           Zauna

16. Ɗanka mai ƙiri.                              Budurwa mai kyau.

17. Na faɗa da ɗankar nan.                  Budurwar nan ta burge ni.

18. Sauke man ata kamsa.                   Ba ni ɗari biyar.

19. Asawan abokina ne ya baje.          Mahaifin abokina ne ya rasu.

20. Yana dari yana naka.                    Yana gida yana barci.

21. Naɗo shi a ta-sulaiman.                Kira shi a waya.

22. Hita da da gulamin nan.                kyale yaron nan.

23. Na hita da ɗankar nan                   Na ƙyale budurwan nan.

24. Ɗankar nan ta naɗo ni                  Budurwannan ta kira ni.

25. Gulamin nan ya zuba.                  Yaron nan ya tafi.

26. Rijalun nan ya baje                      Mutumin nan ya mutu.

27. Jalabce ka yi watu                       Zauna ka ci abinci.

28. Ɗankar nan la nakahu                 Budurwar nan jahila ce.

29. ka yi ‘yar gabas?                         Ka yi sallah.

30. Maridanci ya naɗe asawana        Babana ba ya da lafiya.

31. Zuba kawai ga ƙashi nan duƙowa  Tafi kawai ga ɗansanda nan zuwa.

 

5.0 Sakamakon Bincike

Sakamakon wannan bincike yayi daidai da maƙasudi ko manufar binckiken domin kuwa an samu nasarar zaƙulo wasu daga cikin kalmomi da jimlolin da ‘yan lakum suka ƙirƙira kuma suke amfani da su a zantukansu na yau da kullun kamar yadda ya gabata. Sannan idan an lura da kyau a cikin gundarin aikin, za a fahimci cewa daga cikin dabarun da suke bi wajen samar da kalmomoinsu akwai: Ƙirƙira wato su ƙirƙiri wata sabuwar kalma su ba ta wata ma’ana, sannan suna amfani da aro (borowwing) musamman daga harshen Larabci. Sannan akwai dabarar kwatance misali nakasa (bacci), nashanshani (ƙafafu) namaraya (kuka),baya ga wannan kuma akwai wata dabara da suke amfani da ita ta gusar da ma’ana inda suke ɗaukar wata kalma ta Hausa sai su sauya ma’anarta da wata ma’anar ta daban da makamantansu. Daga ƙarshe kuma suna anfani da dabarar rawar ‘yanmata wato na gaba ya koma baya  inda ake ɗaukar gaɓar kalma ta farko a mayar da ita baya a ɗauki ta baya a mayar da ita ta farko. Misali turba (batur), sirba (basir) da makamantansu.

 

5.1 Kammalawa

Wannan bincike an gudanar da shi a kan nazarin Hausar ‘yanlakum a garin Gusau binciken yayi ƙoƙarin fito da kalmomi da kuma jimlolin da ‘yanlakum suka ƙirƙira kuma suke anfani da su a zantukansu na yau da kullun. Baya ga wannan an yi bayanin nagartattun hanyoyi da aka bi a lokacin gudanar da wannan aiki waɗanda suka haɗa da: Bitat ayyukan da suka gabata.Hira da masu ruwa da tsaki a wannan harkar, Ziyarar shafukan yanar gizo.Lura da sa ido, Daga ƙarshe a cikin sakamakon binciken an lissafa hanyoyin da su ‘yanlakum suke bi domin samar da waɗannan kalmomi na rukuninsu. Baya ga wannan an kawo sakamakon bincike da kuma bayanin  kammalawa wanda ya yi bayanin aikin a dunƙule sannan aka kawo manazarta.

 

Manazarta

Abdulƙadir, Z. (2013). Karin Harshen Rukuni: Nazarin Hausar Kan Titi. Unpublished M.A Thesis. Zaria, Ahmadu BelloUniversity.

 Abubakar, I.A. (2001). Dangantakar Harshe Da Addini: Nazari A Kan Karin Hausar Gardawa A Birnin Kano Da Kewaye. Maqala Da Aka Gabatar A Taron Ƙarawa Juna Ilimi Tsakanin Malamai da ɗalibai. Kano: Jami ar Bayaro. (Unpublished).

Adamu, A.U. (2008). Salon Taɗin Mata Hausawa a cikin Garin Kano. Kundin Digiri    na Biyu, Sashen koyar da Harsunan Nigeriya. Kano; Jami ar Bayero.

Bello. Musa, A. (2011). Hausa-Niga: Nazari A kan Walwalar Harshe da Zamantakewa Tsakanin Rukunin Matasa Maza Hausawa a Yau. In Studies in Hausa Language, Literature and Culture. The 6th Hausa International Conference. CSNL. Kano: Bayero University.

Dawakin Tofa, M. I. (2005). Karin Harshen Mahauta. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Kano: Jami ar Bayero.

Fagge, U.U. (1999). Tasirin Karin Harshe na Rukuni wajen Ƙirƙirar Sababbin Ma’ anoni a Hausa. Takardar Da Aka Gabatar A Taron Ƙarawa Juna Ilimi. Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami ar Bayero.

Muntari, H. (2008). Karin Harshe Na Rukuni A Hausa: Nazari A Ƙasar Zazzau. Kundin Digiri na Biyu.Sashen Harsuna Da Al adun Afirka Zariya: Jami ar Ahmadu.

 

https://www.google.com/amp/s/docplayer.net/amp/54653968-Karin-harshen-rukuni-nazarin-hausar-masu-sana-ar-kayan-gwari-hamisu-ahmed-ma-arts-16486.html

https://www.amsoshi.com/2022/03/hausar-rukunin-masu-sanaar-waya-garin.html?m=1

 

Waɗanda aka zanta da su:

Malan Sanusi Muhammad (Malan Muhammadu)dan shekara 35, Ranar Lahadi  8/1/2023

Malan Umar Ibrahim shekare, dan shekara 25, Ranar Litinin 9/1/2023.

Malan Usman malan Ibrahim kagane, dan Shekara 40, Litinin 9/1/2023.

Doctor Sulaiman Shala Gusau, dan shekara 38, Ranar Talata 10/1/2023.

Post a Comment

0 Comments