Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alqasim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 35)
Baban Manar Alƙasim
6) Duk wata gamayyar
zamantakewa da ka sani in har ya kasance babu girmama juna to ba ta da amfani,
ban ƙi kowa ya auri kinin da ya ga dama ba, don a rayuwa mutum zai iya
mulki da kansa ne kawai, shi ma din wani lokaci kudi da lafiya suna iya yi masa
barazana ko su kawo masa matsala a rayuwa, amma wanda duk ya sayi rariya, haƙiƙa ya san za ta zubar da ruwa,
haƙiƙa Allah ya fifita maza a kan mata, ciki har da ciyarwar da namiji
yake yi wa mace, idan ya kasance mace ce za ta ciyar da namiji to ko ya so ko
ya ƙi, sai ya rasa wani ɓangare na matsayinsa na maigida, ko
dai ita macen ta yi aiki da ƙarfin kudin da take badawa, ko
shi ya ji tsoron kar ta dauka masa mataki sai ya bar ma ta gidan.
Akwai abubuwan da ba zai yuwu a
buga misali da su ba ko kadan, mun dai yi zancen ƙwarya ta bi ƙwarya a matsayin uwaye, ban ce
dole ba ne amma na fadi ra'ayina, sai dai in za mu duba rayuwar Annabi SAW da
Khadija RA za mu fahimci cewa; ba wai shekarun ne kadai ta fi Annabi SAW ba
(Kamar dai yadda ya shahara a tarihi), shi dan gidanta ne da ya yi kasuwanci a
cikin dukiyarta, ta yi masa kyakkyawar biya, inda ta aure shi, ta kuma haifa masa
'ya'yan da muke kira daya daga cikin ahlul baiti a yau, zancen ilimi kuwa an ce
ta riƙa karanta Attaura, shi kuwa Annabi SAW a sa'in bai iya rubutu da
karatu ba, Ƙur'ani ba a wuri daya ya tabbatar da haka ba. A tsawon wadancan
abubuwa guda uku da muka tattauna, kowanne mace ta fi ka matsala ne, ba dole ba
ne ka sami girmamawar da kake buƙata, shi ya sa wasu matan ma da
wahala su auri wanda suka girme shi, masamman mace mai ilimi, zan iya tunawa da
maganar da wata abokiyar karatuna ta yi, wato Dr Furere Bagel, a wata hira da
muka yi bayan mun fito aji, take cewa ko ba ta da miji ba za ta auri wanda ta
girme shi ba, wato sa'an ƙanninta kenan, ka san dan
jarida da son jin maganar da ta saba fahimtarsa ko ta saba ta sauran jama'a. Da
na matsa ma ta da tambaya sai ta nuna tana son kowani lokaci ta riƙa jin cewa ita yarinya ce a
gaban maigidanta, wato shi ne tsoho, a nan ta yi aiki da ilimi ne, ita ba
lokacin take kallo ba, nesa take hange, masamman sanin halin maza a yau, sau da
yawa za su fito maka da cewa suna bala'in ƙaunarka amma a zahirin gaskiya
sha'awa ce tsagwaronta, Dr da yake malamar jami'a ce ta ƙi yarda ta lumshe idanunta gaba
daya, daya na barci daya ta bar shi a bude sabo da tsaro, ba iyakar tambayoyin
da na yi ma ta kenan ba, na kuma nemi sanin dalilin da ya sa mata ba sa son
kishiya.
A nan Dr ba ta yi wata doguwar
magana ba, sai ta ce; a shekarunta da ta sani ba zai yuwu ta auri maras mata ba
(Wai idan ma ba ta da aure kenan), don ba za ta auri wanda ta girme shi ba,
kenan zai yi wahala a sami wanda ya girme ta kuma bai da mata, in ma an samu
dole a binciki dalili, ka ji magana a bakin masu ilimi masamman malaman
jami'o'i, da wannan za mu ga irin sayar da ran da Khadija RA ta yi wajen auren
Annabi SAW, da irin tabbacin da take da shi (Wanda babu a yau) na cewa zai riƙe ta da mutunci da amana,
maganar ilimi kuma ba ta zama wata matsala ba a tsakaninsu, har ta koma ga
Allah ba a taba jin ta da Annabi SAW ba, sai dai a ji shi da wata a kanta. Mace
dole ne ta nemi girmamawar namiji ta kowace hanya, ba tare da ya sanya ido a
kan tsufarta, talaucinta ko rashin babban dangi ba, maza a yau, kamar yadda Dr
Furera ta nuna, in mace ta fara girma suna iya barinta su koma wajen wata,
kenan kallon shekara kafin a yi maganar aure ma yana da kyau, don a rayuwarmu
ta yau, in dai ka ji wani yana son ya auri wace ta girme shi, ka dan yi hira da
shi, da wahala ka taras soyayyar ce a zuciyarsa ba sha'awa ba, sai dai kuma ni
ba ina ba da shawara ne kar a auri babbar mace ba, amma namiji ya kalli
shekarunsa ya gwama da na matar. Zancen "Taya ni takaba" ma ba abu ne
da mutum zai iya watsi da shi ba, maza (ba duka ba) suna da bala'in son kansu,
sai ka ga baba dan Hamsin da doriya ya auri yarinya 'yar shekaru 15 - 18,
tambaya a nan, wai shin haramun ne? Amsar ita ce ban taba gani ba, a maimakon
haka ma Annabi SAW ya auri A'ishah RA tana 'yar ƙarama matuƙa, ƙasa da shekara goma sha biyar
din, kenan in koyi da sunnan ma'aiki za a yi, babu laifi a ce mutum ya auro
budurwa a cikin matansa ko da ƙwara daya ce.
Kawai dai za mu dan sake dubawa ne, Annabi SAW makaranta ne, shi ya sa ya auro wace ta isa haihuwarsa da wace ya isa haihuwarta, ya zauna da mata daya kal har ta rasu ya kuma zauna da 9 lokaci guda, bisa wannan za mu ga Bukhari ya fitar da hadisan da suka nuna cewa Annabi SAW ya riƙa zaga matansa gaba dayansu da wanka guda, har aka nuna cewa Annabawa SA suna da ƙarfin da daidakun mutane ba su da shi, kenan har da tsufar da Annabi SAW ya yi a lokacin, yana da ƙarfin da matashin yanzu bai da shi a shimfida. To in dai mutum in ya ƙara tsufa ƙarfinsa a shimfida yana raguwa, ba zai yuwu kenan tsoho ya auro yarinya danya shataf ba, kuma ya iya biya ma ta bukatunta, in ma ya ce shi yanzu yake jin ƙarfi yana buƙatar sabon jini, a ganina gwara ya auro bazawar da ta gama nuna, jiran mai tsinka kawai take yi, matuƙar ba 'yan dabarbaru za a yi ba, kamar dai yadda kare ya fadi da aka kore shi daga gindin kanya, fitacciyar magana dai tsohuwa tana iya auren yaro, haka tsoho yana iya auren yarinya in dukansu sun daidaita, sai dai kuma don samun tsayuwar aure a ginshiƙi mai kyau, kuma ba cuta ba cutarwa, yana da kyau kowa ya duba dacewa a shekaru. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.