Ticker

6/recent/ticker-posts

Intanet Da Duniyar Hausawa

Muƙalar da aka gabatar a ajin ALH 400 (Seminar), a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau, Jahar Zamfara, Nijeriya, (Disamba 2022 - Janairu, 2023).

Intanet

MUSTAPHA IBRAHIM

beenmala@gmail.com
+2348060671290

TSAKURE

Intanet dai yanzu ta zama hantsi leqa gidan kowa dan intanet ta zama wani sashe na rayuwar mutane, domin za'a shiga wani hali mara daɗi muddun aka ce ba intanet na ɗan wani lokaci, Hausa na ɗaya daga cikin yarukan da suke haskawa a duniyar intanet, don akwai manyan kafofin intanet na Hausa masu ɗinbin yawa da ake amfani da su. Saboda haka ya dace a duba wasu abubuwa da suka shafi wannan duniya ta intanet don qara fayyace wa 'yannan abubuwa kamar haka. Al'adun Hausawa a duniyar intanet. Ci gaba da ƙalubalen da ke cikin kafafen intanet na Hausa. Yaɗuwa da bunƙasar al'adun Hausawa. An yi Toamfani da rain Pulatoriyya (Platonism) wajen gudanar da binciken inda aka ɗauki intanet a matsayin duniya mai zaman kanta wanda kuma al’amuranta ke da alaƙa da abubuwan da ke gudana a duniyar yau da kullum. Sannan an yi amfani da hanyar ɗora aiki da ta dace da tunanin Bahaushe

 

GABATARWA

Hausa babban harshe ne a Afrika masu amfani da wannan harshe ake kira Hausawa, Hausawa na daga cikin harsunan Afrika da suka samu ta gomashi da daukaka a duniya. Haka kuma tana daya daga cikin manyan harsunan da ake amfani da su a intanet. Wanna dama da harshen Hausa ya samu ya sa shi ƙara haɓaka na shiga lungu da saƙo saboda intanet.

Intanet ta zama hantsi leka gidan kowa a wanna zamani shi yassa Hausawa suka yi amfani da wanna dama dan yaɗa harshen su da al'adun su dama adabin su baki daya.

Wannan bincike ya ɗauki intanet a matsayin duniya mai zaman kanta. A cikin duniyar akan tarar da duk waɗansu al’amura na yau da kullum suna gudana tamkar yadda suka kasance a sananniyar duniyar mutane.

  Wanna aiki zai duba wane ne Bahaushe, kuma micece intanet? Wace alaƙa ke tsakanin Bahaushe da internet? Kuma zai duba yadda ake samun bayanai daga intanet, kuma aikin zai fito da shaharar da harsen ya samu sanadiyar intanet da yadda yake yaɗuwa a duniya da irin sabbin kalmomin da harshen ya samu sanadiyar intanet da cigaban da ya samu ta hanyar ƙirƙirar shafukan da manhajojin da ke aiki da harshen Hausa, kuma wa'yannan abubuwa sun shafi dukkan rayuwar Bahaushe da mai jin harshen Hausa dama wanda yake koyon harshen na Hausa.

Kuma aikin zai duba matsalolin da intanet ta haifar ga harshen Hausa da kuma yanda ya dace ayi don magance su dama sauran maganganun masanan sashen

 

 

RA'IN BINCIKE

 

Wannan aiki zai duba abubuwa guda biyu kuma duk masu cin gashin kansu.

a. Bahaushe

b. Intanet.

A kan haka zamu yi wannan aiki a kan Bahaushen ra'i. Akwai masana da ke goyon bayan amfani da Bahaushen Rai wajen gudanar da bincike. Bunza, (2019) na ɗaya daga cikinsu inda yake cewa:

Lokaci ya yi da al’adunmu da tunanin magabatanmu ya yi tasiri ga ilimin mu da bincike-binciken ilimin mu. Ban ce ra’o’in Turawa na ilmi na a kan kuskure ba, amma a kowane irin al’amari gara a kai na hannu gida kafin a dawo a kama na dawa. (Bunza, 2019: 721).

A bangare na biyu kuma za muyi amfani da ra'in Pulatoriyya (Platonism). Pulatoriyya ya tafi kan cewa, rayuwa ta ƙunshi gaskiya biyu wanda ake gani da wanda ba a gani. Ɓoyayyiyar Gaskiya da mabiya Zahiriyya (Realism). Yan falsafa da ke kallon gaskiya a ɓoye take suna da ra’ayin cewa duk wani abin da ake gani a duniya rayawar zuci ce kawai. Misali, launin fari ko baƙi ko shuɗi da wani abuke ɗauke da shi, ba zahiri ba ne. A maimakon haka, rayawa da ƙwaƙalwa ta yi na samuwar launin ne ya sa har idanu ke kallon sa. Pulatoriyya ya tsaya ne a tsakaninsu. Ya haɗa tunanin duka biyu

 

HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

Domin samun ingantattun bayanai tare da cimma manufar binciken, an bi wasu tsararrun hanyoyin gudanar da bincike.

1. Fira: anyi fira da mutane daban-daban musamman masana a kan sannin al'adun Hausawa da masana a kan harkar intanet dan kara samun haske a kan abubuwan da suka shafi intanet.

2. Karance-karance: wanna ya shafi karance karancen maƙalu daban-daban da kundayen digiri musamman wa'yanda suka shafi intanet da kuma al'adun Hausawa

3. Nazari: nazartar duniyar intanet ta fuskoki daban-daban. Wannan ya haɗa da nazarin sigar duniyar da hada-hada da kai-komo da sauran al’amura da ke gudana cikinta.

4. Bincike a kan shafukan intanet musamman wa'yanda ke tafiya akan harshen Hausa da wasu shafukan sada zumunta da suka hada da

Academiya

Bakandamiya

Rumbun ilimi

Ta Sambo

BBC Hausa

VOA Hausa

Facebook

Telegram

TicTok. Da sauransu

 

WAI WAYE A KAN BAHAUSHE

 

Masana sun yi tsokace-tsokace masu tarin yawa a dangane da wanda ya kamata ya amsa sunan Bahaushe, a inda mafi yawa daga ciki suka bayyana cewa, "Bahaushe shi ne duk wani mutum wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa Hausawa ne, kuma sun haife shi a ƙasar Hausa, sannan ya ɗauki harshe da al'ada da ɗabi'u na Hausawa. To wannan shi ne Bahaushe."

Kasar Hausa ta fara ne daga Arewacin Nijeriya zuwa Kudancin Jamhuriyar Nijar, wanda nan ne mazaunin Hausawa na gado.

Abdalla, (2010) Ya bayyana cewa "Duk wanda salsalarsa babu wani yaren iyaye sai Hausa, to shi ne Bahaushe. Idan a jerin iyaye da kakanni akwai wanda ba Bahaushe bane, to kai ma ba Bahaushe bane. 'Na aro wannan ma’aunin bisa cewa Hausanci ƙirar halitta ce, ba lafazi ba. Misali: A ƙasar Turawa, in a cikin iyaye da kakanninka akwai baƙar fata, to ko ka fi madara fari a matsayin bakar fata kake.

A wannan ma’aunin, babu maganar zama a wata al’umma da kuma sanin yarenta, domin ka zama ɗan wannan al’ummar. Misali: Duk iya Larabcin baƙar fatan da ya zauna a garin Maka, ba za a taɓa kiransa Balarabe ba, ba wai kawai don akwai bambancin fatar Balarabe na ainihi da baƙar fata ba, aa, kawai ba Balarabe bane, kuma shi ma ya san haka.'

Saboda haka komai iya Hausar Babarbare da Bayerabe da Tibi da Inyamuri da Bafulatani ba zai taɓa zama Bahaushe ba, sai dai a kira su da "Hausawan Zamantakewa".

A cikin ƙamusun Hausa na Jami'ar Bayero, Kano (2006), an bayyana cewa "Bahaushe shi ne haifaffen mai magana da harshen Hausa da rayuwa irin ta Hausawa."

Tunda haka ne, yanzu a dai-dai wannan gaɓar zamu duba wasu abubuwa, mu yi nazarinsu, ta yadda za su zamo mana hoto ko madubin ƙara bayyana mana Bahaushe na ainihi. Daga cikinsu akwai:

1. HARSHE: Kamar yadda aka bayyana a cikin Ƙamusun Hausa na Jami'ar Bayero (2006), harshe na da ma'anoni daban-daban, amma ɗaya daga cikin ma'anarsa ita ce, harshe na nufin "Hanyar magana tsakanin al'umma iri ɗaya".

A saboda haka idan muka ɗauki wannan ma'ana ta harshe, zamu ga cewa dukkan wata ƙabila tana da harshe irin nata da take gudanar da harkokinta na yau da kullum da shi, kamar yadda ya zamo cewa harshen Balarabe shi ne Larabci, Bature kuma Turanci, Bayarbe kuma Yarabanci, to haka shi ma dukkan wani Bahaushe harshensa shi ne Hausa.

2. SIFFA: Ma'anar wannan kalma ita ce "Hanyar bayyana kamannin abu" Ƙamusun Hausa na Jami'ar Bayero (2006). Idan an ce haka kenan zai iya kasancewa bayyana siffar dabba ne ko mutum ko wani abu makamancin haka. To amma tunda muna yin magana ne a dangane da abun da ya shafi Bahaushe, to kenan batummu zai karkata ne ga bayyana siffa ta ɗan-Adam.

Abu ne sananne a duk lokacin da aka ce Bature kai tsaye za a hasaso cewa wannan mutumin fari ne, mai kwantaccen gashi da dogon hanci da sauransu. Haka ma dai idan ka je kan Larabawa suma tasu siffar daban take. Idan mun dawo maƙotanmu na kusa wato Fulani, su ma dai zamu tarar da suna da irin tasu siffar. Misali: suna da tsawo, sirara ne masu dogon hanci da dogon wuya da zarazaran yatsu da kwantaccen gashi da sauransu. Saboda haka shi ma Bahaushe kamar sauran ƙabilu yana da irin tasa siffar, wadda take bayyana shi a matsayin Bahaushe na ainihi, kamar yadda zamu gani a halin yanzu.

3. HALAYYA: Kamar yadda aka bayyana a cikin Ƙamusun Hausa na Jami'ar Bayero (2006), halayya na nufin "ɗabi'a, musamman ta mutum." Masana da manazarta sun bayyana halayyar Bahaushe da cewa, Bahaushe mutum ne mai halayya ta ƙwarai, abar koyi da yabawa. Sannan kuma sinadaran halayyar Bahaushe sun haɗar da:

i) ALKUNYA: Bahaushe mutum ne mai alkunya, a inda yake bayyana hakan a dukkan lokacin da wani abun kirki ya haɗa ku da shi, misalin hakan na bayyana a tsakanin mata da miji ko siriki da iyayen matarsa ko mace da sirikanta da kuma 'ya'yanta na fari. Wannan ne ma ya haifar da ɓoye suna ta yadda uwa bata iya furta sunan ɗanta na fari saboda alkunya.

ii) KAMA SANA'A: Bahaushe mutum ne mai riƙe sana'arsa da muhimmanci tun tale-tale, a inda zaka tarar da cewa kowacce sana'a har sarki ne da ita, wato shugaban duk masu yin irin wannan sana'ar, irin su noma, da kira, da farauta da rini da wanzanci da dukanci da sauransu.

iii) RIƘON ADDINI: Bahaushe mutum ne mai riko da addini, la'akari da yadda bayan ya karɓi addinin Musulunci ya rike shi hannu bibbiyu, har ya kai ga, a duk lokacin da aka ce wane Bahaushe ne, to abun da za a fara kawo wa shi ne Musulmi ne ko da kuwa ba hakan bane ba.

 

4. MUHALLI: A tsarin gidan Bahaushe, maigida shi ne shugaba a gidansa. Masana sun ƙara da cewa, duk matansa da yayansa, da sauran yaran gida da masu yi musu hidimomi, suna ƙarƙashinsa a matsayin mabiya. Maigida ne zai ɗauki nauyin ciyar da kowane mazauni a gidan, shi ne kuma zai yi wa kowa tufafin sakawa, ya kuma ba su makwanci, haka kuma, shi ne wanda zai shirya musu irin ayyukan da kowa zai yi, ya kuma raba wa kowa nasa aikin, ya kuma tabbatar da kowa ya yi aikin da ya ba shi. Idan ana buƙatar wani abu a gidan, shi maigidan ne za a tambaya, sai ya ba da izini kana a ɗauki abin. Haka kuma nauyin kare lafiyar mutanen gidan, da kare mutuncinsu da yi musu tarbiya duk a wuyan maigidan yake, a matsayinsa na shugaban gida.

Zaman gandu, wato gida-cikin-gida shi ne tsarin zaman Bahaushe na asali, inda yake zaune a cikin babban gida tare da magidanta fiye da goma, kowane da yankinsa a gidan, inda yake tare da rukunin iyalinsa a ƙarƙashin shugabancin Uban-gandu, wanda shi ne dattijo mafi tsufa a gidan, wanda shi ne babba a shekaru, ba wanda ya kai shi tsufa a gidan. Wannan tsoho, zai kasance a nasa rukunin tare da iyalinsa, akasari matansa da ƙananan yayansa waɗanda ba su isa aure ba. Saura manyan magidanta, kowanne yana da nasa rukunin, inda shi ma yake zaune da nasa iyalin. Irin wannan zama, zama ne na ‘yan’uwantaka da ƙara ƙulla zumunci, da taimakon yanuwa, da haɗa kai. Saboda za ka tarar komai nasu gabaɗaya suke gudanar da shi, kawunansu a haɗe suke, suna taruwa su yi aiki gabaɗaya, misali lokacin damuna sai duk su tafi wajen gonarsu ta Gandu su haɗu su nome ta sai kuma su bi sauran gonakin ‘yan’uwa suna nomawa har su gama. Wannan irin zama, zama ne na cuɗe- ni-in-cuɗe-ka, da kuma lumana ba ƙiyayya da gaba.

 

WAI WAYEWA KAN INTANET

An gudanar da rubuce-rubuce masu tarin yawa dangane da tarihin samuwar intanet da bunƙasar ta an Kawo tarihin tiryan-tiryan zai kasance tamkar maimaici ne ga ayyukan baya kawai ba tare da gabato da sabon al’amari ba. Kalmar intanet baƙuwa ce a fannin nazarin Hausa. Asalin kalmar a turanci ita ce “internet.” Masana da dama sun yi ƙoƙarin ba da maanar intanet. Umar (2002). Ya bayyana maanar intanet da cewa: Intanet kafa ce wadda ta haɗa bayanai daban-daban, kuma an sauƙaƙa hanyoyin amfani da waɗannan bayanai yadda kowa zai iya

Mukoshy, (2015) . Ya bayyana tasa ma’ana da cewa:

Intanet kafar sadarwa ce ta na’urorin zamani wadda ta game duk duniya. Tana ba da damar sadar da bayanai kowaɗan ne iri, kuma zuwa ko’ina a duniya cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

Amfani (2010). Cewa yayi: Intanet tsari ne da ya haɗa duniya, ta haɗakar layin iska na na'urori waɗanda ke amfani da tsare-tsaren yanar gizo don biya wa biliyoyin masu amfani buƙatu a faɗin duniya.

 

DUNIYAR INTANET GA AL'ADUN HAUSAWA

Idan ana maganar al’adu a jimlace, kafar intanet ta kasance taska ta al’adu. Wannan ba sabon abu ba ne. Tuni kafafen intanet suka kasance wani bagire da ake rubuce-rubuce dangane da al’adu. Ko bayan rubuce-rubuce, akwai hotuna da bidiyoyi dangane da al’adun al’ummomi daban-daban. Wannan ya haɗa da bayyanannu da ɓoyayyun al’adu. A matakin duniya, abubuwan da ake samu dangane da al’adu a kafafen intanet sun haɗa da:

Abinci

Sutura

Wasanni

Bukukuwa

Gine-gine da sauransu

Tuni hankalin masana da manazarta ya kai kan tasirin intanet a kan al’adun Hausawa. A wasu lokutan sukan yi rubutu da ke nuna wannan tasiri kai tsaye. A wasu lokuta kuwa, akan tsinci batun ne yayin da suke tattauna tasirin zamananci kan al’adun Hausawa. Ko ba komai dai, intanet na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da zamani ya zo da su, waɗanda kuma suke da matuƙar tasiri a rayuwar alumma. Abin lura a nan shi ne, yawancin ayyukan da aka gudanar a kan wannan batu sun karkata ne zuwa ga bayyana illolin intanet a kan al’adun Hausawa. Babban misali a nan shi ne, aikin Shehu da Rambo, (2019) mai taken: “Shafin Zumunta na Was’af. Tasirinsa ga Lalacewar Tarbiyyar ‘Ya’yan Hausawa.” Kai tsaye sun dubi yadda wannan shafi ke kai wa ga taɓarɓarewar al’adun al’ummar Hausawa musamman tarbiyya.

a. Wasannin Hausawa

Wasa dai na nufin duk wata magana da aka furta ko wani aiki da aka aikata da nufin raha da nishaɗi. ” Yayin da aka ce wasannin gargajiya kuwa, ana nufin wasannin Hausawa da suka kasance sanannu. Bayan haka, sun kasance na Hausa tsura ba waɗanda aka kwaikwaya daga baƙin al’ummu ba. Daga cikinsu akwai waɗanda suke da takamaimai wuri da lokacin aiwatarwa, wasu kuma har da sanannun kayan aiki da ake amfani da su yayin gudanar da wasannin. Daga cikin wasannin gargajiya na Hausawa akwai na furuci, wato waɗanda suka shafi magana. Sannan akwai wasannin kurma, wato waɗanda aikatawa ake yi ba tare da wani furuci ba.

b. Abincin Hausawa

Bai zama laifi ba, idan aka faɗi cewa kalmar abinci ba ararriyar kalma ba ce daga kowane harshe. Dalilan faɗin haka sun haɗa da kasancewar abinci ɗaya daga cikin abubuwa na farko da ɗan’adam zai fara cuɗanya da shi yayin da ya zo duniya.

Wannan na nuna cewa, dole ne ya samar wa kansa sunan da yake kira wannan abu da shi. Za ta iya yuwuwa Hausawa sun fara ambaton sunan abinci ne da furucin: “abin da za a ci” ko “abin da ake ci.” Sannu a hankali har aka gajarce shi zuwa abinci. Ma’anar abinci ita ce: duk wani abu da mutane ke haɗiyewa ko taunawa sannan ana cin su ne domin ɗanɗanonsu ko amfaninsu a jiki. Wanan ma'anar ta yi kama da ma’anar da aka samar a kafar Rumbun Ilimi inda suka ce abinci: “shi ne dukkan abin da za a ci sannan kuma ya bai wa jiki sinadaran da yake buƙata domin samun ƙarfi (Rumbun Ilimi, ND: 1).

5. Sana’o’in Hausawa

“A san mutum a san sana’arsa” in ji Hausawa. “Sana’a” ba Bahaushiyar kalma ba ce. An aro ta ne daga Larabci. A larabci tana nufin “aiki.” Sallau, Bayan tafiya ta yi tafiya sai ma’anar kalmar a wurin Bahaushe ta ƙara faɗaɗa har ta ƙunshi duk wani aiki da za a yi don gudanar da wani abu da za yi a musanya a tsakanin ɗaiɗaikun al’umma ko rukunin jama’a.”

 Sana’a ta ce “abin da mutum yake yi don sabawa kamar gini.”

Akwai bayanai sosai game da sano’o’in Hausawa daban-daban a duniyar intanet.

A kafar intanet mai suna Al’ummar Hausawa, Musa, (2019: 1) ya rubuta maƙala mai taken: “Sana’ar Kiyo a Ƙasar Hausa. A tarihin tattalin arziki da sanaoin Bahaushe, kiwo na da gurbi na musamman. Har ila yau, kiwon kaji sanannen alamari ne a gidajen Bahaushe. A inda aka fito,

da wuya a samu wani gidan Bahaushe da ba a kiwon kaji. Akwai sanannen kirarin

nan da ake yi wa kiwon kaji cewa: “’Yar ƙaramar dukiya da babbar riba.

 

 

AMFANIN INTANET GA HAUSAWA

 

Kafafen intanet na da matuƙar amfani wajen haɓaka harshe da yayata shi. Masana da dama sun yi rubuce-rubuce dangane da tasirin intanet da zamananci a kan al’adun Hausawa. Daga ciki akwai:

aikin Almajir, (2009) da Muhammad, (2011) da Magaji, (2018) da Shehu da Aliyu, (2019) da Shehu da Rambo, (2019) da Usman da Bunza, (2020). Abin lura a nan shi ne, mafi yawansu sun karkata ne kan fito da ire-iren illolin da intanet da zamananci ke da shi ga al’adun Hausawa. Duk da haka, akwai aikin da ya yi ƙoƙari matuƙa inda ya bugi jaki ya bugi taiki. Wannan aiki shi ne na Yartsakuwa, (2017). Aikin ya yi ƙoƙari matuƙa wajen zayyano amfani da kuma aibin kafafen intanet tsakanin shafi na 35-37. Wannan bincike ya nazarci ayyukan magabatan. Sakamakon ya nuna cewa, amfanin intanet ga Hausa da Hausawa sun haɗa da:

1. Samun Ilimi a Sauƙaƙe

Ɗaya daga cikin manyan alfanun intanet shi ne samun ilimi har gida. Ta hanyar amfani da intanet, mutum zai karanta nau’ukan rubuce-rubuce da dama yayin da yake kwance a ɗakinsa. Haka kuma, zai iya sauraron odiyo ko ya kalli bidiyoyi. Haƙiƙa wannan janyo nesa kusa ne tare da sauƙaƙawa. Misali, a shekarar 2020 da aka samu yaɗuwar cutar korona, ƙasashen duniya da dama sun komar da tsarin karatunsu kacokan zuwa kan intanet. Jamioin ƙasar Hausa ba su da wannan tsarin. Ko ba komai, Bahaushe ya ce: Ba a fafe gora ranar tafiya.

Intanet kafa ce ta neman ilimi. Akwai makarantu da dama da suka kasance saman intanet. Ɗalibai za su yi rigista da irin waɗannan makarantu daga duk wuraren da suke a faɗin duniya. Za su riƙa ɗaukar darusa ta intanet, su rubuta jinga ta intanet su kuma yi jarabawa ta intanet. Daga cikin irin waɗannan makarantu akwai:

a. Arizona State University–ASU Online

b. Boston University. (Boston, Massachusetts)

c. Indiana University–IU Online.

d. Northeastern University

e. UMass Online. (Amherst, Massachusetts)

Hausawa na iya morar wannan dama ta hanyar yin karatu a ƙasashen ƙetare ta kafar intanet. Baya ga haka, a yanzu haka akwai kafafen intanet na Hausa da suke ƙoƙarin samar da makarantu ta kafar intanet. Daga cikin masu wannan hoɓɓasa

 

a. Akwai masu gudanar da kafar Bakandamiya (https://bakandamiya.com/). Akwai

b. Akwai masu kafar Wikihausa waɗanda tuni suka fara koyar da kwasakwasai da suka haɗa da na koyan kwamfuta da girke-girke da sauran ɓangarorin ilimi da dama.

c. Akwai masu kafar academiya inada suke gabatar da maƙalu da kundayen digiri daban-daban musamman da harshen Hausa

d. Akwai rumbun ilimi inada suke da dukkan wani fanni na ilimi kuma a cikin harshen Hausa suna temake ma fagen ilimi sosai suma wannan kafar

2. Sauƙaƙawa

Sauƙaƙawa a nan bai taƙaita a kan sauƙin da mai karatu ke samu ba kaɗai. Yana nufin

(i) Sauƙin da marubuci ke samu, inda yana iya ɗora rubuce-rubucensa bisa intanet. Wannan hanya ta fi sauƙi inda ba zai kashe kuɗin buga littafi mai yawa ba.

(ii) Gwamnatoci da cibiyoyin ilimi na samun sauƙin ɗaukar nauyin ɗakunan karatu. Bayan littattafan da ake tarawa da kundaye da sauran abubuwan karatu,

(iii) Akwai kuma abin da ake kira e-library, wato ɗakin karatun intanet. Ɗakunan karatu na tara dubban ɗaruruwan littattafai a kan intanet. Da a ce sai an samo kwafinsu, lallai akwai buƙatar kuɗaɗe masu yawa da kuma gine-gine masu yawa inda za a ajiye su.

3. Bunƙasa Hausa

Kamar yadda ake bunƙasa Hausa ta hanyar rubuce-rubuce a duniyar zahiri, haka ma abin yake a duniyar intanet. Wani abu mai jan hankali shi ne, sau da dama rubutu bisa intanet ya fi yi wa matasa sauƙi a kan rubutu ta amfani da takarda da alƙalami. A haka ana samar da rubuce-rubuce da dama a duniyar intanet. Tare da ƙirƙirar wasu kalmomi dan ƙara bunƙasa harshen Hausa kammar yadda yazo daga kamfanin Algaita na fassara fina-finai daga wasu harsunan zuwa harshen Hausa. Misali:

Biyuni - Double body

Turken sadarwa - GPS

Ingantayya - Update

Saƙon sakaye - Mouse code

Zaizaya - Decode

 Ya rage ga masu kishin Hausa da su dage wajen bunƙasa alamarin domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

4. Yayata Hausa

Idan mutum ya ci gaba da rubutu domin amfanin Hausawa, to haɓaka ta kawai yake yi. Idan kuwa ya kasance cewa waɗanda ba Hausawa ba na amfana da rubutun, to a nan yana yayata ta ke nan. Babbar hanyar yayata Hausa cikin sauƙi a yau shi ne ta amfani da intanet. Wanda ke zaune a ƙasar Hausa na iya yin rubuce-rubuce da za su zaga duniya. Hakan kuwa na ƙara wa harshen sanuwa tare da ɗaga darajarsa cikin jerin harsunan duniya. Ba makawa, yayatuwar Hausa na daga cikin abin da ya fifita ta tare da ɗaga darajarta sama da tsaranta a yau. Duk da haka, “idan kana da kyau, sai ka ƙara da wanka.

 

KAFAFEN SADARWA

 

Kafafen yaɗa labarai na nufin hanyoyin sadarwa na zamani waɗanda kan iya bai wa ɗimbin jama’a damar samun bayanai da isar da saƙo kai tsaye.

Misali: kafar telebijin da Radiyo da Jarida. Kalmar “media” wadda aka fassara da Kafafen yaɗa labarai, a ƙarnoni biyu da suka shuɗe, ta kasance ana amfani da ita ne kawai ga abin da ya shafi Jaridu. Kafin daga baya (a faɗaɗa ma’anarta) ta ƙunshi Radiyo da Tallabijin.

Intanet ma, kafar sadarwa ce ta na’urorin zamani wadda ta game duk duniya. Tana ba da damar sadar da bayanai kowaɗanne iri, kuma zuwa ko’ina a duniya. Har wa yau, Intanet yana ɗauke da kafafen sadarwa barkatai, da suka haɗa da; babbar manhajar Gogul (Googol) da ta Korom (Chrome) da kuma ta Mozilla Faya fos, (Mozilla Firefox). Waɗabanda a cikinsu za a iya samun manhajar Imel (E-mail). da manhajar Jimel (Gmail) da manhajar Fesbuk (Facebook) da manhajar Was’af (WhatsApp) da manhajar Tuwita (Twitter) da manhajar Badu (Badoo) da manhajar Istagiram (Istgram) da manhajar Tugo (2go) da manhajar Telegiram (Telegram) da manhajar Wicat (WeChat) da manhajar Turu (True) da manhajar Linkin (LinkedIn) da manhajar Yutub (You Tube) da manhajar Sikayif (Skype) da manhajar Buloga (Blogger) da sauransu da dama da ba mu ambata ba.


HAUSA DA KAFAFEN SADARWA

Kusan ana iya cewa tsawon ƙarni ɗaya ko biyu, Hausa ta kasance daga cikin manyan harsuna da ke taka rawa ta fuskar sadarwa a kafafen yaɗa labarai na gida da wajen Nijeriya.

A yau, babu wata ƙasa doron duniya da take ji da kanta, face tana amfani da harshen Hausa a kafafen yaɗa labaranta. Musamman abin da ya shafi ɓangaren radiyo.

Alal misali: Gidan Radiyon BBC da ke London shi ne ya fara shirye-shiryen Hausa, kafin daga baya Gidan Radiyon Jamus (DW Hausa) da Muryar Amuruka (VOA) su biyo baya.

A halin yanzu akwai kafafen yaɗa labarai a manyan ƙasashe da ke amfani da Hausa, waɗanda suka haɗa da: Gidan Radiyo Faransa (FRI) da Gidan Radiyon ƙasar Sin (CRI)

Yusuf (2011) yana cewa, “Kafafen yaɗa labarai daga Nijeriya da Nijar da Ghana da

Kairo (Cairo) da ma wasu hukumomin yaɗa labarai na Afirika da dama, duk sun kasance suna amfani da Hausa wajen yaɗa labarai. Haka kuma, akwai wasu manyan kafafen yaɗa labarai na duniya da suke amfani da Hausa wajen yaɗa labarai da suka haɗa da: BBC London da VOA da Raiyo Moscow da Radiyo Peakin da Radiyo Germany da sauransu.

Harshen Hausa na ƙara haɓaka tare da tallata al’adunsa da kuma adabinsa ta hanyar shirye-shirye masu ɗimbin yawa da waɗannan kafafen yaɗa labarai ke gudanarwa a kowace rana.

 

 

MATSALOLIN DA HAUSA TAKE FUSKANTA A KAFAFEN INTANET

 

Duk da ɗimbin nasarorin da Hausa take samu a kafafen sadarwa, akwai tarin matsaloli kuma masu yawa da take fuskanta a waɗannan kafafen. Ɗaya daga cikin manyan waɗannan matsalolin da wannan takarda ta fi damuwa da su ita ce, matsalar rubutun

Hausa. Babu shakka duk wanda yake bibiyar waɗannan kafafen sadarwa na zamani zai ga cewa, babu wata kafa daga cikinsu da ta tsira daga kwamacalar rubutu. Wanda wannan ba ƙaramar matsala ba ce da take gurgunta harshen. Har wa yau, matsalar rashin amfani da jinsi yadda ya kamata, ita ma matsala ce da ta mamaye Hausa a kafafen sadarwa.

A nan, za mu ɗan bijiro da wasu ‘yan misalai dangane da yadda waɗannan matsaloli suke faruwa a wajen amfani da wannnan harshen a kafafen sadarwa. Misali:

Saɓa ƙaidar Amfani da Jinsi:

“An yi girgizar kasa da ya kai……” maimakon “An yi girgizar kasa da ta kai…….” (Voice of America (VOA), 4 ga Junairu, 2016. Shirin safe “…Wane waina ake toyawa...... ? maimakon“…Wace waina ake toyawa?......” (BBC Hausa, 1 ga Fibirairu, 2017 shirin safe, labarai daga A’isha Sharif Baffa). “…sai dai wannan bitar an shirya wa ‘yan kasuwa ce…” maimakon “…sai dai wannan bitar an shirya wa ‘yan kasuwa ne…” (Radio France International (RFI), Alhamis 7 ga Junairu, 2016. Shirin safe, na Kasuwa a Kai Miki Dole, shirin Musa Kutama).

 

Matsalar Saɓa Tsarin Rubutu:

An yi taruka daban-daban a lokuta mabambanta, inda masana suka tattauna domin daidaita qa’idojin rubutun Hausa. Taro na qarshe kamar yadda Yahaya (2002) ya bayyana shi ne, wanda aka yi a babban birnin qasar Nijar, wato Yamai.

A wannan taron ne aka yi matsaya guda a kan daidaitaccen tsarin rubutun Hausa a Nijeriya da Nijar. Babbar matsalar da ake fama da ita a yau ita ce, mafi yawan masu rubutu da harshen Hausa, ba su bin wannan tsari na rubutu da aka yi matsaya a kansh,i wasu da dama ba su ma san meye tsarin ya shata a wajen rubutu ba, wannan kuma yana haifar da tarnaƙi sosai.

 

Gurɓata Tarbiyya:

Intanet tana bada gudunmawa sosai wurin ɓata tarbiyyar ƴaƴan Hausawa, domin kamin yawaitar intanet ba za'a taba ganin ƴaƴan Hausawa suna shiga ta batsa shiga ta tsiraici shiga ta Allah wadai ba don suna jin nauyin yin haka, amma a yanzu zakaga ƴaƴan Hausawa suna shiga ta tsiraici suna raye-raye tamkar ba diyan Hausawa ba suna ɗorawa a shafunan intanet daban daban.

Yawaitar kallon fina-finai na Batsa da na yammacin duniya a shekarun baya yara basu san yanda wannan rayuwa take ba ta sha'awa ko ace ta saduwa amma a sanadin intanet zakaga yaron da bai wuce shekara sha biyar ba yasan yadda zai shiga intanet ya dauko irin waƴannan fina-finai da basu dace ba

 

Ɓata Al'adu:

Intanet ta taka muhimmiyar rawa wajen bata al'adun Hausawa, kamin intanet ba za'a samu irin waƴannan gurbatattun al'adun ba na rashin kunya da rashin ganin girman manya, dan a yanzu zakaga ƙaramin yaro ya hau kafar intanet yana zagin shuwagabannin ko sarakuna ba tare da ganin girman su ba ko rashin sanin ya kamata ba. A yanzu idan kaga wasu abubuwan a TicTok sai ka rantse ba Hausawa bane sai in kaji sunyi magana ko kaga wasu daga cikin al'adun su sannan zaka yarda cewa hausawa ne don al'adun da suka nunawa Sam bazakace Hausawa bane.

A yanzu zakaga yar Bahaushe ta dasa ɗauɗauka tana rawa tana bayyana duk wata halitta da Allah ya yi mata tana yada ta ga duniya sai kace ba ƴar Hausawa ba.

 

INA MAFITA

Mafita a nan ita ce kara ƙaimi wuri kiraye kiraye kan dai-dai taciyar hanya da kara yaɗa irin illolin da waƴannan abubuwa suke yi da tashi tsaye wurin kula da irin abubuwan da yara suke ma'amala da su, da bibiyar na'urorin da wayoyin da yara ke amfani da su, dan sanin irin abubuwan da suke yi a wanna duniya, kai kuma matsayinka na babba mai hankali sai ka san irin ɗanbonin da zaka rika ɗorawa su a wayoyin su da na'urorin su da shawarwari na hikima da jan hankali cikin nishadi, da kara jawo yara ga jiki don ta wanna hanya ce zaka dora yaro duk yadda kake so in kana bashi isasshen lokaci dan kula da shi da aza shi a kan irin tarbiyyar da kakaso. Allah ya sa mu dace.

 

KAMMALAWA

Wannan aiki yayi ƙoƙarin fito da Bahaushe da irin halayensa da wurin zaman sa da Yaren sa da ma abinci Bahaushe. Kuma Aikin ya duba intanet da irin ma'amalar Bahaushe a duniyar internet da irin cigaban da Harshen Hausa ke samu duk a sanadiyar wanna duniya ta intanet, da irin yadda Hausa ke haɗe wasu yaruka musamman sanadiyar intanet, kuma aikin yayi wai waye kan irin matsalolin da suke cima Bahaushe tuwo a ƙwarya da yadda ya kamata a bi don magance wayyanan matsaloli, musamman na yada batsa a shafukan internet dama shafukan sadarwa ba ki daya

MANAZARTA

Abubakar, N. da Mansur, A. (2018). "Harshe da Adabi, Hanyoyi Ne Na Samar da Wanzuwar Zaman lafiya da cigaba mai ɗorawa" Katsina. Takardar da aka gabatar a Sahen Nazarin Yarukan Afurka. Al'Qalam University, Katsina.

Abubakar, N.(2016). "Harshe Hausa a kafafen yaɗa labarai."

Sokoto. Takardar da aka gabatar a taron karawa juna sani, A Sahen Nazarin Fasaha da Addini a Jami'ar Usman Danfodiyo dake Sokoto. 1-3 ga watan Maris 2016.

Adamu, A.U. (2002). "Hausa Language and Capture on the Internet" an dauko ranar 01s tgawatan Janairun 2023 A

Amfani, A.H. (2010). "Hausa Internet Terms. " London. Semina paper presents at Department of Anthropology, University of London

Mukoshy, J. I.( 2015). “Nahawun Keɓaɓɓun Kalmomin Intanet na Hausa.” Kaduna:

Muƙalar da aka Gabatar a Taron ƙarawa Juna Sani a Jami’ar Jihar Kaduna.

Sani, A-U. (2021). "Zamani Zo Mutafi, Al'adun Hausawa a Duniya Intanet." Sokoto. Kundin gigiri na farko da aka gabatar a Sashen Nazarin Yarukan Najeriya, a Jami'ar Usman Danfodiyo dake Sokoto.

Sani, A-U.(2021). "Promoting the use of the Hausa language on internet." An ɗauko 11 fa watan Janairu 2023 A

Yahaya, I.Y. (2002). "Hausa a Rubuce : Tarihin rubuce-rubuce a cikin Hausa." Zaria. Nothan Nigeria publishing Company.

Zaruƙ, E.M da wasu (2005). "Sabuwar Hanya Nazarin Hausa." Ibadan. University press PLC

Post a Comment

0 Comments