Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 04)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  04)

Baban Manar Alƙasim

Akwai wasu dalilai wadan da suke tunkudo matashi zuwa ga soyayya, sai dai wasu ba su cika kula da su ba, bari dai mu yi ƙoƙarin lissafa su kamar haka:-

a) Ƙarancin tausasa wa matashi a tsakanin uwaye yana ba da gagarumar gudummuwa wajen karkatatar da shi zuwa ga inda yake zaton zai dan sami tausasawa, idan ya kasance ba wani mai sakewa da shi, sai ya sami wanda zai zauna da shi na tsawon lokaci, ya nuna masa cewa yana ma son ya kasance tare da shi kowani lokaci, dole ya karkata inda hankalinsa zai kwanta, masamman yadda halittar namiji take buƙatar ta mace, ita ma ta macen take buƙatar ta namiji, in suka hadu sai soyayyar ta taƙaitu wajen biyan abin da aka rasa a baya, a maimakon saƙa rayuwar da za ta dore har abada.

b) Karkata ta dabi'a wajen wani jinsi na daban sakamakon canjin da aka samu na physiology ga matasa, matasanta a kowani lokaci ba ta kama da yaranta, to ko yara ne akan sami irin wannan shaƙuwar ta buƙatar wani jinsi, a dazu na ji wani uba yana cewa: Uwar dansa ta roƙe shi minti guda daya ya hana ta, amma ya dauki jakar kacokan ya miƙa wa wata yarinya, matashi shi ya fi buƙatar wani jinsi don sanyaya wa rayuwarsa.

c) Gasa a tsakanin matasa takan kawo kusantar jinsuna, sau da yawa wani lokaci matasa in sun ga wata mace sukan taya wa junansu wanda zai iya magana da ita, akan lura da aji, ko hasken fata, ko matsayi da dai sauransu, saurayi bai son a ce duk tsararrakinsa suna da 'yammata sai shi kadai, in ma shi bai nema ba abokansa za su matsa masa, a irin wannan yanayi bai shirya kusantar wani jinsi ba amma rayuwa ta tilasta shi.

d) Tasirantuwa da littafan soyayya, fima-fimai na soyayyan da na batsa sukan sanya matashi ya buƙaci wani jinsi wanda ba na sa ba, galibin abubuwan da suke nunawa da wahala su faru a irin wannan surar, yadda masoyi zai watsar da komai na rayuwarsa a kan wanda yake ƙauna, har ya zama kamar bai da wani abin yi sama da buƙatuwarsa da masoyinsa, sai matashi ya fara tsammanin cewa shi ma in ya yi masoyi haka za ta wakana, sai ya yi ƙoƙarin jarrabawa, zai kuma buƙaci soyayyar ta yi daidai da wace yake karantawa ko yake gani, duk kuwa da cewar ko su masu fima-fiman sukan sami matsala a rayuwar aurensu.

e) Wani lokacin kuma matashi yakan yi zaton cewa yanzu fa ya girma, bai kamata a ce babba kamarsa bai da budurwa ba, ko ita macen ta riƙa jin cewa ita ma fa ta girma, soyayya kuma ita take tantance girma da yaranta, masamman wannan zamani na waya, da za ka ji ana magana ana dararraku, wani lokaci a yi ta danne-danne ga waya, ana hira da budurwa ko saurayi, za ka riski cewa wace ta girma ba matayi takan yi ta kuka cikin dare, gami da salloli da roƙon Allah, ƙaramar da ba saurayi kuma a kira ta bera! . Soyayyar ƙuruciya tana da tasirori da dama, da kuma abubuwan da suke alamta tunkudarta ga matashi, misali:- a) Yawon da tunani yake yi wa matashi, galibi kwalliyar masoyi yake tasowa a duk lokacin da matashi yake kadaita, kamar ni dai lallen da mace take yi yana saye imani na, wani kuwa sam bai ƙaunarsa, yana da abin da yake ba shi sha'awa, kuma zai riƙa satar kallonsa a jikinta, duk in ya kadaita sai ya riƙa dawo da shi yana tunaninsa, ita ma budurwar da abin da take kallo, tun ma ba ita ba, don tana iya bata komai a dalilin wannan tunanin, wata ƙila ma ta rame kamar mai rashin lahiya.

b) Mafi yawan abin da yake tsakanin matasan buƙatuwar juna ce, kowa yana fatar a ce ga ranar da jikin masoyinsa zai halasta masa, don ya jima yana kallon gabobin da suke motsa sha'awarsa, in da za su zauna yau na tsawon lokaci, ba zai hana su buƙaci zama nan gaba ba, don ba zaman da buƙatarsu take biya, kuma ba za su iya haƙura da juna ba har sai buƙata ta biya, irinsa ne in ya zo da tsautsayi sai ka ga ciki ya bulla wajen wace ba a taba zato ba, to soyayyar ƙuruciya ta yi tasiri.

c) Sannu a hankali wannan soyayyar takan tashi daga mafarke-mafarke zuwa buƙatar kadaituwa da tunani, ta inda za ka ga matashi ya lumshe idanu kamar yana barci, amma a farke yake, tsabar tunanin masoyi ce kawai ta mamaye zuciyar, wani lokaci ma sai ka kira shi sau biyu kafin ya san cewa da shi kake magana, da za a hana shi auren masoyin shi kenan wani tashin hankali na masamman ya taso, ko mai karatu ne babu sauran zancen imani da ƙaddara bare a sa rai zai yi haƙuri ya ci gaba da girmama na gaba, matsalar tasirin soyayyar ƙuruciya kenan da ta tattara a kan sha'awa. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  04)

Post a Comment

0 Comments