Muƙalar da aka gabatar a ajin ALH 400 (Seminar), a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau, Jahar Zamfara, Nijeriya, (Disamba 2022 - Janairu, 2023).
Ruƙayya Yusuf S/Fada
08034978078
rukayyasfada@gmail.com
Tsakure
Wannan muƙala mai taken
‘Tasirin Auren Hausawa a kan Yarbawa mazauna Gusau’ muƙala ce da ta yi duba a kan al’adun Hausawa na aure
waɗanda suka yi tasiri a kan Yarbawa mazauna Gusau. Muƙalar ta gano al’adun waɗanda su ke al-adu ne na Hausawa
Yarbawa mazauna Gusau suka ɗauka suka saka a cikin al’adun Auren su sanadiyyar cudanya
ta tsawon lokaci. A yayin gudanar wannan bincike an yi amfani da
manya-manyan hanyoyin gudanar da bincike waɗanda suka hada da:
a.
Bitar
ayyukan da suka gabata
b.
Fira
da wasu Al’ummar Yarbawa da ke Gusau
c.
Ziyarar
wasu shafukan yanar gizo
d.
Karatun
bugaggun Littafai
1.0
Gabatarwa
Hausawa da Yarabawa al’ummu ne daban-daban, sai dai kuma
sun kasance suna maƙwabtaka da junansu. Wannan ya sa
al’ummun suke da kusanci har wasu sukan kasance a ƙasar wasu. Ma’ana dai Hausawa
kan je ƙasar Yarabawa su zauna su yi
kasuwanci ko wata sana’a. Haka ma
Yarabawa kan zo ƙasar Hausa su zauna su yi
kasuwanci ko wata sana’a. Wannan ba
sabon al’amari ba ne idan aka yi la’akari da yadda kowace al’umma ta kasance a ƙasar wata.
Kasancewar ƙasar da ake kira
Nijeriya a yau ta haɗa da wani yanki na ƙasar Hausa da
kuma ƙasar Yarabawa wannan ya taimaka wajen haɗuwar al’ummun
biyu (Hausawa da Yarabawa). Akwai kuma sana’ar fatauci wadda tun kafin a raɗa wa Nijeriya
suna ake yin ta wadda Hausawa kan je a wasu ƙasashe daga ciki har da ƙasar Yarabawa. Wannan ma ya taimaka wajen samun cuɗanya tsakanin
Hausawan da Yarabawa. Dangane da Yarabawa da suke zaune a garin Gusau, wannan dalili
yasa aka samu musayar auratayya a tsakanin al’ummun biyu sanadiyyar zama
wuri guda
1.1
Manufar Bincike
Babbar manufar wannan binciken ita ce, binciko irin hulɗa da ke tsakanin
Hausawan garin Gusau da Yarabawan mazauna
garin Gusau. Akwai kuma wasu
manufofi da suka haɗa da:
i.
Fito
da irin cuɗanya da ta gudana tsakanin
al’ummun biyu wato Hausawa da Yarabawa.
ii.
Fito
da al’adun Hausawa na Aure da sukayi tasiri a kan na Yarbawa mazauna Gusau.
1.2
Matsalolin Bincike
Nazarce-nazarce sun gudana a kan abin da ya shafi tasirin aure ko wata al’ada ko wani harshe a kan wani ko
ma cuɗanya tsakanin
wata al’umma da wata daban wadda
ke hardasa tasirin wani abu a kan wani kamar da Burgress da Locke, (19530 da
Rauf, (1977) da Funtua, (2010) da Rambo, (2013) da Auta, (2014) duk sun yi
magana a kan aure. Sai dai duk
binciken da aka zo da shi babu wanda ya kalli cuɗanyar Hausawa da
Yarabawan gari Gusau. Babu shakka waɗannan al’ummu
biyu sun yi cuɗanya a tsakaninsu kuma cuɗanyar ta haifar da
wani sakamako, amma manazarta hankalinsu bai kai ga wannan cuɗanyar ba. Yin wannan cuɗanyar ya haifar da tasirin bikin Hausawa a kan na
Yarabawa mazauna garin Gusau.
1.3
Hanyoyin Gudanar da Bincike
Wannan maƙalar ta kammala
ne ta hanyar hira da wasu mazauna unguwannin
da Yarabawa suke a garin Gusau da ma
wasu Hausawa da suke zaune a garin na Gusau. An kuma tambayi wasu masu ilmi dangane da kasantuwa da cuɗanya tsakanin
al’ummu biyu. Haka kuma an bi hanyar karance-karancen bugaggun littattafai da kundaye
da muƙalu da masana da manazarta suka gudanar. Wannan ya ba da
damar tattara dukka bayanan da aka gina wannan bincike.
1.4. Ra’in Bincike
An zaɓi a ɗora wannan maƙalar a kan ra’in Cuɗanya
Bourhis (Interraction). Bourhis ya assasa wannan ra’i, kuma ya bayyana
cewa, ta fuskar hulɗa da cuɗanya tsakanin wata al’umma da wata ana samun wata al’umma
ta yi tasiri a kan wata. Bourhis ya ƙara da cewa, ana
samun cuɗanya ta fuskar karɓar horo,wato
mutum ya samu horo kafin ya tsunduma cikin sha’anin rayuwar wasu[1].
Wannan maƙalar ta mayar da hankali ne wajen
duba cuɗanya tsakanin Hausawan garin Gusau da Yarabawa mazauna garin Gusau tare da
duba irin tasirin da harshen Hausa ko Hausawan suka yi a kan Yarabawa.
Al’ada kalma ce da aka aro ta daga Larabci aka mayar
da ita Yar Gida a Hausa ma’anar ta ita ce sabbaben abu wato abin da aka saba da
shi kenan
Dangambo (1984) cewa ya yi Al’ada it ace abin da aka
saba yi yau da gobe.
2.0 Tasiri
Tasiri ya nufin wani abu ya yi amfani a kan wani abu
na kwarai ko na banza. Kamar yadda aka sani idan Kabila biyu wuri guda to wadda ta fi karfi a ciki zata
nashe mai raunin.
Kasancewar garin Gusau gari ne na Hausawa daga
bisani Yarbawa suka shigo garin sai aka samu hulda tsakanin al’ummun biyu wanda
haka ya haifar da mu’amula a tsakaninsu wadda ta hada da harda ta aurenya,
wannan dalilin ne yasa aka samu sauyin al’adu ta fuskar yadda suke gudanar da
bikin aurensu sakamakon auren Hausawa ko kuma bayar da aure ga Hausawa.
2.1
Ma’anar Aure
Aure alaƙa ce ta halaccin
zama tsakanin miji da mata, ana yin sa ne domin shi aure sunna ce ta Annabi
Muhammada Rasulullahi (S.A.W) domin tsarkaka zuri’a. Aure muhimmin abu ne ga
al’umma saboda haka akwai hanyoyi da matakai na tabbatar da shi. Mataki na
farko shi ne neman aure. Haka kuma akwai wasu matakai na wali, da dukiyar aure da
sauransu.
Rambo, (2013), ya ruwaito, Burgress da Locke, (1953) na
cewa “Aure zamantakewa ce ta amincewar mutum ɗaya ko fiye da ɗaya ko mace ɗaya ko fiye da ɗaya mai dangantakar
mata da miji”. Rauf, (1977:78) ya bayyana aure da: “Ƙulla yarjejeniya da za ta haifar da halaccin
saduwa da mace da samun zuri’a. Kuma wani ɓangare ne na
mu’amala da ibada”.
Auren gargajiya na Hausawa ya danganci zaman tare a
tsakanin namiji da mace a bisa yardar juna ko amincewar dangi ta hanyar wasu ƙa’idoji na al’ada ko na addini. Ibrahim, (1985:i). Aure
muhimmin al’amari ne ba kawai a wurin al’ummar Hausawa, har ga sauran
al’ummomin duniya gaba ɗaya.[2]
A gudummuwa irin wannan za a iya cewa: “Aure na nufin haɗuwa ko ratsawar
wani abu a cikin wani abu, mutum ko dabba ko tsiri da makamantansu. Domin samun
albarkar da ke tattare da abubuwan da suka haɗu ko suka ratsa
juna”.
Idan kuma aka kalli ma’anar a addinance za a iya cewa,
“Aure wata hanya ce ta baiwa namiji da macce damar zama tare da saduwa ta
hanyar jin daɗi da mutunta junansu. Ita wannan hanya ko yarjejeniya ana
gabatar da ita ne a gaban shaidu tare da yanka sadaki, kuma yadda addinin
musulunci ya ƙayyade a kuma zartar da shi ta
hanyar da sunnar Manzon Allah (SAW) ta tanada.
Daga ma’anoni da suka gabata za’a iya cewa aure hanya ce
ta hada ko kulla dangantaka tsakanin Mace da Namiji waɗanda za su zauna
tare kuma a guri daya a matsayin mata da miji wacce kowace irin al’ada ta duniya ta
amince da ita a kan dangantaka ta din-din-din domin yawaitar al’umma da kuma
cigabanta.
2.2 Hausawa
Al’umma ce dake zaune a Arewa masu yammacin tarayyar Nijeriya. Da
kudu masu yammacin jamhuriyar Nijar. Al’umma ce mai dinbin yawa, sun bazu a
cikin kasashen Afirka. Da kasashen Larabawa, kuma a al’adance masu matukar
hazaka ne, akalla akwai sama da miliyan hamsin waɗanda harshen
Hausa shi ne asalin harshen su. A tarihi kabilar Hausawa na tattare a salsalar
birane watau alkarya. Hausawa dai sun samu kafa daularsu ne tun daga 1300’s,
sa’adda suka sami nasarori kamar su daular Mali, Songhai, Borno da kuma Fulani,
a karni na 19 Hausawa suna amfani da Doki ne domin yin sifiri da balaguro.
Mutane sama da miliyan hamsin ne magana da harshen Hausa a Nijeriya da Nijar da
Arewacin Ghana da kuma wasu Al’umma daga yankin Kaolak a Senigal har zuwa
Khartum dake kasar Sudan asalin inda zuciyar Hausawa take shine garin Kano,
Katsina da Sokoto.
2.3 Tsokaci a Kan Al’ummar
Yarabawa
Al’ummar
Yarabawa kamar sauran al’ummu da suke zaune a cikin ƙasar Afrika. Kamar yadda ya zo a ƙarni na 19, cewa al’ummar sun samu asalin sunan na su daga
Hausawa, wato ‘YARRIBA’. Wanda ya samu karɓuwa har bayan da
Turawan Mulkin Mallaka da masu ‘yaɗa addinin Kirista suka sauya yadda ake furta kalmar ta
koma “Yaruba” cikin sauƙi.Usman (2003:107-111).
Manazarcin dai ya ƙara da cewa, wannan suna na Yoruba ya samu asali ne ga daga cibiyar
Yarabawa wato Oyo. A cikin wannan ƙarni na sha
tara. Babu tantama wannan ra’ayin yana da tangarɗa, musamman idan
muka lura da kalmar da aka ta’allaƙa da ita a
matsayin asali. Haka kuma za a iya yarda da cewa, kalmar ta samo asali ne daga
su kansu Yarabawan da suke cewa, “AWA OMO YORUBA” wato (Mu ɗiyan Yoruba),
wannan ya fi zama ƙwaƙƙwaran dalilin da za a iya dogaro da shi fiye da
wancan.Usman (2003:107-111),
Ban da
waɗannan ra’ayoyi akwai ma wasu ra’ayoyi da aka samu a cikin
wasu rubuce-rubucen tarihi da tarihihi. Misali mu duba wani aikin da Shaihin
Malami Muhammadu B. Masani Al-katsinawi (d. 1078 A.H.-1667 A.D) ya yi da wani
littafi mai taken Azharul-Ruba Fi Akhbar
Bilad Yarba. Akwai wani littafi na Muhammadu Bello mai taken Infaqul Maysur. Wanda ya yi bayani a kan
Yarabawa a yunƙurinsa na bayanin ƙasar Baƙaƙen fata (Tukrur). Bayansa kuma akwai wani aiki da wani
limamin Kirista mai suna Rev. Samuel Johnson ya rubuta a 1897 A.D.
kuma ya ƙara tabbatar da abin da Muhammadu
Bello ya faɗa a cikin aikinsa game da Yarabawa.
Su dai
Yarabawa sun kasance masu yin hijira daga ainihin ƙasarsu ta haihuwa zuwa wata domin nema. Kuma sun ɗauki Ile-Ife a
matsayin wata cibiya ta su. duk da cewa ba a can kaɗai suke ba. ko dai
yaya lamarin yake tarihi ya bayyana cewa, babu wani musu, asalin Yarabawa daga
zuri’ar KWA ta yankin Afrika suka fito. Kuma suna da dangantaka da harsuna
kamar Igala, da Igbo, da Edo, da Idoma, da kuma Nupe da Makamantansu.Usman (2003:107-111),
Akwai Yarabawan yankin
Arewa maso Yamma, wato Yarabawan Oyo da
Oshun, da Ibadan, da yankin Arewacin Egba. Akwai kuma na Kudu maso Gabas waɗanda suka haɗa da Ondo, da
Owo, da Ikale, da Ijebu da kuma na yankin Ekiti. Kuma suna da bambancin karin
harsuna a tsakaninsu. Yanzu haka wurin da suka zaune shi ne Kudu maso Yamma wanda
ya haɗa da jihar Legas, da Ogun, da Ondo, da Oshun, da kuma Oyo.
(Usman, 2003:107-111).
2.4 ZuwanYarabawan Gusau
Yarabawa
sun zo Gusau rukuni-rukuni. Rukunin Yarabawan da suka zo Gusau na farko sun zo
ne tun zamanin zuwan Turawan mulkin mallaka wato shekarar 1903-1960. Amma daga ƙididdigar ƙidaya da aka yi
a 1952 an bayyana cewa, Gusau tana da kimanin mutane 83, 884, ciki kuwa harda
Hausawa da Fulani da Igbo da Yoruba da Maguzawa. Daga cikin Yarabawa sun kai
kimanin 963. Sai a shekarar 1991 aka sake ƙidaya yayin da aka samu adadin mutum 132, 390, daga ciki
Yarabawa suna da 1,522.Usman, (2003:111)
Rukunin
farko na Yarabawa da suka zo a Gusau ana sa ran sun zo tun a shekarar 1910.
Usman, (2003:113), ya bayyana cewa, a wata tattaunawa da ya yi da wani mai suna
Mal. Raji mutumin Uyo ya bayyana masa cewa, “Yarabawan farko da suka zo sun zo
ne sakamakon Turawan mulkin mallaka kuma sun zo ne domin yin aikin dafa abinci da
raino da tuƙin mota. Kuma su Turawan suke yi
wa wannan hidima.
Rukuni
na biyu da suka zo kuwa sun zo ne sakamakon gina hanyar jirgin ƙasa a
shekarar 1917, bayan gama
layin dogo a shekarar 1927 aka buɗe shi. Haka kuma an buɗe Coci a
shekarar 1926 domin ma’aikata
da suke kula da layin dogo.
Sai kuma
rukuni na uku da suka zo a
shekarar 1965 har zuwa
1970 su kuma waɗannan sun zo ne a sakamakon aikin kamfani na masaƙu da kuma na casa da mai. Ko bayan waɗannan Yarabawan
akwai waɗanda suka zo sakamakon tuƙin mota da dafa abinci da raino da masu aikin layin dogo.Akwai
kuma ‘yan kasuwa,duk sun zo sun zauna a Gusau kuma sun zama ‘yan ƙasa. Yarabawa sun fi yawa a Unguwar Sabon-gari, kuma suna
da sarki a unguwar. Duk da cewa ba unguwar Sabon-gari kaɗai suke ba,
misali idan aka je unguwar Damɓa a Gusau za a tarar akwai
Yarabawa masu yawa a can kuma suna da nasu Sarki. Yarabawan da suke a unguwar
Sabon-gari sun fi Hausawa yawa, kuma sun kai kimanin kashi 95% a unguwar.Usman,
(2003:111)
Mafi
yawan kayan da Yarabawa suka zo da su daga ƙasarsu ba su wuce, goro da ayaba ba. Idan
suka zo nan ƙasar Hausa kuwa sai su sayi
gishiri da barkono da fatar dabbobi da gyaɗa da rogo da
albasa da makamantansu.Usman, (2003:111)
Akwai
rukuni na huɗu da ake sa ran sun zo a shekarar 1969 zuwa 1970
sakamakon sana’a da neman mafaka, duk da cewa ba kowane Bayarbe ne ya zo don
neman mafaka ba, (Usman, 2003: 111-120).
2.5
Taƙaitaccen
Tarihin Garin Gusau
Garin
Gusau, gari ne da a can baya yake a cikin tsohuwar daular Katsina, yanzu kuma
ita ce babban birnin jihar Zamfara. Mafi yawan mutanen da ke zaune a wannan
gari Katsinawa da Zamfarawa ne, su kuma waɗannan ƙabilu dukkansu Hausawa ne. Gusau, (2014:18) Kasancewar wannan gari (Gusau) yana a ƙasar Hausa kuma akwai albarkatun noma, ya sa ya albarkatu
da yawan baƙi kamar Yarabawa da Inyamurai
(Igbo) da wasu ƙabilu masu saye da sayarwa na daga
kayan da ake nomawa a wannan gari da ma jihar baki ɗaya.
Kamar
yadda tarihi ya gabata an kafa garin ne a shekarar 1811, bayan tasowa daga
‘yandoto a shekarar 1806. Gusau na daga cikin manyan garuruwan tsohuwar jihar
Sakkwato kafin daga bisani ya zama babban birnin jihar Zamfara a shekarar 1996.
Kundin bayanin tarihi na ƙasa na 1920 ya
nuna, garin yana kan titin Sakkwato zuwa Zariya ne, kilomita 179 tsakaninsa da
Zariya, kolimita 210 tsakaninsa da Sakkwato. Daga gabas ya yi iyaka da ƙasar Katsina da ta Kwatarkwashi daga Arewa kuma ya yi
iyaka da ƙasar Ƙaura, daga Yamma kuwa ya yi
iyaka da ƙasar Bunguɗu. Ta ɓangaren Kudu
kuma ya yi iyaka da ƙasar Ɗansadau da Tsafe, (Gusau, 2012:7)
Kasancewar
almajirin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo wato malam Sambo Ɗan Ashafa ya kafa Gusau, wanda yake da shi da jama’arsa
ba ruwansu da bautar iskoki, ko tsafi irin wanda Hausawa ke yi kafin zuwan
addinin Musulunci, wato garin Gusau ba ya da tarihin jahiliyya,
haka ta sa duk al’adun Gusawa, al’adu ne irin na Musulunci, kuma
shigowar wasu mutane wato baƙi a Gusau, ba ta
gurɓata waɗannan kyawawan al’adu ba, domin kuwa mafi yawan baƙin da suka tahowa malamai ne na Musulunci da
almajirai, Fulani da wasunsu kan taho garin don tsira da addininsu da
mutuncinsu da kuma dukiyarsu.
3.0
Tasirin Auren Hausawa A kan na Yarbawa
Kasancewar kowace al’umma tana da nata tsarin yadda
take gudanar da bukukuwanta amma sakamakon cudanya a kan samu nason al’adu ta
sanadiyyar cudanya a tsaninsu.
Al’adun auren Hausawa sun sha bam-bam dana Yarbawa amma
a sanadiyyar zamantakewarsu wuri daya yasa al’adun Hausawa sukayi tasiri akan
na Yarbawan mazauna Gusau, gasu kamar haka:
i.
Nagani Ina so:
Wannan wata al’ada ce da Hausawa sukeyi wadda idan Namiji ya ga Macce
yana so zai saye kayyaki kamar:
Cingam, Biskit, Lemu, Goro da Ruwa ya tura akai gidansu domin neman aurenta. A da Yarbawa ba su
yin wannan al’adar amma a yanzu suna yi kuma suna kiran nagani ina so da “IYOJU” a
harshen yarbanci.
ii.
Lefe: kalmar ta
samo asali ne daga wani akwati na kaba da Hausawa ke sakawa
wanda a da shi ne ake kai kayan aure. Lefe na nufin kayan da Ango ke kaiwa Amarya a lokacin neman aure waɗanda suka
hada da: Atamfofi, Leshi, Takalmi, Jikka, kayan kwalliya akwati
da sauransu. A al’adar Yarbawa namiji baya yiwa Mace Lefe Idan zai aure ta sai da akwai wata al’ada ta su wadda ta yi kama da wannan, al’adar itace Ango zai yi wa Amaryar kayan cin biki, galibi
wadannan kayan basu wuce kala Ukku kuma yana yin wadannan
kayan ne ta hanyar yin anko tsakanin
shi da Amaryar, Idan Leshi zai dunka mata ya kan saye yadi goma sha biyar ya dauki yadi goma ya bata yadi biyar. A
harshen Yarbawa suna kiran wadannan kayan da “IGBA IYAWO”. To amma a sakamakon
auratayya tsakanin Yarbawa da Hausawa yasa yanzu suna yin Lefe
iii.
Kayan Ɗaki: Komattsai ne da iyayen Amarya tare da taimakon dangi
suke haɗuwa a kaiwa amarya waɗanda suka hada da: Manyan Kujeru, Gado, Katifa,
Durowa da makamantansu. Al’ada ce wadda Hausawa suke yi amma a sakamokon cuɗanyar Yarbawa
suna yin wannan al’ada, wanda a da can hakkin waɗannan kaya sun rataya a kan Miji ne a tasu al’adar.
iv.
Gara: Al’adar Bahaushe idan
zai aurar da ‘Yarshi yana yi mata Gara (Kayan Abinci) waɗanda suka
hada da
Shinkafa, Taliya, Makaroni, Manja, Mangida, Manshanu da makamantansu a
kai ta da su, wadda Yarbawa ba su da wannan al’ada sai dai suna da
makamanciyarta, sai dai kuma akwai
saɓani a tsakaninsu. A Bahaushiyar al’ada iyayen Mace su
ke kai gara amma a al’adar Yarbawa Namiji ne yake sayen kayan abinci ya kai gidan iyayen yarinya
tare da kuɗi da za’a rabawa danginta, wannan al’ada suna kiranta da
“ERU IDANA” amma a yanzu sakamakon auratayya tsakanin al’ummun biyu suna yin
Gara.
4.0 Sakamakon Bincike
Wannan muƙala ta kawo yadda al’adun Hausawa na Aure suka yi tasiri akan na Yarbawa
mazauna Gusau. Sauye-sauyen al’adun waɗanda suka haɗa da:
a.
Nagani Ina so: Wannan al’ada ce da Hausawa su ke yi wadda a
yanzu haka Yarbawa suna yin ta waɗanda suke zaune a garin na Gusau
b.
Lefe: Wanda a al’adar Yarbawa basu yin shi sai sanadiyyar cudanya
da Hausawa
c.
Kayan Ɗaki:
Wannan
wata al’adar Bahaushe ce wadda ita ma a yanzu Yarbawa mazauna Gusau suna yin ta.
d.
Gara: Wannan al’ada ce ta Bahaushe wadda ake yi lokacin
aure wadda a yanzu haka Yarbawa mazauna Gusau suna yin ta.
5.0
Kammalawa
Wannan maƙala ta duba
lamarin cuɗanya tsakanin Hausawa da Yarabawa. Sakamakon wannan cuɗanya ya haddasa
tasirin wasu al’adu da kuma harshen Hausa a kan na Yarabawa. Maƙalar ta gano cewa har alaƙa ta auratayya ta shiga tsakanin al’ummun biyu. An
yi bayanin al’ada da abunda ake nufi da tasiri tare da kawo ma’anar aure. An yi tsokaci akan al’ummar Yarbawa tare da
kawo takaitaccen tarihin Gusau. An kawo yadda Yarbawa suka samu kansu a garin
Gusau da mu’amular da ta shiga tsakaninsu kamar ta fannin bukukuwansu waɗanda
suka hada da Bikin aure, Haihuwa da sauransu. Muƙalar
ta bayyana al’adun da suka yi tasiri na bikin auren Hausawa akan na Yarbawa
mazauna Gusau.
Manazarta
Abraham,
R. C. (1962). Dictionary of the Hausa
Language. London: Hodder Sydney.
Adamu, (2010) “The Major Landmarks in the History of Hausaland”. The Eleventh Inaugural Lecture. Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University.
Adamu, M. (1991) Hausa Factor In West
African History, (Tasirin Hausawa a Afrika ta Yamma. Zariya: Ahmadu Bello
University Press.
Bargery, G. P. (1934). A Hausa-English Dictionary.
London: Oɗford University Press.
Burgress, and Locke, (1953). The Family, 2nd (ed): New York. American Book. Co.
Bourhis, R. Y. (1997) Language
in EthicInteraction: A Social Psychological Approach. England: Pergamon.
Bunza, A.M. (1991), “Ba Baƙo Ruwa ka sha Labari;
(Ƙimar Baƙo da Baƙunci a Al’adar Bahaushe)”
CNHN (2006), Cibiyar
Nazarin Al’adun Nijeriya Jami’ar Bayero Kano.
Funtua, da Gusau, (2010), Al’adu da Ɗabi’un Hausawa da Fulani El-Abbas Printers
and Concepts Kaduna
Gusau, R. A. (2014) Garin Gusau a Taƙaice Gusau: Al-Huda Ventures.
Gusau, S. M da Gusau B. M. (2012) Gusau
Ta Malam Sambo. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Ibrahim, M. S. (1982) “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci a
Kan Rayuwar Hausawa ta Gargajiya”. Kundin Digiri
na Biyu. Kano: Jam’iar Bayero.
Madabo, M.H (1979) Ciniki da Sana’o’i a Ƙasar
Hausa Annuri Printers and Publication D/Rimi.
Mu’azu, A. (2013) Baƙin Al’adu a Ƙagaggun Littattafan Soyayya na Hausa. Zariya: Ahmadu Bello
University Press
Rambo, R. A. (2013), “Gwagwarmayar Kamancen Neman auren
Hausawa Da Na Dakarkari”. Takardar da aka gabatar a taron ƙarawa juna Sani a
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Rauf, M. A. (1977). Islamic
View On Women and Family: New York: Cambrige Press.
Sallau, B.A. (2010) Wanzanci da
Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kaduna: Najiu
Professional Printers.
Smith, M.G. (1959) “The Hausa System of Social Status” in Africa Vol. XXVII. No. 1.
Usman A. F. (2003) “Inter-Group Relations in Gusau: A
Case Study of Yoruba and Hausa C. 1920-1996. PhD Theses, Department of History
Usmanu Ɗanfodiyo University
Sokoto.
RATAYEN HIRARRAKI
S/No |
Suna |
Shekaru |
Adireshi |
Matsayi |
Rana |
1 |
Mal. Raji |
57 |
Sabon-gari Gusau |
Mamba a ƙungiyar Yarabawan Gusau |
Alhamis 10/11/2022 Da 10:00ns |
2 |
Haruna Umar Gusau |
40 |
Sabon-gari Gusau |
Ma’aikacin Gwamnati sashen lafiya
a Gusau |
Alhamis 8/12/2022 Da 5:31ny |
3 |
Boda Radiyo |
55 |
Sabon-gari Gusau |
Mai Gyaran Radiyo |
Alhamis 15/12/2022 Da 5:00ny |
4 |
Mujiddat
Abdulrauf |
46 |
Sabon-gari Gusau |
Malama |
Lahadi 15/01/2023 Da 7:00nd |
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.