Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 37)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alqasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 37)

Baban Manar Alƙasim

Darasin yau yana daya daga cikin mahimman darussa na wannan shirin, domin magana ce a kan matsalolin da suke faruwa a tsakanin ma'aurata, wato sabbin shiga, komai wayewar mace da namiji, ko ta yi ta sayar da kanta a matsayin 'yar auren holewa in dai ba ta zauna da namiji a matsayin matarsa bisa shari'a ba to baƙuwa ce, matar da ta yi rayuwa da namiji koda shekara daya tal ta yi da shi, tana da abubuwan da za ta fadi wadan da tsohuwar 'yar daduro ba ta sani, haka namijin da bai taba aure ba koda kuwa ya yi ta tamfatsewarsa da mata in dai bai taba aure ba to akwai abubuwa da yawa wadan da sai an yi masa bayani. Babban dalilan da suke haifar da matsaloli a tsakanin wasu ma'auratan a shekarar farko suna da alaƙa ne da rashin sabawa da zamantakewar aure, dukansu biyu sun yi ta bata wa juna ne lokaci a rayuwar da ba ta haƙiƙa ba, namiji ya riƙa jin cewa shi ne komai na ta, in 'yar ajiyar zuciya ta yi sai ya fara ƙoƙarin sanin dalili, duk abin da take so nan da nan za a yi ma ta, in kudi ta nuna tana buƙata ko dai a ba ta nan take, ko kuma a aiko ma ta, ita kuma za ta iya yarda cewa tabbas zai iya yin komai, don a fahimtarta ƙauna takan sa masoyi ya yi abin da bai taba tsammanin zai yi ba, kuma ita masoyiyarsa ce, yana ƙaunarta sama da kowa. Shi ma din samma-kal, domin takan nuna masa iya abin da za ta iya fitarwa na ƙauna, takan fito masa a matsayin wace take daidai da ta sayar da ranta a dalilinsa, shi ya sa ma takan ce masa "In ba kai ba rijiya" wato ƙauna ta kai ma ta inda take ganin rayuwa ba ta da amfani matuƙar ba da shi ne ba, buƙatarta kawai ta gan ta tare da shi, suna musayar doke-doke da 'yan dararraku, ba ta da wata magana sai ta sa, kamar yadda ba ta son ganin fuskar kowa sai ta sa, ko baƙanta ma ta rai ya yi in ya yi murmushi shi kenan an gama, ta sauko kenan. To yanzu rayuwa ce za a yi ta haƙiƙa, ba wata maganar sha'awar kaza, in fuska ake son gani yanzu ga ta ba hoda ba tozali, in kwalliya ce to sun ma ga junansu suna warin zufa ba ƙamshin turare ba, satar kallo ko wayon taban wani wuri bai ma taso ba tun da duk sun biya wa juna buƙata ba daya ba ba biyu ba, yanzu abin da ya rage shi ne fuskantar zahiri a haƙiƙaninsa, ita mace tana buƙatar wannan kulawar da ta jima tana gani, in kuma bai samu ba to haƙiƙa wani canji ne na daban wanda ba ta san sa ba ya kurdado.

Haka shi ma namiji yana son ya ci gaba da ganin wannan tarairayar da yauƙi gami da takwarkwasa kamar yadda ya saba tun tale-tale, sai dai kash! Ba abin da ya dace kenan ba, ya kamata in kida ya canja rawa ma ta canja, misali; mace a gidan uwayenta (wasu) da safe sai an gama komai za a tashe ta ta yi sallah ta yi shirin makaranta, amma yanzu sai dai ta tashi ta shirya wa maigida abinci, ba ta da zama har sai ya fita, don ita ma tana da buƙatar karyawar kamarsa, kenan aikin abinci da sanyin safiya ya kama ta, wanda a lokacin da take ganin tana soyayya ne ba shi a kanta. Tana gama abincin safiya sai kuma zancen wanke-wanke, ga gyaran daki, da tsaftace wuraren biyan buƙata kamar kicin da ban daki, sai kuma sharar gida da shirya gado da daki, bayan 'yan uwanta da baƙi da za ta yi, wannan duk za ta yi ne bayan wanka da kwalliya, wadan da a da su kadai ta sani, tana kammalawa sai zancen abincin rana, idan ma har ta iya kammalawar kenan, tana sa rai ta yi aikin wahala, ta gaji tibis, sabo da hidimar gida yanzu tana jirar maigida ya zo ya rarrashe ta, cikin sanyin murya da magana mai dadi a yi wannan a yi wancan, wanda a fassararta su ne soyayyar, in ba ta samu ba kuma canji ne yanzu sai haƙuri.

Shi kuwa ya saba a dafa a ba shi, ba abin da ya san kudinsa, yanzu komai shi ne, duk wani abu na gida da bai saba sanin yadda ake yi ba yanzu shi ne ma zai dauki nauyin kammala shi, garin neman abin rufin asiri sai ka ga ya dawo gida a jigace, yana sa rai da cewa yanzu matarsa za ta tarairaye shi kamar yadda ta saba, to a da lokacin tana gidansu ta riƙa yi masa a matsayinta na budurwarsa bare yanzu da komai na ta yake wuyarsa? Shi bai san wace wahala ta sha a gida ba, in bai sami yadda yake so ba sai ya yi tunanin an sami canji ne, ba tare da kallon cewa ita ma tana buƙatar abin da shi ma yake buƙata a wurinta ba. In ba a kai hankali nesa ba sai ka ga da yin aure ba a dade ba har an fara dauki ba dadi a tsakanin ma'aurata, balle ma ba wanda ya gama sanin halin dan uwansa, kuma ga rayuwarsa a hannunsa, shi namiji yana ganin shi ne babba, matarsa dole ta sunkuya masa a matsayin matar aure, ita kuma ta saba da rayuwar gida, ba wani mai matsa ma ta, yanzu farar daya ta zama kamar wata mai aiki, tana buƙatar wani lokaci kafin ta saba da dan sabon canjin da ya shugo rayuwarta, irin wannan karatu na auren sabon shiga abu ne da ya dace kowanne cikin amarya da ango su sani tun yanzu, don su riƙa yi wa juna hanzari, wani abin yakan faru amma ba bisa ganganci aka yi ba. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

 

Post a Comment

0 Comments