Gudummuwa da Jaruntakar da Dangaladiman Gobir Malam Alu Dan Sarkin Gobir Yakuba, Kuma Natsinin Kabi Na Farko Ya Tabbatar A Kasar Kabi

    Gudummuwa da Jaruntakar da Dangaladiman Gobir Malam Alu Dan Sarkin Gobir Yakuba, Kuma Natsinin Kabi Na Farko Ya Tabbatar A Kasar Kabi

    Sardauna Muhammad Lawal Argungu
    Wakilin Daular Gobir
    Shugaban Kungiyar Gobirawan Nijeria
    Reshen Jihar Kebbi 

    1.  Asali da Salsalar Dangaladiman Gobir Malam Alu Dan Sarkin Gobir Yakuba

    Shi dai Dangaladiman Gobir Malam Alu ɗan Sarkin Gobir Yakuba ne, watau jika ga Sarki Gobir Ibrahim Babari, wanda ya kafa babban Birnin ƙasar Hausa, watau Birnin Alkalawa. Kuma shi ne ƙane ga Sarkin Gobir Ali ɗan Yakuba na Gawon Gazau, wanda ya yi sarauta a shekara 1817-1835. Sauran yanuwansa sun haɗa da: Salihu Mai Kadaye da Mummuni da Bunu ɗan Gazumi da Masari Maikai.

    Bayan zumansa ÆŠan Sarki, ÆŠanGaladiman Gobir Malam Alu, kuma Malami ne, domin ya rubuta Alqur’ani mai girma hizo sittin, Æ™ira’ar Warsh da hannunsa. Haka kuma, ÆŠangaladiman Gobir Malam Alu shi ne Natsinin Kabi na farko, tun lokacin Sarkin Kabi Yakuba Nabame, ya yi sarauta daga shekaera 1860-1901.

    2.      Dalilin Tasowarsa Daga Gobir Zuwa Kabi

    A hakikani Gaskiya wannan tarihi baya kammala batareda anyi bayani kan watsewar birnin  Kabi wato babban birni na Kabawa bayan tshohon Birnin su na surami.

    Watsewar Kabawa daga Birnin Kabbi, inda suka waste gida ukku: wasu suka yi Dandi, wasu Kebbe, wasu kuma Argungu, amma shi Sarkin Kabbi Yakubu Nabame da Mahaifinsa Samaila Ƙarari, su suka zo Argungu. Amma shi Fulani sun tafi da shi Sakkwato. Zaman Yakubu Nabame a Sakkwato, sai ya zama kamar Sarkin YaÆ™in a gare su, saboda ya san hanyoyin yaÆ™i. Wata rana, Fulllani suka É—aura yaki zuwa Æ™asar Gobir, a lokacin Sarkin Gobir Ali É—an Yakubu a wurin wannan yaÆ™i ne, Gobirawa suka fahimci akwai wanda ke jifar mashi, wanda ba Bafillatani ba ne. Saboda haka, jarumawan mayaÆ™an Sarkin Gobir, wadanda aka sani da suna ’Yankwana. Sai É—aya daga cikinsu ya yi kukan kura, ya nufi Yakubu Nabame. Koda ya isa wurinsa, sai ya ganshi ashe ba Bafillatani ba ne, da kuma tsagensa na Kabawa, sai suka zo da shi wurin Sarkin Gobir, a inda Sarkin Gobir Ali É—an Yakuba, ya tambaye shi sunanansa. Sai Yakubu Nabame ya ba shi amsa da cewa sunana Yakuba. Shi kuma Sarkin Gobir Ali É—an Yakuba, ai mai sunan baba ka yi É“arna, domin mu nan da kake gani darnin gidanmu muke kariya, idan ka yi zucciya ka je ka tayar da Kabi. Haka kuma, a duk lokacin da ka shirya, a shirye muke mu taimaka maka.

     Tun lokacin da Gobirawa suka yi wa Yakubu Nabame habaici, tun daga wannan ranar bai sake fita zuwa yaÆ™i ba, sai tunanin komawa gida, watau Æ™asar Kabi.

    A lokacin da Yakuba Nabame ya dawo gida, wato Argungu, sai ya tarar da yanwansa, Lailabawa, kuma su ke mulki a lokacin. Haka kuma, suna ƙarƙashin mulkin Fulanin Gwandu, domin a duk shekara a Gwandu suke biyan haraji, kuma Kabawa suna kai musu haki na bayabaya.

    Saboda haka, A shekarar da Yakubu Nabame ya dawo gida, sai Fulani suka aiko da cewa, Kabawa su biya haraji. Shi kuma ya aika musa da cewa, a gaya musu Nabame ya dawo. Don haka biyan haraji, da kai haki na bay-baya ya ƙare. (A nan ne cikin waƙar Marigayi Aliyu Ɗandawo Shuni yake cewa, bayan shekara dubu biyu, sannan Nabame ya bayyana, ya fanshi Kabawa, ya gagari Fulani, da ruwan kebo da masu, kun sun yi kulli kulinsu, ina ruwan sadauki, ya dai buwaye ku, bindiga ai ba ta ƙara tashi). Ana cikin wannan hali ne sai Sarkin Kabi ya aika wa Maigirma Sarkin Gobir cewa, yana yi masa tuni, kuma ya dawo gida.

    Saboda haka, sai Sarkin Gobir ya turo Æ™aninsa Dangaladiman Gobir Malam Alu da ya zo Kabi, domin taimakawa Kabawa, kamar yadda suka yi mass alkwali. Don haka, Dangaladiman Gobir Malam Alu Dan Yakuba, ya bar Æ™asar Gobir da dawakai É—ari (100) tare da ’yan Æ™asa mutun É—ari biyu da tamanin (280). A lokacin da ya bar Gobir zuwa Kabi, Dangaladiman Gobir Malam Alu ya yi sansani a wani wuri da aka sa wa suna Gobirawa a Æ™asar Augie. Bayan ya taso zuwa garin Natsini, saboda Æ™ura ta yawan dawaki, sai mutanen Sarkin Kabi, suka sheda masa cewa, suna ganin alamun an kawo  masu yaÆ™i. Sai Sarkin Kabi ya amsa da cewa,  ba yaÆ™i ba ne. Yana sane da zuwansu. A lokacin da Dangaladiman Gobir Malam Alu ya iso garin Natsini, sai ya aika wa Sarkin Kabi Yakubu Nabame cewa ya yi baÆ™o. Don haka, Sarkin Kabi ya je wannan gari na Natsini, inda suka sadu da Dangaladiman Gobir da ayarinsa. Bayan da Sarkin Kabi Yakubu Nabame ya sadu da Dangaladiman Gobir Malam Alu da jama’arsa, sa’annan ya yi masa bayani irin matsalar da yake fuskanta da Fulani. Saboda haka, ya nemi a shiga yaÆ™i gadan-gadan. Sai Gobirawa suka ce, ka san cewar sun yi tafiya mai nesa, saboda haka a bari su huta. Sarkin Kabi Yakubu Nabame ya amince da wannan shawara, bai san da cewa Gobirawa sun yi wannan, domin su nuna mass suna da dabarun yaÆ™i daban-daban. Saboda haka, Gobirawa sai da suka bari dare ya yi, suka É—aura yaÆ™i, suka je wuraren Fulani suka sa masu wuta. Haka kuma, duk Bafullatanin da ya futo sai su kashe shi. Koda safiya ta yi, Gobirawa sun gama da Fulani.

    Da gari ya waye, Sarkin Kabi da rundunarsa da dawaki ashirin (20), suka zo domin a haɗa da dawakan Gobirawa ɗari (100) domin shirin yaƙi. Sai Magaji Mai doron yaƙi, kuma shugaban mayakan Dangaladiman Gobir Malam Alu, ya shaida masu cewa, ai tun cikin dare suka gama da Fulani. Saboda haka, sai Sarkin Kabi Yakubu Nabame ya naɗa Dangaladiman Gobir Malam Alu ɗan Sarkin Gobir Yakuba, a matsayin Natsini, kuma shi ne wanda ya daɗe da wannan sarauta, domin ya shekara arbain da ɗaya (41) yana sarauta, daga shekara 1860-1901.

    Ga kirarin da ake yi wa wannan basarake

    Gabjiya Magajin Adam,

    Jagaban Sarakai.

    Dangaladiman Gobir Malam Alu, kuma Natsinin Kabi, shi ne ke jagorar sarakuna da zarumawa a wurin yaƙi, tare da taimakon sarkin yankinsa watau Magaji Mai doron yaƙi.

    Haka kuma, Gobirawa sun taimaka wa Kabawa a lokacin yaÆ™in da ya faru tsakanin Kabawa da Fulanin Sakkwato. Dangaladiman Gobir Malam Alu tare,da taimakon almajiransa, watau Magajin Baberi da Magajin Kulodo, su ne suka taimaka aka ba Sarkin Kabi Saman Yakubu laya mai suna Gogarna babbar laya’, wadda aka umurce shi da ya cije ta, kuma ya hau dokinsa tana cije ga bakinsa. A lokacin ne aka gan shi bisa toran giwa É—auke da jariri a baki. A lokacin ne Sarkin Musulmi Abdulrahman, shi da mutunensa suka gudu, suka bar tamburransu, su ne Kabawa suka É—auka a matsayin ganimar yaÆ™i.

    Bayan rasuwarsa, Dangaladiman Gobir, kuma Natsinin Kabi, Malam Alu, É—ansa Malam Usman Manu ya gade shi, kuma ya shekara goma sha É—aya watau daga 1901-1912. Haka kuma, É—ansa Malam Muhammadu Nababa, ya zama babban Malami a Æ™asar Argungu, wanda ake girmamawa matuÆ™a, shi ne kakan Wakilin Daular Gobir Sardauna Muhammad Lawal Argungu. 

    Al-Æ™ur’ani Mai Girma, Hizu Sitin –ƘIra’ar Warsh, wanda Dangaladiman Gobir Malam Alu É—an Sarkin Gobir Yakuba, ya rubuta da hannunsa, a  shekarar 1860, kuma shi ne Natsinen Kabbi na farko, daga shekara 18601901.

     

    Gogarma babbar laya, wadda ÆŠangaladiman Gobir

    da almajiransa suka bai wa Sarkin Kabi Sama

    Tarihin Hausawa

    Tarihin Hausawa

    Tarihin Hausawa

    Tarihin Hausawa

    Tarihin Hausawa

    Tarihin Hausawa

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.