Hasashen Asalin Ranar Hausa ta Duniya

    Ranar Hausa ta Duniya ta samu asali ne daga wani gyara da aka yi a shekarar 1901.

    Abubakar Sarki ASUK
    07039311880

    International Hausa Day

    Ranar Hausa ta duniya,  rana ce da aka keɓance domin nuna muhimmancin harshen Hausa , da tattauna hanyoyin bunƙasa shi da kuma jawo hankali a kan irin ƙalubalen da harshen yake fuskanta.

    An fara bikin farko a shafukan sada zumunta musamman  a shafin Twitter.

    An zaɓi ranar 26 ga watan Augusta domin tuna ranar da aka ƙirƙiro haruffan "ƙ" da "ɗ" da

    "ɓ" wanda babu su a haruffan Turanci.

    Najeriya, kuma a irin wanan rana hausawa na duniya na cika shafukan zumunta  da zantuttuka masu nuna alfahari da Harshensu, wasu wajajen sukan shirya bukukuwa a wanan rana.

    Ranar Hausa dai ta samo asali ne a shekarar 2015 bayan ɗan jarida Abdulbaƙi Aliyu Jari da wasu abokansa na shafukan sada zumunta suka ayyana ranar a matsayin ranar da masu magana da Harshen Hausa za su haɗu su tattauna cigaba da ƙalubalen da harshen ke fuskanta a karni na 21.

    Muhimmancin Ranar Hausa

     

    An ƙirƙiri ranar ne domin ciyar da harshen hausa gaba, adabinsa, al'adunsa da kuma, samun haɗin kan hausawa a duniya baki ɗaya.

    Abdulƙadir Labaran Koguna (Sarkin Hausawa Hausan Duniya) Yana ɗaya daga cikin mutanen da suka ƙarfafa wannan biki a duk duniya gaɓa ɗaya.

    In da ƙungiyarsa ta Al'umar Hausawa Duniya tane gabatar da wannan taron a duk duniya a irin wannan rana. Kamar Chinq, France, England, Niger Chard da sauran ƙasashen duniya.

    Tarihi ya nuna cewar a da Turawa suna rubuta Hausa ne gwargwadon sautin da suka ji a kunnensu. Daga baya suka dinga yi wa harshen gyare-gyare har aka tabbatar masa da matsaya ƙwaya ɗaya.

    Tarihi ba zai manta da shekarar 1773  in dawani Baturen ƙasar Denmark mai suna Nibuhr wanda ana kyautata zaton cewa shi ne ya fara rubuta Hausa cikin rubutun boko a ƙasar Danmark.

    Ya rubuta wasu kalmomi gwargwadon yadda ya ji su daga wani bawa ɗan ƙasar Barno da wani Balaraben Tunis suka kaiwa sarkin Denmark Ziyara.

    Nibuhr ya rubuta kalmomi bayan da ya nemi wannan bawa ya koya masa Hausa. Kalmomin su ne:

    Crua...........Ruwa

    Dolma........Dalma

    Sinkaffer......shinkafa

    Bavia............Baiwa

    Coroma........ƙorama da dai sauransu.

    Bayan nan Turawa sun ci gaba da rubuta kalmomin Hausa gwargwadon yadda suka ji sautinsu.

    A rana mai kamar ta yau wato 26,08,1909 Wani bature mai suna Hans Vischer (Ɗan Hausa) ya yi wa wasu harufan Hausa da babu su a cikin abajadan boko lankwasa, kamar:

    B............ Ɓ ɓ

    K............ Ƙ ƙ

    D............Ɗ ɗ

    A don haka hukuma ta yarda a yi amfani da su maimkon wasu ɗige-ɗige da ake yi.

    Harshena abin tunƙahona......

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.