Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 05)
Baban Manar Alƙasim
Akwai kuma batacciyar soyayya, ita ce soyayya maras
tabbas, abin da aka sani kishiyyar soyayya ƙiyayya ce,
soyayya takan sanya jin dadi ne da farin ciki da sakewa, ƙiyayya kuma ta sanya
damuwa da lalacewa, shi ya sa in mutum ya ji wani aljani ya ce yana son wane ko
wance yake shakkar haka, domin wanda ake ƙaunar kullum
cikin wahala za ka isko shi, a maimakon sakewa da walwala da walawa. Wannan
batacciyar soyayyar tana da alamomi ne a wargaje, sai dài kowacce alama tana da
masabbabinta, amma a ƙarshe sukan ba da sakamako guda daya:-
a) Alokacin da aka sami soyayyar da sha'awar saduwa
ce gaba, babu ko shakka ba ta iya haihuwar 'ya mai ido, shi ya sa addini ya
gindaya wasu shingogi don tsarkake rai, dukiya da mutunci, yanzu dai duba auren
holewa (Mutu'a), in za ka auri mace na tsawon sa'a guda kuma ka bakka ta
sadaki, amma da zarar sa'ar ta gama cika shikenan kudinka ya ƙare, ka ga a
nan ba a tsare maka dukiyarka yadda za ka amfana da ita na tsawon lokaci ba,
addini ba zai yi umurni da asara ba, shi ya sa ma nan da nan ya hana caca don
tsare dukiyar jama'a.
In kuwa maganar soyayya za a yi, da wahala duk wani
mai hankali ya yarda da cewa akwai wata soyayya ta gaskiya da za a iya yin ta
na 'yan mintuna ko sa'o'i ko kwanukka da watanni, soyayyar gaskiya akan yi ta
ne na dindindin, in wani dalili ya shigo to ba da gangan aka sanya ba, to a
lokacin da namiji zai sadu mace ya rabu da ita na tsawon minti 15 da zarar
kudinsa ya ƙare, shin a kan kudin ake soyayyar ko a kan
kwanakin da yi alƙawari?
A nan babu wani zancen soyayya, macen kudin kawai
take nema kuma ta samu, in zai ci gaba da irin wannan soyayyar to lallai sai ya
ƙaro kudi, shi
kuma jikinta kawai yake nema, in ya gama amfani da ita shi kenan, ita da banza
kuma duk daya, ta zama tamkar karuwa, cinta da shanta duk na ta ne bare a yi
zancen sutura ko tausayi da soyayya. Wannan soyayyar tabbas batacciya ce, don
mai yin ta ba ya buƙatar ƙaruwa da ita,
ita macen ba ta fatar samun ciki, don ta san dan ba zai bi uban ba, shi uban da
aka ce dansa ne yana shakku, don mazinaciya ba ta kwanciya da mutum guda,
tambayar a nan: Shin da gaske ne wannan dan na sa ne, ko na wani ne? Cinsa da
shansa a wuyar wa suke? In da soyayyar gaskiya ake yi murna ake yi in ciki ya
shiga ta kowani banagare, ita da mijin, 'yan uwanta da na sa, wannan soyayya ta
holewa ba ko shakka mai cutarwa ce, addini ya fadi ƙarara babu cuta
ba cutarwa.
b) Soyayya ta zamto ba ta da manufa, saurayi yana
soyayya ne amma shi kansa bai san dalilin da yake yi ba, galibin irin wannan
soyayyar ta fi yawa a makarantu da jami'o'i, inda dan talaka zai fada soyayya
da 'yar mai kudin da tabbas ya san ba zai aure ta ba, ko shi ke da kudin
gidansu ba za su yarda ya wuro mace kamarta ba, sau da yawa samari kan ƙulla irin
wannan soyayyar, wani lokaci ko karatu ba sa iyawa, har ma a fadi jarabawa ko a
sami ƙaramin sakamako duk a banza, tunda in suka gama
karatu ba wanda zai sake ganin wani, amma fa in ya zo da tsautsayi ko ba a sami
ciki ba an dai bata juna, addini kuwa ba ya umurni da alfahasha.
c) Samun rudu wurin soyayya, wannan kuwa takan
kasance ne inda wata budurwa take mugun son wani saurayi, shi kuma sai ya riƙa biye ma ta ba
tare da zuciyarsa tana wurinta ba, akan dade ana yi amma babu wani abin sha'awa
na a zo a gani, ko ya kasance ita yake ƙaunar ya ga ya
mallaka amma zuciyarta ba ta tare da shi, tana lallaba shi ne kawai don kar a
ce ta wulaƙanta shi, sau da yawa saurayin yakan ji labarin ta
yi aure ne kawai, ina da abokai guda biyu, daya ya je zance ne aka ce masa ta
yi aure da mako biyu, dayan kuwa ce masa ta yi ka zo ranar kaza, da ya zo sai
isko ana daura aurenta da wani, su biyu dukansu sun nuna soyayya ta gani ta
fadi ga samarin amma ga yadda ta ƙarasa.
d) Ya kasance ana nuna soyayya ta ƙarshe amma bisa
wata fa'ida da ake samu, wasu lukutan irin wannan soyayyar ta fi faruwa a
karkara, koda yake takan faru a marayan ma, yarinya ce guda amma tana da samari
kusan biyar, ina ƙarami ma na ga yarinyar da ta ajiye lefen mutum 6,
kuma saurayi daya tal za ta aura, abin da ya sa ta haƙura da su don
'yan kurdin da suke bakka ta, su ma samarin a kan sami mai 'yammata da yawa,
yau yana nan gobe yana can, abin da yake so kawai ya riƙa jin dadin
muryarsu ko ya yi alfaharin yana da 'yammata kaza.
e) Sai kuma lokacin da samari da 'yammata za su
sami kansu tsundum cikin yanayin da kowa yake hanƙoron biya wa
wanda yake raya cewa masoyinsa ne buƙata ba tare da
an daura aure ba, galibin irin wannan auren ko an yi bai cika yin albarka ba,
don an gama tamfatsewa kamin aure, duk sun san kawunansu cewa ba kamammu ba ne,
irin wannan sau da yawa mijin yakan riƙa shakkun alaƙarta da kowani
namiji, ita ma duk lokacin da ya fara alaƙa da wata ta riƙa zarginsa
kenan, an ƙulla soyayyar kan barna da sabon Allah. A nan zan
dakata. Sai mun haɗu a rubutu na
gaba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.