Na
Dokta Korao H. Mahamadu
Gabatarwa
A’uzu billahi minal shaitani razim.
Bismillahi Rahamani Rahim
Assalamu alaikum jama’a ‘yan uwa, kuma barkammu da yau.
Idan ba ku manta ba, yau da ‘yan shekaru ke nan, muka ce muku, harshen Hausa, harshe ne na farko, wanda daga gare shi ne yawancin harsunan duniyar nan suka fita; kuma mun Æ™ara da cewa Hausa na da rubutu, wanda shi ma ya aifi yawancin rubutu da yawancin mutane ke anfani da shi kamar su Latina, Larabci da sauransu. To, ina hujjar wannan bayani?
Za mu yi anfani da harshe da rubutun Hausa, domin a gane. Sai ku biyo mu sau da ƙafa.
I. /. Harshen Hausa
Tabbat, harshen Hausa, harshen farko ne, kuma
da izinin Allah, za mu gwada muku hujjojin. Yanzu dai
za mu yi anfani kaÉ—an da harshen Hausa don mu nuna muku kaÉ—an daga cikin
martabobinsa.
Idan ba ku
manta ba, ƙasa da rana da wata da tarmamu da saurensu, sun bayyana ne a gare
mu, bayan tsayuwar jirgin tsira na Annabi Nuhu (T.A.A.T.G). A lokacin da rana
da wata da tarmamu suka bayyana, wata ƙabila ta riƙa bauta musu, bauta ta
fuskar addini. Kuma jagoran addinin shi ne wakilin rana da wata da tarmamu da
saurensu.
To wace
ƙabila ce ta farko wadda ta bauta ma waɗannan abubuwan? Ai babu shakka HAUSAWA
ne !
Hujja ?
Sunaye da
kalmomi kuma da karin magana dangane da rana da wata da tarmamu da saurensu da
ake samu a cikin harshen Hausa. Wakillan Rana da Dare, can da farko, RA da RE
ake kiransu da Hausar ainahi.
Ƙaƙa RA da RE
za su ba mu kalmomi da sunaye da karin magana da yawa a cikin harshen Hausa ?
RA da RE wakillan rana da dare ne, kuma su ne za su yaÉ—aÉ—a addini ko’ina cikin duniyar nan. YaÉ—uwar addinin RA da RE (kowa da nashi), zai Æ™arfafa harshen Hausa ta fuskar kalmomi da sunaye da karin magana, kamar haka:
1.1. /. Da
kalmar RA.
Za mu samu haka:
RA - NAWA
RA - NAW
RA – NA
RANAWA, da
RANAW da RANA, dukkansu ma’anarsu guda ce, cewa da ALLAH NE. To, masu sauraren mu, kar a zarge mu
da cewa mun soki ra’ayin addinin musulunci ko na christa ko kuma can wani
addini, muna bada wannan sanarwa, domin a san mafari da manufa. A game da wannan lamari na RA - NA, waÉ—anne kalmomi ne da sunaye da
karin magana za mu samu?
A kwai :
RANA
RANI
RANAU
RAKEA
RANARKA
BA KA DA RANA
RANKA YA DAÆŠE
ds…
Idan an ji kuma an gane da yanda muka samu
kalmomi da sunaye da karin magana da RA ko da RE, ƙaƙa ne? Wannan tambayar ce
ke ba mu damar anfani da aji na biyu, cewa da RE.
1.2. /. Da Kalmar RE
A fuskar bauta ma rana da wata da tarmamu, ba a
kiran RA ba tare da RE ba. Wannan al’amarin zai ba mu kalmomi, da sunaye da
Karin magana kamar haka:
RA – NAWA da RE
RA – NAW da RE
RA – NA da RE
Dukan waÉ—annan sheÉ—arun ma’anarsu guda ce, cewa
da RANA DARE, inda muke Æ™wanÆ™wance sunayen rana da dare, wa’anda suke makamman
ainahi na awon lokaci ga harshen Hausa. A game da RE waÉ—anne kalmomi da sunaye
da Karin magana ne za mu samu?
A
kwai:
DARE
ADARE
BABARBARE
BA’ADARE
BA’ARE
GARE KA
RENI
ds...
Kun dai ji a taƙaice, kuma kun gane da yanda
muka samu kalmomi da sunaye da karin magana da waÉ—annan kalmomin cewa da RA da
RE, waÉ—anda a duniyar nan, ba su da ma’ana in ba ga harshen Hausa ba. Kuma idan
ba ku yarda ba ku jarraba da duk harshen da kuke so, ku gani!
1.3. /. Sakamako
Dangane da wannan sanarwa, mine ne ya kamata a
gane kuma a riƙe?
Na É—aya shi ne, yanda harshen Hausa ke gudanar
da al’amuransa.
Na biyu ko, ya shafi kaÉ—an daga cikin tarihin Hausawa.
Sai ku biyo
mu sau da ƙafa.
1.3.1. /. Sakamako Kan Harshe
Abin da ya kamata a gane na farko a game da
harshen Hausa shi ne, harshen Hausa kamar ƙwame yake, ba harshe ba ne wanda ke
buÉ—e kamar yawancin harsunan duniya;
Abu na biyu wanda ya kamata a gane, kuma a riƙe
game da harshen Hausa shi ne wannan haÉ—uwa, gamuwa, É—oriya, ko kuma auren
ƙaramin baƙi da babban baƙi, wanda ake kira
gaɓa ko syllable a turance.
Harshen Hausa ne kaÉ—ai zai bada fassara da ma’ana a kowace gaÉ“a;
Abu na ukku wanda ya kamata a gane shi ne
lauɗi: ana iya a ja shi, ko a taƙure shi, ko kuma a lanƙwasa shi; wannan lauɗin
na harshen Hausa, ya ɗauko tushensa ne daga wannan ɗoriyar gaɓoɓin.
Wannan lauÉ—in na harshen Hausa na ba mu damar
kwatamta sheɗara ko jumla, kamar sarƙa, ita kuma gaɓa ko syllable kamar zobe.
Ku san da sani cewa, idan a kwai zobe, to sarƙa ba ta ƙarewa, haka harshen Hausa
yake;
Abu na huÉ—u wanda ya kamata a gane ga harshen Hausa
shi ne: duka kalma, sheÉ—ara ce ko jumla; haka kuma duka sheÉ—ara ko jumla na iya
taƙurewa ta koma kalma, kamar dai yanda kuka ji ɗazu.
Abu na biyar wanda ya kamata a riƙe shi ne
bambanci da ke da kwai tsakanin harsunan duniya:
Akwai harsuna na ainahi, kamar harshen Hausa;
Harshen ainahi kamar ƙwame yake, ba harshe ba ne wanda ke buɗe, a rufe yake,
idan babu mabuɗi, sai a yi haƙuri.
A kwai aifaffi; Su dai aifaffin harsuna, rabi
rufe rabi buɗe; kuma ba su kama da ƙwame.
A kwai yayayyi, waÉ—anda a buÉ—e suke samsamsam.
Abin da ya kamata a gane kuma a riƙe a nan shi
ne, kwatamci da harshen Hausa; duk harshen da ba ya yi kamar harshen Hausa, to
ba na ainahi ne ba, kuma ƙarshensa ɓacewa, ba yin mutum ba ne, sarautar Allah
ce.
Kun dai ji a taÆ™aice kaÉ—an daga cikin al’amuran
harshen Hausa, yanzu sai mu shiga kaÉ—an daga cikin tarihin Hausawa.
1.3.2./. Sakamako Kan Tarihi
Sakamako na farko kan tarihi, shi ne tabbata
muku da cewa, mutanen farko a duniyar nan, wanda suka fara addini, baƙaƙe ne,
kuma Hausawa ne; sun fara da addinin rana da wata da tarmamu, sai addinin
gumaka ya biyo, sannan sauran;
Sakamako na biyu kan tarihi shi ne, maimaitawa
da ƙwanƙwancewa bisa ga mutanen farko na ƙasar Misira ko Egypte.
Idan ba ku manta ba, Farfesa CHEICK ANTA DIOP
(Allah ya jiƙan shi, amin) na ƙasar Sanagal, ya tabbata muna da cewa mutanen
farko na ƙasar Misira, ainahi baƙaƙe ne, mu kuma muka ƙara da cewa Hausawa ne.
Ga hujjojin:
Hujja ta É—aya, hoto ne, da muka É—auko cikin
littafinsa mai suna baÆ™aÆ™e da al’adunsu,
ko kuma NATIONS NEGRES ET CULTURES,
bugu na huÉ—u, shafi na É—ari da goma. Shi dai wannan hoto an É—auke shi ne kamar
Fira’auna; Fira’auna ko kun san Misisra
ce;
Hujja ta biyu, ita ce MAGAJIYA
RAKEA, wadda ke ta ukku cikin sarakunan Gobirawa, sanannu. Za mu É—an dakatawa
kaɗan bisa ga MAGAJIYA RAKEA domin ƙarin bayani.
Magajiya, kun san dai sarautar mata ce a ƙasashemmu na Hausa? Kuma
wakiliyar ‘yan bori ce!
Rakea ko suna ne na mata a
ƙasashemmu na Hausa.
Idan ba ku manta ba, mun shaida
muku da cewa, harshen Hausa, harshe ne mai kwaÉ—o, to za mu sa mabuÉ—i mu buÉ—e
kwaÉ—on domin mu gane ma’anar wannan suna na RAKEA.
RAKEA suna ne mai nuhin RA-KE-A-EA. Kun gani a nan, sheÉ—ara
ce, ko jumla. Idan ta taƙure, ta koma suna, sai ta ba
mu RAKEA.
EA, INNA
dukansu ma’anarsu guda ce, cewa da uwar ‘yan bori.
A taÆ™aice RAKEA na nuhin uwar ‘yan bori. Wato
MAGAJIYA.
Wannan maccen, cewa da MAGAJIYA RAKEA, ita ce
gimbiya ta farko a duniyar nan, wadda ta kafa iko da addini a cikin ƙasar
Misira.
Hujja ta ukku, wannan sunan na Fira’auna, ko
kuma FARAON, wanda ‘yan mulkin
mallaka suka laƙa ma sarakunan Misira, kalmar Hausa ce, kuma tana dangane da
wannan gimbiyar, baHausa, cewa da RAKEA.
Abin ganewa a nan, shi ne can da ainahi FARAU a
ke cewa; kuma FARAU na nuhin waÉ—anda suka fara kafa mulki da addini a cikin
Æ™asar ta Misira, da magadansu; idan kun yi la’akari, dukansu na da sunaye
wanÉ—anda ake kiran su da shi.
Kenan al’amarin
Fira’auna daga baya ne ya wanzu, zamanin ikon ‘yan mulkin malakka, inda
suke kiran Sarkin Misira da wannan laƙabin.
Hujja ta huɗu, rijiya ukku cikin ƙasa ukku; ko
wace rijiya na game da ‘yar uwarta da sarÆ™a; rijiya ta farko na nan cikin
Misira; biyu ɗin na nan cikin ƙasashen Afirka, baƙar fata.
Sakamako na ukku kan tarihi shi ne gadon iko da
addini na gargajiya gare mu Hausawa.
Iko da addini na gargajiya, sun É—auko tushensu
ne daga RA da RE; kuma wannan kalma ce hujja: HATTARASA. Wanda duk ya je fadar
sarakunammu na gargajiya ya ji wannan kalma; to minene ma’anar wannan kalmar?
Za mu sa mabuÉ—i mu buÉ—e kalmar domin mu gane ma’ana ; sai ku biyo mu sau
da ƙafa:
HATTARASA
HAR TA RA SA
HAL TA RA SA
HAG GA
SARAUTA RA SA
HAR GA
SARAUTA RA SA
HAL GA
SARAUTAR RA SA
HATTARA SA!
Dukkan su
ma’anarsu guda ce, cewa da hattarasa.
Kuma duka
sarki na Hausa da rawani aka san shi ; kenan rawani hikimar sarauta
ce ; idan haka gaskiya ne to mine ne ma’anar rawani? A nan ma za mu yi
anfani da mabuÉ—i domin fahimta ;
RAWANI kalma
ce wadda ta ƙumshi gaɓa ukku :
A kwai RA (ku
tuna da bayanin É—azu),
a kwai WA
(mai nuhin babba, magaji),
a kwai
NI (aikau) mai nuhin mai magana.
Kun ga RAWANI
kalma ce mai nuhin zawati ko kyalle na naÉ—awa ga kai, to amma idan muka walwale
kalmar sai mu gane ma’ana da manufa. Kenan RAWANI al’adar Hausawa ce, kuma ta
É—auko tushenta ne tun daga RA.
Sakamako na
huÉ—u, shi ne gadon sarautar mata ga Hausawa. Tabbat, ikon Sarauniya SABA,
Sarauniya DAURA, Sarauniya TAHAWWA, Sarauniya MANGOU, ba tatsinniya ba ce,
gaskiya ne, kuma dukansu sun É—auko tushensu ne daga RA.
Sakamako na
biyar shi ne jikokin waɗanda suka gina waɗannan daulolin na ƙasar Misira,
waÉ—anda ake kira pyramide, na nan
cikin Najeriya da Nijar.
Sakamako na
shidda, shi ne jikokin Nubiyawan farko, na nan cikin Najeriya da Nijar.
Sakamako na
bakwai shi ne yawancin sunayen ƙabiloli, Hausa ce. Misali: SUMERIEN, AGADIEN, KANANEEN, ARAMEEN,
MANDING, BAMBARA, KOTO KOLLI… ds.
Yawancin
sunayen ƙasashe, Hausa ce. Misali: BABYLONIE, EGYPTE, HABASHA, SOMALIE, YEMEN,
INDE …ds.
Sakamako na
takwas, shi ne ƙaryatar da tarihin Hausa na banza bakwai da Hausa bakwai.
Sakamako na
tara, shi ne Æ™aryatar da Æ™azafi da jahilci da ‘yan Æ™ar da Æ™amzon kurege ke yi,
cewa Hausawa larabawa ne, ko kuma yawancin kalmomin Hausa larabci ne.
Abin da ya
kamata a gane shi ne, kafin Annabi Mohammadu (S.L.A.S) ya zo duniyar nan, har
ya bayyana, akwai Hausawa; kuma a san da sani cewa Annabi Mohammadu (S.L.A.S),
annabi ne na ƙarshe sananne, kuma dalilin shi ne, harshe da addinin larabawa
suka yaɗu, a lokacin nan tuni Hausawa sun ƙaura.
YaÉ—uwar
addinin musulmunci, ko kuma jihadi da aka yi nan a ƙasashemmu na Hausa,
tsakanin junammu ne, baƙaƙe ; kuma
yawancin mayaƙan ba su jin larabci, balle a ce an ci mu da yaƙi, kuma an bida
mu da harshen larabci.
Akwai abu
guda wanda lalle mun yi imani da shi, shi ne aro, ko kuma fanfaÉ—e da ke akwai
tsakanin harshe da harshe, idan sun haÉ—u wuri guda.
To a faÉ—a
muna inda Hausawa suka zamna tare da larabawa a nan Afirka, har harsunansu suka
shiga juna, inda Hausa ta gaɓɓato, ko kuma ta zaɓɓato kalmomin larabci?
Haba jama’a, kar mu zama ‘yan amshin shata, ko
kuma kwando abin zuba shara. Mu hankalta, mu nazarta, mu ƙwanƙwanta, mu maida
niyya ga bincike domin fitar da takaici da jahilci, domin cin gaban kammu da
kammu.
Da wannan gargadi muke dasa aya ga wannan babi,
sai kuma mu gyara zama, mu karkaÉ—e kunnuwammu, domin sauraren babi na biyu,
wanda ke ba mu bayani kan rubutun Hausa, inda nan ma, za ku ji hikimar
kakannimmu.
II./.Rubutu
Rubutun farko a duniyar nan sananne, an same
shi a cikin wata ƙasa wadda a ke kira MESOPOTAMIE,
musamman ma a SUMMER.
(projection)
MESOPOTAMIE, kalmar Girkawa ce mai ma’ana MESOS (tsakkiya) POTAMOS (ruwa), wanda muke kira tsibiri da harshen Hausa; tsibiri
ko kalma ce wadda ta fito daga cibi RA; cibi RA na nufin wuri inda rana ta fara
bayyana a cikin duniyar nan.
SUMMER ko, fassarar kalma
ce mai faÉ—in daga inda masu rubutun suka fito. Sumer ko kalmar Hausa ce mai
nuhin bisa.
Ga wani dan
misali, domin ku gane al’amarin:
DU ga
wannan kalmar an yi hoton tudu;
SAG ga wannan an yi hoton kai tsaye;
DU ga
wannan an yi hoton tafiya ko gudu;
KUR ga wannan an yi hoton duwatsu;
TUM an ce
É—auka;
DUDU an
ce ƙafa, dudduge;
GUB an ce
tashi tsaye, ko kuma sa ;
KI. an ce kibbiya ko kuma kihi.
Dukan waÉ—annan kalmomin, ba su da ma’ana ga
larabci ko ga yahudanci, ko kuma ga duk harshen da kuke so, in ba harshen Hausa
ba; ku tuna da abin da muka shaida muku É—azu. Don dai ku gane, kuma ku yarda,
za mu shiga cikin ma’anar wannan kalmomin. Sai mu Koma Ga Ma’ana Ta Sama.
2.1.2./.
Rubutu Mai Lungu Ko Cuneiforme
Shi dai wannan rubutun ana kiran shi da sunan «Ã©criture cunéiforme» ; wannan
kalmar ta CUNEIFORME ta fito ne daga CUENUS mais nufin lungu, FORME (kama) ; a taƙaice dai wannan
kalmar na nufin rubutu mai lunguna ko kuma mai kama da ƙusa ;
Ga dai alamar rubutun:
(projection)
Abin tambaya a nan shi ne: wace ƙabila ce ta
ƙirƙiro wannan rubutun?
Masu ilimin bincike, sun faÉ—i cewa, wannan
hikimar SEMITES ce, wato Yahudawa da
Larabawa da saurensu, tunda su ne aka tarda a wurin. Amma inda abin yake da
É—armun kai, shi ne yanda su magadan rubutun, ba su anfani da shi ta fuskar
Æ™ere-Æ™ere ko sutura ko gini ko lamba ko shaidu…ds, har su bada gudummuwa ga
ƙwanƙwancewa da fassarar rubutun .
Wannan
lamarin ya É—aure ma yawancin masu ilimin harshe kai, ko kuma masu nazari.
Wannan hanyar da suka É—auka, ba ta dace ba , shi ya sa waÉ—ansu masu
hankali, kamar Jean BOTTERO, sun yi watsi da lamarin, inda
suka ce ya kamata a maida bincike bisa ga wasu ƙabilu inda waɗannan kalmomin za
su samu ma’ana cikakka. Wannan daidaituwar, za ta bunÆ™asa, kuma za ta Æ™arfafa
wannan ilimin da ake kira archeologie,
wato (ilimin kufai).
A fuskar rubutun, gogayen aikin sune :
SIR WILLIAM FLINDERS
PETRIE (1905);
A.H.GARDINER, (1915);
ALBRIGHT, (1948);
CLAUDE SCHAEFFER;
(1929)…ds.
A nan, sakamako ya rinjaya ne ga yanda mutanen
ke anfani da laka ta fuskar rubutu, ko kayan aiki ko na ƙawa da saurensu.
WaÉ—annan abubuwan namu ne, tunda har kwanan gobe, za mu yi anfani da su. Akwai
wasu abubuwa waɗanda aka binciko a nan ƙasashemmu na Afirka masu kama da
hakanan. Idan ko haka gaskiya ne, to biri ya yi kama da mutum.
A cikin wani littafi mai suna « tsakanin
adali da rubutu , shekara ta 1994» da malam JACK GOODIE ya gabatar,
mun samu wurin da aka ba mu bayani kan wannan rubutun, cewa ya ƙumshi babbaƙu
talatin da biyu (32). Su dai waɗannan babbaƙun ana rubuta su ne daga hauni zuwa
dama, kuma sun fito ne daga cikin na Kanana ainahi tun ƙarni goma sha hudu
kahin aihuwar annabi ISA (T.A.T.A.).
Shi kuma wannan rubutun ya aifar da na PHENICIENS, mai babbaƙu ishirin da biyu
(22) ; su kuma Yahudawa da Girkawa, sun ramta daga gare su wajen ƙarni
goma sha ukku.
Idan kuma mun komo ga wannan rubutun HIEROGLYPHE, wato HIERO (sacre: tsarkakke) GLYPHE (écriture: rubutu), sai mu gane da cewa duk
waÉ—annan kalmomin, na harshen Girkawa ne, ke nan rubutu ya rinjaye su; Idan ko
haka gaskiya ne, abun tambaya a nan shi ne: shin wai su masu yin wannan rubutu,
farfaru ne ko baƙaƙe? Ƙaƙa suke kiran
rubutun? Ba a yin la’akari da wannan
damuwar, sai dai a cilasta muna da ƙarya.
Ba za mu yarda ba, kuma da iznin Allah za mu ci
gaba da bincike don ci-gaban kammu da kammu.
2.2./. Alamar
Babbaƙun Duniya
Alamar babbaƙun duniya ta kasu gida biyu :
akwai na farar fata, kuma akwai na baƙar fata.
2.2.1.1./. EGYPTE
A. I. Y. Y. W. W. B. H. P. F. M. M. N. R. H. H.
H. H. S. S. CH. K. K.F. G. T. TJ. D. DJ.
(projection)
2.2.1.2./.COPHTE
A. V. G. D. E. S. Z. I. TH. I. K. L. M. N. X.
O. P. R. S. T. E. F. CH. PF. O. SC. F. CH. H. G. SC. D.
(Projection)
2.2.1.3./. GREC
Babbaƙun grec sun kasu gida ishirin da huɗu
(24); ga yanda suke:
A .V.G. D. E. Z. I.TH. I. K. L. M. N. X. O. P. R. S. T. Y. PH. CH. PS. O.
Idan muka lura, a cikin babbaƙun, babu waɗansu,
kamar su B. C. F. G. H. J. Q. U. W.Y.
(projection)
A game da ainahin waÉ—annan babbaÆ™un, ra’ayi ya
kasu gida biyu:
Waɗansu kamar GELB sun ce an ƙirƙiro su a Grece
wajen 750 kahin aifuwar Annabi ISA;
WaÉ—ansu ko sun ce Samidawan yamma ne suka
ƙirƙiro su wajen 700 kahin aifuwar Annabi ISA.
A game da babbaƙun, abin da Girkawa suka yi,
shi ne ƙara hikima ga wasulla daidai da harshensu.
Idan muka dawo kan babbaƙun, za mu gane da
cewa, Girkawa da Samidawa sun yi abun ga da Hausawa ke cewa “hankaka maida Æ™wan
wani naka”. WaÉ—ansu masu hankali, kamar su COLDSTREAM
1977, HAVELOCK 1973, GOODY da WATT
1963, sun ce wannan zance bai dace
ba; Inda rubutu ya fito ainahi, shi ne ASIE
MINEURE. Sun ƙara da cewa babbaƙu da tsari da kamar babbaƙu, aikin mutane
ne masu magana da harshen KANANA,
harshen Samidawa.
Kash! Ga zance ya bi hanya to amma sai ya
ratse, tunda cikin sarakunan gobirawa sanannu, akwai na farin mai suna KANANA,
Gobirawa ko baƙaƙe ne. Idan ko haka
gaskiya ne, Kananawa ba Samidawa ba ne, ba Larabawa ba ne, ba Yahudawa ba ne,
ba Geze ba ne, ba ma Kiyaya ba ne , manoma ne, kuma suna cikin zuri’ar jikokin
Annabi Nuhu (T. A..A.S.T.G.).
2.2.1.4./. LATINA
A. B. G. D. E. V. Z. K. L. M. N. O. R. T.
(projection)
2.2.1.5./. YAHUDAWA
Babbaƙun
Yahudawa talatin da É—aya ne; ga dai kamanninsu:
A. B. V. G.
D. H. W. Z. H. T. Y. K. KH. K. L. M. M. N. N. S. A’. P. F. F. TS. TS. K. F. SH. S. T.
(projection)
2.2.1.6./. LARABAWA
A. B. T. TS. DJ. H. KH. D. Z. R. Z. S. SH. S.
DH. T. Z. A’. GH. F. Q. K. L. M. N. H. W. Y.
(projection)
2.2.1.7./. ETHIOPIE
H. I. H. M. S. R. S. S. Q. B. T. TCH. H. N. GN.
A. K. H. W. A. Z. S. Y. D. J. G. T. TCH. P. S. S. F. P.
(projection)
2.2.1.8./.LYBIQUE
B. G. D. W.
Z. Z. Z. T. I. K. L. M. N. S. S. F. C. Q. R. S. T. T.
(projection)
2.2.1.9./. TIFINAGH
B. CH. D. D. F. G. DJ. H. I. J. K. O. KH. L. M
. N. W. R. S. T. T. Z.
B. G. D. H. W. Z. H. T. Y. K. L. M. N. S. G. S.
Q. R. S. T. F. G. Z. D. D. Z. H.
° = a; é; e; i
(projection)
Abin da ya kamata a lura da shi a nan, shi ne
yanda babbaƙun suke:
zube barkatai;
ba tsari;
ba ma’ana;
ba a san ba wanda ya ƙirƙiro su;
waÉ—ansu sun fi waÉ—ansu yawa ;
babu cikakkun
wasullai ;
babu ayoyi
babu langayen
wasullai ;…ds.
Ko wannan
al’amarin ne ya sa, watakila, ake kiran rubutun zamani da sunan « écriture conventionnelle : rubutu na yarjejeniya » ?
2.2.2./. Ma’anar BabbaÆ™un A
Jimilce
ALEPH
na nufin “sa” da harshen semitique,
wannan baÆ™i babu shi ga harshen Girkawa, amma sun É—auke shi kamar «a» ;
BET: na nufin “gida” ko “tanti”, kuma ma’anar shi “b”;
GAML: na nufin “raÆ™umi”, ko kuma “tozon
raÆ™umi” g;
DELT: na nufin “Æ™ofa” d;
HE: babu ma’ana h;
WAU : na nufin “kusa” ko kuma “ijiyar
sau”; babu shi da harshen Girkawa:
ZAI : na nufin “icce mai
bada olive”;
HET: na nufin
« katanga » ko «shimge» ;
TET : babu
ma’ana ;
YOD : na nufin
« hannu » ;
KAF:
na nufin « tahin hannu » ;
LAMD:
babu ma’ana;
MEM: na nufin “ruwa”;
NUN : na nuhin “kihi”;
AIN: na nufin “ijiya”;
PE : na nufin “baki”;
SADE :na nufin “É—an fatsa”
ko “lauje” ko kuma “hanci”;
QOF: babu ma’ana;
RES: na nufin “kai”;
SIN : na nufin “haÆ™ori”;
TAU : na nufin “shaida” ko
kuma “lamba”.
Idan aka
jimilta waɗannan babbaƙun, sai mu ce su ishirin da ɗaya ne (21); waɗansu na da
ma’ana, kuma waÉ—ansu ba su da ma’ana;
Abin da muka
gane a nan , shi ne: harsuna ukku ke anfani da waɗannan babbaƙun: akwai
yahudanci, akwai larabci, akwai misiranci. Misiranci ko ba harshen semites ba ne, kamar yanda ake kirari
cewa babbaƙu ko kuma alphabet aikin
Samidawa ne. Abun
tambaya a nan shi ne, yaya ake Æ™era abun da ba ya da suna, ba ya da ma’ana?
A nan ma, ya isa mu gane da cewa, alphabet dai, ba aikin Samidawa ne ba,
kuma ba aikin Turawa ne ba; idan haka gaskiya ne, to ina ya kamata mu maida
bincike da nazari kan asalin rubutu, ko kuma asalin alphabet ?
Tunda su dai Shinuwa (mutanen Sin) da Indiya (mutanen Hindu) ba su da alphabet, ai sai mu nuho Afirka, baƙar
fata, mu gani ko!
To haka É—in ba ta faru ba; ke nan dai, sun
sani, don wannan ne, ta wani fanni, ake gallaza muna, ake sa muna yunwa da
ƙishirwa, da yaƙi da sauransu, don kar mu ci gaba! Abun tambaya a nan shi
ne : shin wai wannan rubutun da su Turawa da Larabawa da sauransu ke
tamaƙa da kuri da shi, daga ina ya fito ? To a nan ne babbar hikimar
wannan sakamakon bincikemmu da nazari kan rubutun Hausa da za mu ba ku zuwa
gaba idan Allah Sarkin sarauta ya yarda.
Kafin ranar za mu ba ku É—an bayani kaÉ—an ga
ma’ana da fassara kan babbaÆ™un latina ko na larabci, kamar dai yanda Turawa
masu bincike da nazari kan lamarin suka faÉ—i ; Ga wani É—an misali wanda LOUIS-JEAN CALVET, Farfesa na ilimin
al’umma da harshe na Jami’ar SORBONE
ya bada a cikin littafinsa mai suna « HISTOIRE
DE L’ECRITURE : Tarihin Rubutu», FEVRIER 1997:
Idan muka gane da cewa baƙi ya fito daga hoton
abubuwa, to a nan ma, waɗansu babbaƙun, ba su da tushe; yaya aka yi haka? Zancen ga ko akwai gaskiya dai? Idan muka
ɗauki ɗan misali kaɗan kan babbaƙun (aleph da delt), sai mu ce akwai duhu cikin
lamarin;
Kowa ya san Larabawa da Yahudawa ba makiyayan
shanu ne ba; ba su da shanu duk duk duk; To daga ina ne “sa” ya fito har yake
nufin “a”?
To amma inda wannan lamari zai fi dacewa, da
inda zai fi ma’ana sai ga HAUSAWA (masu hawan shanu); wanda ko ba ya da sa, ba
shi hawan sa, balle ya yi zancen sa! Ke nan wannan baƙi, cewa da A, tushen alphabet, magana ce a dunƙule, mai nufin
masu shanu mafarin alphabet, biri ko
ya yi kama da mutun; za ku samu ƙarin haske zuwa gaba, bayan exposition (nuni) da iznin Allah !
Baƙi na biyu wanda muka ɗauka don misali, shi
ne DELT; shi dai wannan baƙin an
ɗauke shi kamar ƙofa mai lungu ukku. Abun tambaya a nan shi ne: wane irin gida
ne mai wannan Æ™ofar, wanda ya dace da tabi’o’in makiyaya, masu gidan fata? Wannan ma’ana dai ba ta dace ba, kuma haka
dai ake yi domin a ɓatar da mu, a ƙara tura mu cikin daji.
Kun ji kuma kun gani, yanda ake horon mu da
cewa rubutu, aikin makiyaya ne, musanman Larabawa da Yahudawa. Akwai gaskiya ko
? Amsa na gare ku matasa.
Abin da muka amince ma, shi ne yanda babbaƙu ke
fitowa daga hoto; amma fassara da ma’ana da tushen babbaÆ™u na latina da na
larabawa da yahudawa, ba mu amince ba, kuma za mu yi yaƙi matuƙa kan lamarin
har gaskiya ta tabbata da iznin Allah !
Ga dai wani É—an misali tamkar shirme wanda shi
wannan baturen, Farfesa CALVET, ya
rubuta kan ainahin baƙi.
(projection)
Na É—aya, ya É—auki hoton rana, wanda ake kira da
sunan “soleil” da harshen faransanci,
“solej” da wani harshe.
Na biyu, ya É—auki hoton rana, wanda ake kira “ra” da harshen mutanen Misira, wanda ya
kira copte, “soleil” da harshen faransanci. Sai ya ce
waÉ—annan misalan biyu, ba su da dangantaka, kuma ba su kama da juna ta fuskar
ainahin baƙi.
Wacce ce
hujjarsa, tunda ya ce wannan kalmar ta mutanen Misira ce, ai akwai su can
dauri, ya tambaye su mana, ya ji ma’ana ko kuma fassarar “ra”, in dai har
binciken gaskiya ne yake yi, ai zai gane kurensa, domin ƙarin haske kan
lamarin, to hakanan É—in ba ta faru ba, don son rai, don son suna da girman kai.
Akwai
dangantaka ƙwarai tsakanin misalan biyu, kuma suna kama da juna ta fuskar
ainahin baÆ™in. Idan ba ku manta ba, ai “ra”
rana ce ko, kuma mun gani yanda wannan kalmar ta “ra” ta ba mu kalmomi, da sunaye da karin magana a cikin harshen Hausa;
Kuma harshen Hausa kaÉ—ai ya kai hakanan, wanda duk ya yi gardama ya jarraba ya
gani.
2.2.3./. Babbaƙun Baƙar Fata
A game da
rubutun duniya, Turawa sun ce, kowace ƙabila ta gwada hikimarta kan
lamarin ; To amma shi baÆ™in mutum, iliminsa bai ba shi wannan fusa’ar
ba ; Wannan ƙazafi ya damu wasu Afirkawa, inda suka ƙirƙiro rubutu
iri-iri, kamar haka:
(projection).
2.2.3.1/. WOLOF
A. C. M. K. B. MB. J. NJ. S. W. L. G. NG. N. D.
ND. X. H. Y. T. R. N. F. N. R.
2.2.3.2./. MASABA
P. T. C. K. B. D. J. G. F. S. NZ. M. N. NY. N.
Y. W. H. L. R.
2.2.3.3./. MANENKA
H. P. R. DY. TY. D. R. S. GB. F. K. L. M. NY.
N. H. W. Y.
Abun takaici a nan , shi ne duk da kishin da
waÉ—annan Afirkawa suka yi, rubutun nasu bai samu martaba ba kuma bai samu
karÉ“uwa ba ga ma’ikontammu da mutane.
A game da ainahin babbaÆ™u da ma’anarsu, mun
gano da cewa zama dai bai same mu ba, don haka muke cewa a sake bincike.
III./. A Sake Bincike Kan Rubutun
Ainahi
3.1./.Ainahi Ko Tushen Rubutun Hausa
Shi dai wannan rubutun, mun same shi ne ga wani
bawan Allah, a jahar MARADI, ƙaramar hukumar Dakoro, jamhuriyar Nijar.
Wannan bawan Allah, bahaushe ne, bagobiri;
Sunansa DOGUWA MAI WASA (Allah ya
jiƙan shi. Amin). Manomi ne, kuma mahalbi ne. Ya gadi wannan rubutun ga
kakansa, shi kuma ya hori jikansa mai suna ADARE
SALIHU. Shi
kuma Adare Salihu ƙane ne gare ni.
Ana
anfani da wannan rubutun ta fuskar bambanta magungunan gargajiya.
Babu shakka Hausawa na da rubutu, wanda ke
Æ™umshe da ma’ana, da hikima, da Æ™ayatarwa.
Ga alamar rubutun:
(Projection)
Rubutun Hausa na ƙumshe da abubuwa guda biyar
masu É—imbin ma’ana:
Kafin mu ba
ku bayani dalla dalla, muna son mu fara da yanayin furuci na harshen Hausa.
Harshen Hausa na da yanayin furuci guda goma
sha É—aya (11):
Akwai zuzau
Akwai tunkuÉ—au
Akwai ragaÉ—e
Akwai ragare
Akwai tsayau
ds…
Idan ana son
a jimilta babbaƙun Hausa, sai mu ce su
arba’in da É—aya ne (41). Yaya ne su babbaÆ™un ke gudanar da
rayuwarsu ? Sai ku saurare mu da
kyau.
Babbaƙun Hausa
sun kasu gida biyu :
Akwai maza ;
Akwai
mata ;
Akwai
manya ;
Akwai ƙanana.
Idan kuma
muna son mu kwatamta babbaÆ™un Hausa, sai mu ce al’amuransu É—aya suke da duk
halittar Allah. Tunda mun shaida muku da cewa a cikin babbaƙun Hausa akwai maza
kuma akwai mata, to ku san da sani aure zai wanzuwa tsakaninsu, inda a cikin
arba’in da É—aya, takwas aifaffi ne. Wannan lamarin na babbaÆ™un Hausa, zai ba mu
damar ganewa da wannan hikimar ta bambanta namijin kalma da tamatan kalma
(wanda ake kira a turanci genre),
tunda kalmomin da babbaƙu aka yi su; Wannan wani abun ƙayatarwa ne ga masu
ilimin harshe, inda har yanzu ba su hango ba da cewa a cikin babbaƙu, akwai
maza kuma akwai mata. Dukansu babbaÆ™un, kowanne da sunansa, kuma da ma’anarsa.
Bayan babbaƙun Hausa, akwai wasulla. Dukan
tursassan wasullan Hausa su bakwai ne (7); Kowane wasali da sunansa kuma da
ma’anarsa.
Alamar
rubutun Hausa ta ukku, ita ce langayen wasullai. Su ma sun kasu gida bakwai; a
cikinsu akwai masu tafiya da manyan babbaƙu, kuma akwai masu tafiya da ƙananan
babbaÆ™u. A nan ma, kowane langayen wasali da sunansa da ma’anarsa, kuma da
aikin da yake yi bisa ga kowane baƙi.
Akwai goyon
wasullai, su ma su tara ne (9). Akwai ‘yan biyu, akwai ‘yan ukku, akwai ‘yan
huÉ—u.
Alama ta huÉ—u
ita ce ayoyin Hausa. Ayoyin rubutun Hausa sun kasu gida goma (10), kuma kowace
aya na da sunanta da ma’anarta, da aikin da take yi a kan kowace sheÉ—ara ko
jumla.
Alama ta
Æ™arshe ita ce ta ‘yan lissafi, su kuma sun daidata kan gida tara (9).
Kowane É—an lissafi na da sunansa da ma’anarsa.
3.5.6./. Wakillan ‘Yan Lissafi
Wakillan ‘yan lissafin Hausa kala biyar ne (5):
akwai ‘yan ragau, akwai ‘yan Æ™arau, akwai ‘yan ruÉ“anyau, akwai ‘yan raÉ“au,
akwai ‘yan daidaitau.
Taƙaitawa
Ga wata tambaya, jama’a: shin wanda bai san ba
daga inda ya fito, ƙaƙa za ya sanin kansa, har ya san manufa, har ya yi zancen
wani? Saboda haka, dangi ‘yan uwa, muna kira gare ku: mu farka, mu tashi tsaye, mu so junammu, mu rungumi
junammu, mu haɗa kanummu, mu yaƙi jahilci da talauci da sauransu, domin
ci-gabammu da kammu, domin rayuwarmu da kammu, domin tsirar kammu da kammu.
A nan za mu
dasa aya kan rubutun Hausa, sauran bayani sai ranar bikin nuna ma duniya
rubutun (exposition).
BIBLIOGRAPHIE
1/.LA BIBLE
2/. BOUBOU
HAMA, «Histoire du Gobir et de Sokoto», Présence Africaine, 1967
3/. C
HARLES HOUGOUGNET «L’écriture», édition
PUF
4/. CLAIRE
LALOUETTE, «Au royaume d’égypte, le temps des rois-dieux», éd. Fayard 1991.
5/. CHAICK
ANTA DIOP, «nations nègres et cultures», Présence Africaine, 1979
6/. CHAICK ANTA DIOP, « L’unité culturelle
de l’Afrique noire », Presence Africaine, 1982
7/. CHAICK ANTA DIOP, «Parenté génétique de
l’égyptien pharaonique et des langues négro
africaines», NEA, 1977
8/. DOMINIQUE SOURDEL, «Histoire des arabes»,
Que-Sais-Je, PUF, 1985
9/.
GEORGES ROUX «La mésopotamie», Seuil,
1995
10/. GERARD
NAHON, «Les Hebreux», édition seuil
11/. JACK GOODY
«Entre l’oralité et l’écriture», PUF, Juin 1994
12/. JEAN BOTTERO et MARIE JOSEPH STEVE «Il était
une fois la mésopotamie», édition découvertes Gallimard, 1993.
13/. JEAN
DORESSE, «L’empire du Pretre Jean, l’éthiopie antique», édition plon, 1957
14/. LOUIS JEAN- CALVET «L’histoire de
l’écriture»,Plon, 1996.
15/. FRANCIS
AUFRAY, «Les anciens éthiopiens», édition Armand Colin, Paris 1990
16/. LE SAINT
CORAN
17/. HIRA
DA :
KORAU ANGO;
DOGUWA MAI
WASSA;
ADARE SALIHU.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.