Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsakanin Allah Wadai Da Allah San Barka: Hasko Akalar Al'adun Auren Hausawa A Hannun Zamani

Muƙalar da aka gabatar a ajin ALH 400 (Seminar), a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau, Jahar Zamfara, Nijeriya, (Disamba 2022 - Janairu, 2023).

Auren Hausawa

Name: Asma'u Ibrahim B/Magaji

Admision Number: 1610104032

Tsakure

wannan muƙalar za ta dubi al'adun aure na Hausawa. Bugu-da-ƙari, muƙalar za ta kalli yadda zamani ke ta tsoma ƙafa cikin al'adun domin fito da sauye-sauyen da ake samu tun daga zamanin gargajiyar Bahaushe har zuwa yau. Daga ƙarshe kuma takardar za ta yi ƙoƙarin binciko abin da ke faruwa na tsakanin Allah wadai da Allah san barka a kan sauye-sauyen al'adun. Haka kuma takardar za ta bayar da shawarwari a kan yadda za a iya daƙile munanan al'adun da zamani ke kawowa. Sannan kuma takardar za ta yi ƙoƙarin bayyana al'adun da suka fi canacanta ga rayuwar Bahaushe. A ƙoƙarin gudanar da wannan aiki, an yi amfani da gogaggun hanyoyin tattara bayanai da suka haɗa da: Bitar ayyukan da suka gabata, karance-karancen bugaggun litattafai, haka kuma an samu tattataunawa da jama'a a yayin gudanar da wannan aikin. Binciken bai tsaya a nan ba kaɗai, har ila yau, an yi amfani da kafar yanar-gizo domin tattara kayan aikin wannan bincike.

 

1.0 Gabatarwa

Al'ummar Hausawa kamar kowace al'umma. Hausawa al'umma ce da al'adu ke riƙe da ita, wato suka mamaye rayuwarta tun daga haihuwa har zuwa mutuwa. Bunza (2002) ya bayyana cewar: Al'ada ita ce dukkanin rayuwar ɗan'Adam. Wato hanya ce da ɗan'Adam ke bi wajen gudanar da rayuwarsa tun daga lokacin da ya zo duniya har zuwa mutuwa. A ko'ina mutum ya samu kansa dole ne ya kasance a kan wata ɗabi'a da ya tashi da ita, to wannan ɗabi'a ita ake kira da al'ada. Haka kuma babu wata al'umma da za ta rayu a duniya ba tare da tana da wata al'ada da take bi ba.

 

1.1 Dubarun Bincike

Domin ɗaure ƙafar wannan binciken a turken da ya dace, an yi amfani da shahararrun hanyoyin tattara bayanai da suka haɗa da:

1- Karance-karancen bugaggun litattafai

2- Bitar ayyukan da suka gabata

3- Hira da jama'a

4- Amfani da kafar yanar-gizo

 

2.0 Waiwaye A Kan Ma'anar Aure Da Amfaninsa Ga Rayuwar Al'ummar Hausawa

 

Aure wani muhimmin al'amari ne ga rayuwar kowace al'umma. Haka kuma a gurin kowace al'umma aure abu ne da ke tattare da al'adu kala daban-daban wanda kuma haka lamarin yake a wurin al'ummar Hausawa. kamar yadda masana suka bayyana, aure alaƙa ce ta halaccin zama tare a tsakanin namiji da mace. Kuma aure ya samo asali ne tun a farkon ɗan'adam. Haka kuma al'adar yin aure ta kan bambanta daga wani zamani zuwa wani, ko daga wata al'umma zuwa wata. Muhimmancin yin aure ga rayuwar al'ummar Hausawa na tattare da wasu abubuwa da suka haɗa da:

1- Sama wa abin da aka haifa asali

2- Samun magada

3- Samun mazaje ta fuskar yaƙi

4- Haɓɓaka tattalin arziki ta fuskar noma da sha'anin kasuwanci

5- Raya sunnar ma'aiki (Wannan dalili ne da ya samu bayan zuwan addinin musulunci). Da dai sauransu.

 

2.1 Al'adun Aure Kafin Zuwan Musulunci (Lokacin Maguzanci)

 

A lokacin maguzanci da zarar saurayi ya ga budurwa a wajen bikin kalankuwa, matuƙar yarinyar ta amince da shi shi ma ya amince da ita sai ya bi ta gidansu, wato gidan iyayenta can zai rinƙa kwana har na tsawon kwana uku suna kwana a ɗaki ɗaya ba tare da faruwar wani abu a tsakaninsu ba. Haka ita ma yarinyar za ta bi shi gidan iyayensa su yi kwana huɗu. Ana yin haka ne domin iyayen su samu gamsuwar cewa yaran suna son junansu sosai. Da zarar iyayen sun fahimci haka daga nan sai maganar sa rana. Wannan al'ada ita ake kira "Tsarance"

 

-Sa Rana

A lokacin auren maguzawa a kan sanya rana ta musamman wadda ake da tabbacin mutane za su halarta. Kuma a kan yi haka ne ta amfani da shawarwarin iyayen amarya da masu alhaki daga cikin dangin ango. An fi yin irin wannan bikin a lokacin da ruwan sama ya ɗauke (Wato ba'a aikin gona)

 

-Kayan Ɗaurin Aure

Al'adar maguzawa ta tanadi kayayyakin da ake kawowa a matsayin kayan ɗaurin aure waɗanda suka haɗa da:

1- Tulunan giya

2- 'Ya'yan gauɗe

3- Ɗan akuyar maraici (Idan uban amarya ba ya da rai)

4- Akuyar maraici (Idan uwar amarya ba ta da rai)

5- Goro

6- Tabarmi

7- Kaji huɗu

8- Jar shirwa

9- Kaza mai jan gaba

10- Rago mai kwalli

11- Tunkiya, da dai sauransu.

 Waɗannan kayayyakin da aka gabatar a sama su danganta ne da nau'in tsafin da maguzawan ke yi na abin bautarsu saboda maguzawan sun bambanta daga na wani wuri zuwa wani, wata ƙila wanna dalilin ne ya sa al'adun suka bambanta.

 

2.2 Fuskoki Da Lafuzzan Ɗaurin Aure

 

Bambancin wurin zaman maguzawa kan janyo sauye-sauye na yadda ake yin ɗaurin aure a al'adarsu. Ga wasu daga ciki kamar haka:

1- Amfani da ƙasa: A ƙarƙashin wannan al'adar, wakilin ango da na amarya za su zo sai a tara ƙasa, daga nan sai wanda zai ɗaura aure ya samu wata 'yar sanda ya riƙe tare da ambaton wani furuci kamar haka "Ni ne wane (Ya faɗi sunansa) na ɗaura auren wane da wance na ga ɗan babbar bura-ubar da zai kwance shi" Sai ya buga sanda sau uku a saman wannan ƙasar da aka tara shi ke nan an ɗaura aure. Bayan wannan al'adar, akwai wasu al'adun da suka haɗa da:

2- Damar (Wannan shi ma wata siga ce ta yadda maguzawa ke ɗaura aure a da.

3- Amfani da kibiya ko ruwan fartanya (Wannan ma wata siga ce ta fasalin ɗaurin auren maguzawa a wancan lokacin)

 

2.3 Ƙalubalantar Ɗaurin Aure

 

A yayin da aka gama waɗannan al'adu na zage-zage a wajen ɗaurin aure kamar yadda aka ambata a sama, akwai kuma ƙalubalantar ɗaurin aure. A nan idan amarya ko ango wani daga cikinsu ya taɓa aikata wani abin kunya, to wani kan faɗi cewa ya raba ɗaurin auren saboda dalili kaza-da-kaza (Sai ya ambaci dalilin) daga nan sai dattijai su bincika, da zarar an tabbatar da wannan abin kunyar da gaske ne sai a raba auren nan take.

  Wannan bayanin kaɗan ne daga cikin al'adun sigar ɗaurin aure na lokacin maguzawa domin kuwa masana kamar su (Kruis, 1915) da (Fletche, 1929) da (Ibrahim, 1982) da (Yusuf, 1986) da wasunsu duk sun amince da cewar maguzawa su ne asalin Hausawa.

 

3.0 Al'adun Auren Hausawa Bayan Zuwan Addinin Musulunci

 

Bayan shigowar baƙin al'ummu ƙasar Hausa kamar zuwan Larabawa da Fulani, sai al'ummar Hausawa suka karɓi addinin musulunci suka ci gaba da gudanar da harkokin rayuwarsu kamar yadda addinin islama ya tanada. A ɓangaren al'du kuma, Hausawa sai suka yi watsi da al'adun tsafe-tsafe da maguzanci suka riƙi addini hannu bibbiyu. Karɓar addinin musulunci bai sanya Hausawa watsi da wasu al'adun nasu ba. Ma'ana dai ba su yi watsi da al'adun da addini bai haramta masu ba. Sha'anin aure ga rayuwar Bahaushe ya fara canzawa tun daga wurare kamar haka:

 

1- Bayyana so

 Kafin bayyana soyayya a tsakanin saurayi da budurwa dole sai an haɗu. Waɗannan wuraren haɗuwa kuwa sukan kasance ko dai dandali, ko wajen wani biki, ko kasuwa ko wurin talla da makamantansu. Bayan an haɗu tsakanin saurayi da budurwa sai bayyana so. Galibi a al'adar Hausawa saurayi kan bayyana wa budurwa soyayya ta hanyar aike. Wato sai ya samu ɗaya daga cikin ƙawayen wacce yake so ɗin ya faɗi mata, ita kuwa sai ta isar da saƙon soyayyarsa ga wacce yake so ɗin. Wani lokaci kuma akan yi wani abu da ake kira kamu, wato tun yarinya na ƙarama za a yi kamu, kuma galibi iyaye ne ke cewa sun yi wa ɗansu wane kamun wance, kuma shi ke nan haka lamarin zai kasance har su isa aure.

 

2- Kyauta

Bayan haɗuwa da bayyana soyayya kuma sai kyauta. Wannan waɗansu 'yan kayayyayaki ne da mai neman aure ko iyayensa ke kaiwa gidansu yarinyar da ake nema.

 

3- Lefe

Lefe wasu kayayyaki ne da ake haɗawa da suka shafi tufafi da kayan kwalliya gwargwadon ƙarfin mai nema auren. Ana zuba waɗannan kayayyaki ne a cikin Fantimoti ko kwalla ko akwatu.

 

4- Baiko

Wannan tabbatarwa ce da ake yi na an ba wa mai neman yarinya ita. Akan raba ɗan abin masarufi irin su alewa, biskit da sauransu.

 

6- Sa Rana

Wannan wata al'ada ce da ake ɗaukar kayayyaki daga gidansu mai neman aure zuwa gidan iyayen yarinyar da ake nema. Daga nan sai dukkan ɓangarorin biyu na yarinyar da na yaron su tsayar da rana guda wacce za a yi ɗaurin aure a cikin ta. Daga cikin kayan da ake kaiwa akwai: Goro, alewa, tabarma, kuɗi da sauransu. Daga nan sai ɗaurin aure.

 

7- Ɗaurin Aure

A ranar ɗaurin aure akan taru a ƙofar gidan iyayen amarya domin ɗaurin aure. Daga cikin abubuwan da ake gabatarwa a wajen ɗaurin aure akwai:

-Sadaki

-Waliyyai

-Shaidu

-Goro

-Siga

Daga waɗannan ababe da aka lissafa a sama shi ke nan sai addu'ar ɗaurin aure, ita kuma wannan ana yi ne kamar yadda addinin musulunci ya tanada. Wannan shi ne taƙaitaccen bayani dangane da sha'anin al'adun aure bayan zuwan addinin musulunci ƙasar Hausa.

 

4.0 Shawagin Zamani A kan Al'adun Auren Hausawa

 

Idan aka yi duba da bayanan da suka gabata za a tabbatar da cewar, zuwan addinin musulunci ya canza abubuwa da dama dangane da sha'anin al'adun aure na Hausawa, saboda haka ana iya cewa akalar zamani ta janyo al'ummar Hausawa cikin tsarin addini wanda hakan ya haddasa sauyawar wasu al'adu da suke gudana a yayin bikin aurensu musamman na lokacin maguzanci. To ai "Ba hawan ba saukar" Ganin yadda zamani ke shawagi cikin lamurran rayuwa, yanzu kuma wani zamani ya zo haɗe da sauye-sauye na wasu al'adu waɗanda a can baya ba a gudanar da su a cikin sha'anin aure. An samu canji ta fuskar ababe da dama kamar haka:

 

1- Wurin haɗuwa

Yanzu ana haɗuwa ne a shafukan sada zumunta da makarantu, wuraren biki, hotel da sauransu.

2- Bayyana soyayya

Yanzu ana amfani da wayar hannu, wasiƙa, haɗuwa ido-da-ido, kafafen sada zumunta da sauransu

3-Kayan na gani ina so

A wancan lokacin galibi akan yi amfani da kayan gona ne kamar su dawa, gero masara, amma yanzu sam ba haka ba ne

4- Lefe

Da akan zuba lefe ne cikin wani abu da ake kira lefe, daga baya kuma aka din sanyawa a fantimoti, kwalla ko akwati, amma yanzu ana sanyawa ne a cikin akwati mai taya ko firiza wadda ake sanya kayan sanyi a ciki, wai yanzu har a cikinta zuba lefe ake

 

5- Kafin a yi ɗaurin aure

Yanzu kafin a yi ɗaurin aure akan ware wasu ranaku da ake gudanar da wasu al'adu da suka haɗa da: Hotunan biki (Free weeding pictures) da ranar cin fara da cin wainar fulawa, ranar shan rake da ranar cin goriba, kallon ruwa da sauran al'adu barkatai. Wannan kuwa na ci gaba da faruwa ne sakamakon huɗɗa da wasu baƙin al'ummomi kamar Turawa da makamantansu.

 

5.0 Sakamakon Bincike

 

Sakamakon wannan binciken ya cimma matsaya guda a tsakanin waɗannan jimlolin guda biyu, wato "Allah wadai da Allah san barka." Da farko idan aka dubi yadda musulunci ya sauya tsarin wasu al'adu na al'ummar Hausawa, to za a ga cewa abu ne na Allah san barka domin kuwa da ma tsarin ya yi daidai da wasu al'adun na wancan lokacin. Haka kuma idan aka dubi al'adun gargajiyar Bahaushe za a fahimci cewa suna ɗauke da kyawawan halaye da darussa masu kyau na yanayin tsarin zama. Za a iya fahimtar haka  musamman idan aka kalli al'adar nan ta " Ƙalubalantar aure" wadda kai tsaye tana yin nuni da yin ishara da cewa ko a wancan lokacin ba a yarda da munanan ɗabi'u ba. idan kuwa mace ko namiji suka aikata hakan, to akwai yiyuwar ko aure ma ba za su samu damar yi ba don ko an ɗaura shi ana kwance shi idan aka tuna da wannan abin kunyar.

 

Ta fuskar zamanin da ake ciki kuwa a yanzu, to sai dai a ce Allah wadai, domin kuwa an kawo sabbin abubuwa ma su ruguza tarbiyya da lalata dukiya da fasiƙanci da zinace-zinace da shigar banza da yaɗa hotunan banza waɗanda addini da al'adar Hausawa duk ba su amince da su ba. Haka kuma idan aka dubi yadda ake gudanar da soyayya a lokacin maguzanci da kuma lokacin da Hausawa ke gudanar da al'adunsu bayan sun karɓi musulunci za a fahimci cewa, sha'anin aure soyayya ce da ƙaunar juna wadda ake ginawa bisa wasu dalilai da aka ambata tun a gabatarwar wannan aikin, amma yanzu zamani ya sa ana gina soyayya ne ta wani abu daban da ya danganci sha'awa ko kuma wani abu mai kama da haka. Duba da irin sauye-sauyen da ake samu na zamani da kuma rungumarsa da al'ummar Hausawa ke yi ya sa wannan muƙalar ke ba da shawarar cewa, al'ummar Hausawa su yi taka-tsan-tsan wajen sanya rigar kowacce irin al'ada da zamani ya kawo, domin kuwa bincike ya tabbatar da cewa rungumar irin waɗannan al'adu na haddasa mace-macen aure a tsakanin al'ummar Hausawan.

 

5.1 Kammalawa

 

A cikin wannan aiki da ya gabata za a ga cewar an waiwayi sha'anin al'adun aure tun na lokacin maguzanci. Haka kuma an bayyana kaɗan daga cikin dalilan da ke sa a yi auren. Har ila yau aikin bai tsaya a nan ba kaɗai, aikin ya waiwayi al'adun aure na al'ummar Hausawa bayan sun karɓi addinin musulunci. Wannan aikin ya yi wannan gajeren yawon ne domin ya tantance abin da aka samu ko kuma abin da ke faruwa dangane da zamani wanda ake da tabbacin cewar tuni ya yi caraf da akalar al'adun aure na al'ummar Hausawa wanda daga ƙarshe kuma aka bayyana kaɗan daga cikin irin sauye-sauyen da ake samu tare da bayyana amfaninsu da kuma illolinsu ga al'ummar. Daga ƙarshe kuma aka bayar da shawarwari tare da yin kira ga al'ummar don a ankarar da ita a kan abin da ke faruwa.

 

Manazarta

Auta, A.L. (2015). Aure A Rubutun Waƙoƙin Hausa. A Cikin Gusau S.M.

Habib A., Usman I.M, Da Rabi'u M.Z. (1982). Zaman Hausawa Bugu Na Biyu, Don Makarantun Gaba Da Firamare.

Ibrahim M., Yahaya I., Da Bello D. (1982). Hausa Custom. Northern Nigeria Publishing Company Zariya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. Da 'Yar'aduwa T.M. (1992). Sabuwar Hanyar  Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi Na Uku. University Press P.L.C, Ibadan Nigeria.

Post a Comment

0 Comments