Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 36)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alqasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 36)

Baban Manar Alƙasim

Bayan dogon bayanin da muka yi don bayyana hanyoyin inganta zamantakewa a tsakanin ma'aurata guda biyu, yanzu za mu taƙaita bayanin ne a kan wasu 'yan alƙaluma:- 1) Akwai buƙatar daidaituwa ta fuskar fahimtar addini da aƙida, in ya kasance mutum mai ilimi ne, ya zamanto zabinsa na biyu bayan tantance mace mai addini shi ne samun mace mai fahimta irin ta sa, ilimi kala-kala ne, amma in aka yi dace da abin da zuciya take so, to zama yakan fi danƙo, in da za ka lura wasu masu fandararrun aƙidu sukan bar matansu su fita cikin duhun dare ba tare da wani kyakkyawan tsaro ba wai sun je taro, haka za su yanko daji a ƙasa ba dare ba rana wai suna addini, in fahimtar addinin a wannan sifar tsakanin ma'aurata ba ta yi daidai ba akwai matsala. Inda za ka fahimci abin da nake nufi, wani dare wasu sun hana ni barci wai suna maulidi, da na leƙo bayan sha biyun dare sai na ga 'yammata da matan aure duk suna tsattsaye, in ka auri mace ta matsa sai ta fita mauludi, ko wani zaman makoki na mutanen da suka rasu sama da shekara dubu daya ai ka ga akwai matsala, kamar fa ka auro 'yar sunna ne ka ce tazo ku je tattaki ko zagayen gari da sauransu, duk ba ina nufin ba zai yuwu ba ne, manufa dai ka auro wace kuke da manufa iri guda don samun sauƙin tafiyar da zamantakewa a sassauƙar hanya, kafin ka ce ma ta yi kaza ita ta riga ta gama shirya masa.

2) Samun musayar kyakkyawan zato tsakanin ma'aurata, ko na ce masoya, in ya kasance wani yana zargin wani da zina ko daduro dole a riƙa samun matsala, koda kuwa macen ce take zargin namiji da shi, bare kuma a ce maigida ne yake zargin iyalinsa da zina, a zahiri wasu mazan sukan yi ta holewa da yaran jama'a da sunan aure, har sukan nuna cewa ma addini ne, sai mutumin da ake girmama shi ya kulle ƙofa da 'yar jama'a ya ce aure ne ya yi na minti 30, ko na sa'a daya, ba kunya ba tsoron Allah, wa zai iya fassara min wannan da sunan soyayya? Shin saduwa da mace ita ce soyayya? Irin wannan da wahala daga baya ya aure ta don ya san mazinaciya ce, ba zai yarda da ita ba, da ma can sha'awarsa ce kuma ya biya, yanzu zai ce ko ya aure ta za ta ci gaba da wasu ne can daban, don a wurinsu addini ne duk da ba sa so a yi da na su, ita ma da ake yi da ita dole ta yi zargi don ta san dabi'arsa.

3) Ƙoƙarin warware matsalolin gida ta fuskar ƙaddara abin da kowa yake yi, a bayyane yake mace ko amarya ce tana da ayyuka da yawa, kamar wanki da wanke-wanke, guga da goge-goge, tsafta da tsaftacewa, ga harkar ƙundu zalla, waɗannan abubuwa ne da suka shafi soyayya, wadan da mace take yi wa namiji da zuciya daya, kamata ya yi ya maida ma ta da su wajen yaba ma ta da girman abin da ta yi, ita ma takan wuni ba ta yi aikin Naira 100 ba, amma maigida shi yake daukar nauyin komai na gidan, koda kuwa rezar yanke farce ce, da wannan uwargida za ta riƙa yi masa hanzari a wasu abubuwan, shi kuma ya kalli ayyukanta na gida ya riƙa yi ma ta uzuri don samun gamsasshiyar zamantakewa, in kuwa maigida yana kallon wahalhalun da yake yi ne kawai, ita kuwa yana ganin a sama kawai take ci to akwai matsala, haka ita ma in ta dauki lamarin a haka.

4) Wasu lokutan manema ko ma'aurata suna da wata matsala wace take yi musu wahalar magancewa, misali in masoyi ya yi kuskure a maimakon a yi tunanin yadda za a gyara cikin sauƙi don rayuwa ta ci gaba da wanzuwa kamar yadda ya kamata, sai ka ga masoyi yana ƙoƙarin ya rama abin da aka yi masa, ta wurin munana wa abokin rayuwa, sannan a ƙarshe dai yana daukarsa a matsayin masoyi, kamar ba shi ne ake fadin ba a son wani abu ya shafe shi ba, sai ka ce ba shi ne ake ce masa in ba shi ba rijiya, masoyi na gaskiya komai na sa na ka ne, to yaushe za ka ce amma fa na minti kaza ne bayan haka ba ruwana da kai, ko fada ma za mu iya yi a kan kudi?

5) Sau da yawa in masoyi ya munana waninsa rai yakan yi mugun baci, wani lokacin yakan sa mace ta yi yaji, ko takai ƙarar maigida wajen uwayensa, ko abokansa, duk dai a kan fadi tashin da take yi ne don ganin ta maido da zamantakewarta kamar yadda take a da, wasu lokutan a kan yi dace, wani lokacin kuwa shi da banza duk daya, a ganina wannan kuskure ne ba dan ƙarami ba, tabbas wasu iyayen sukan warware matsaloli cikin hikima da samar da sulhu a tsakanin ma'aurata, wasu kuwa sukan sa maigidan ne a gaba su yi masa kaca-kaca, ba na tsammanin cewa sun yi ƙoƙarin gyara ma ta gida ne kamar yadda ta nema. Da idona na ga macen da uwayenta suka zane ta, suka sa igiya suka daure ta wai ta ƙi ba mijin hadin kai, wata ma har dorina aka tanadar ma ta na zana, sabo da mijin yana kukan rashin samun hadin kanta, wannan ko za ta sallamar ta zauna da shi, da wahala a sami soyayyar da ake buƙata, domin matsa ma ta aka yi, kudi sukan sayi sha'awa kamar yadda muke gani ana yi da masu auren holewa, amma ba sa iya sayen soyayya, to ta ina dole zai kawo ƙauna? Da a ce za a bi da lallami, da ban baki, a zauna wuri guda a gamsar da duk bangarorin guda biyu na tabbata za a sami abin da ake buƙata daga duk sassan guda biyu. 6) Sai kuma wata matsala da ake sakaci da ita duk kuwa da mahimmancinta, wato nisantar motsa kishin juna, da gangan wasu matan suke yin ado naƙarshe yadda za su fisgo hankalin wasu mazan a gaban mazajensu, wata ma don wauta har hirar wani take yi ta ce yana burge ta, na ji wace ta sami matsala da maigidanta a kan wani dan wasan Hausa, wata kuma kan wani malami mai wa'azi, wanda kullum ba ta da wata magana sai ta sa, wata don wauta ma hirar tsohon mijinta take yi, to ba ita ba wasu mazan ma sukan kama hira da wasu matan a kan waya ko a sarari sabo da gadarar cewa su ne masu gida, akwai ma masu shigo da 'yammatansu cikin gidansu, waɗannan duk wasu shimfidu ne na hana zaman lafiya a tsakanin masoya ko ma'aurata. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba. 

Post a Comment

0 Comments