Gobir tsohuwar Daula ce da ta shiga gwagwarmaya da daulolin duniyar Sudaniyya. Burin wannan bincike ƙyallaro wasu daga cikin dalilan da suka ɗaga Daular Gobir da Gobirawa sama ga sauran dauloli. An yi garkuwa da fitattun ayyuka wallafaffu da waɗanda ba a wallafa ba tare da taimakon yawon rangadi da tattaunawa da dafa kafaɗar adabin baka da rubutacce. Binciken ya gano cewa, Daular Gobir cin gashin kanta take yi kuma Bahaushiyar Daula ce. Bugu da ƙari, ta ƙi ta aminta da tarihihin Bayajidda ya ratsa Daularta. Dabarun yaƙin Daular Gobir da siyasar sarautunta sun yi tasiri sosai ga daulolin Sudaniyya. Babu Daula daga cikin daulolin Sudaniyya da ta yi yaƙe-yaƙen Daular Gobir. Ƙasar Gobir, Gobirawa suka sari abarsu kuma su suka fara sarauta a ciki duk wani baƙo da ya zo ciki sai dai auratayya ta narkar da shi ya zama Bagobiri. Binciken ya gano, rushewar Alkalawa bai rusa masarautun Gobirawa ba da haɗin kansu. Akwai buƙatar samun cikakken kundin tarihin Gobirwa da al’adunsu domin a taskace shi a kundin tarihin duniya. Gobir ta cancanci haka idan aka yi la’akari da tarihinta da ƙarfin ikonta.
Ba A Wane Bakin Banza: Gurbin Daular Gobir Da Gobirawa A Farfajiyar Sudaniyya
Aliyu
Muhammadu Bunza,
Sashen
Harsuna Da Al’adu,
Tsangayar
Fasaha Da Ilimi,
Jami’ar
Tarayya Gusau,
Jihar
Zamfara
Gabatarwa
Fitaccen mutum, gawurtacce, buwayayye, maɗaukaki, a ji mutum a ga mutum, a san mutum ya yi mutum, shi ne ‘wane’ a Bahaushen tunani. Wane wakilin suna ne mai wakiltar wanda ya yi fice, sunansa ya yi zarra, son kowa ƙin wanda ya rasa. A tunanin Bahaushe, ruwa ba sa tsami banza, matuƙar an yarda da ‘zomo ba ya kamuwa daga zaune’, wanda duk aka ga zomo rataye a kafaɗarsa shi ne ‘wane’. Wannan shi ne hangen Bahaushe na ‘kowa ya ci zomo ya ci gudu’. A duniyar mutane[1] da iskoki[2], ba yadda sunan wani ko wata ko wasu zai yi fice ya mamaye duniyar haƙiƙa da adabi, face yana da wata ɗaukaka da ya buwaya da ita. Ma’aunin wanna takarda a sikelin ‘ba a wane bakin banza’ shi ne, ƙasar Gobir da Gobirawa da suka ɗaukaka sunanta a farfajiyar Sudaniyya. Tunanin wannan bincike shi ne, yaya ƙasar Gobir ta zama wance daga cikin ƙasashen Sudaniyya? Me ya sa za a ce wa Bagobiri ‘wane’ daga cikin dangogin zuriyar al’umma da suka mamaye farfajiyar Sudaniyya?
Dabarun Bincike
Binciken wannan
takarda ba mai faɗi ba ne domin dalilan da suka sanya ƙasar
Gobir da Gobirawanta suka shahara kawai ya dosa. Abu na farko da na tunkara shi
ne, tattaro adabin bakan Bahaushe domin tattaro gutsattsarin sassan adabin baka
da dama da suka kururuta ƙasar Gobir
da Gobirawanta. Mataki na biyu shi ne rubutaccen adabin da ya hau doron burin
bincikena. Na yi ƙoƙarin
tattaunawa da Gobirawa da wasu daga cikin sarakunansu ko mutanensu da ke kiyaye
da tarihin ƙasarsu. Da yake wuƙa ba ta
wasa kanta da kanta na ɗan tunkari abokan zaman Gobirawa da
abokan yaƙe-yaƙensu na
jahiliyya domin yin tankaɗe da rairaya. Littattafan magabata
masu jihadi irin su Muhammadu Bello da Malam Abdullahi da Wazirin Sakkwato da
Abdulƙadir Almustafa sun ba da haske ga bagiren da
ake nazari. Haka kuma, akwai ayyuka da dama da su Gobirawa suka yi na tarihinsu
sun taimaka sosai. Manyan kundayen bincike na Abdullahi Rafi Augi (1982) da
Garba Nadama (1977) da Bello Alƙali (1968)
da wallafaffun ayyuka na Murray Last (1985) da su aka yi garkuwa. Na kakkaɓe wundin
wannan karatu da tattaunawa da abokan aikina da suka rubuta ƙudurinsu
na gabatar da takardun bincike na wannan taron. Na fa’idantu sosai da wannan
tattaunawar domin ita ta ba ni damar samar wa bincikena taken da ya dace da
tunanina.
Ra’in
Bincike
Na shimfiɗa zuciyar
wannan bincike bisa tunanin al’ada a kan abubuwan da adabi ke jewaɗi da su
game da Daular Gobir da Gobirawa. Tunanin mutanen Sudaniyya kan ƙasar
Gobir shi ne, Gobir gidan faɗa (yaƙi) ce. A
ko’in aka ga Bagobiri an ga wani jarumi, bahago ga abin da bai aminta ba, ɗan tawaye
ga kowane irin iko na kama karya da danniya da wariya. Bisa ga wannan hasashe
na rinjayen mutane (na bayan fage da masana masu bincike) da kuma abokan
gwagwarmayar Gobirawa da ke ganin ba haka abin yake ba. A nawa gani, Bahaushen ra’in da zan ɗora wannan
ɗan bincike
shi ne: ‘Ruwa na ƙasa sai ga wanda bai
tona ba.’ Manufa ita ce, a ba bincike dama ya yanke hukuncin abubuwan da aka
tsinta a bakunan mutane. Da mai ganin ruwa na ƙasa, da
mai musanta ba su a ƙasa, duk rijiya ce alƙalinsu.
Tambayoyin
Bincike
Ga alama, Augi (1982)
da Nadama (1977) da Alƙali (1968)
da Last (1985) da Usman (1974) ba su rage hakin susa ba ga mai neman tarihin
Gobirawa da ƙasarsu. Tattare da haka, wannan takarda ta
hango wani ɗan giɓin da ya
kyautu a ce an cike. Zance na farko shi ne, ina ne tushen kalmar ‘Gobir’? Wane
ne Bagobiri idan aka bi taliyon kalmar? Me ya kawo wa Gobirawa fice da ɗaukakar ƙasarsu
tun gabanin bayyanar Turawa da guguwar jihadin ƙarni na
sha tara (ƙn. 19)? Me ya sa har wannan ƙarni
na ashirin da ɗaya (ƙn.
21) kamar Jangwarzo ke karagar mulki? Me ya sa Daular Gobir ta fi kowace daula
tasiri ga daulolin ƙasar Sudaniyya? Idan
bincikena ya ci nasarar yi wa waɗannan tambayoyi shan ruwan tsuntsaye,
aka fahinci saƙon, to ta tabbata: ‘Ruwa na ƙasa
sai ga wanda bai tona ba.’
Warware
Ƙunshin Matashiya
Manufar ba a wane
bakin banza shi ne na duk wanda ya shahara akwai abin da ya taka ya yi wa tsara
fintinkau. Me ya sa Bahaushe ya ce, ‘Wane mutum in ji mutuwa!’ Bai ce, ‘Wane
mutuwa inji mutum’ ba. Domin ya san ko ba a gwada ba linzami ya fi bakin kaza.
Na yi amfani da kalmar ‘gurbi’ domin fito da matsayin Gobir da Gobirawa a
gurabun daulolin Sudaniyya. Farfajiyar Sudaniyya ita ce (Western Sudan) a da, wadda a yau West Africa/ sub-Saharan Africa za ta wakilta. Gabanin bayyanar
ikon Turawa a ƙasar Hausa da ƙasashen da
ke maƙwabtaka da ita duk a rubuce-rubucen Larabci
da adabin baka Sudan ko Sudaniyya ake kiransu. A rubuce-rubucen
masu jihadin ƙarni na goma sha tara (ƙn.
19) ana cewa ƙasar Biladil
Suudan wanda Turawa ke kira Western
Sudan ko Sudanic Africa. Marigayi
Makaɗa Aliyu Ɗandawo
ya tabbatar da wannan kalmar ta Sudaniyya a waƙarsa ta
Sarkin Kabin Argungu Sama’ila ɗan Yakubu da yake cewa:
Gindi: Shugaban
tahiya Sarkin Kabi mai Sudani
:Ila marin rugga ɗan Yakubu
sa gurhwani.
Ƙarni
tabbacin wannan akwai sarautar Sarkin Sudan a Sakkwato (wadda ke Wurno) akwai a
Kabi a Daular Kabi (wadda ke Lailaba). A Kwantagora sarauta ce. A Yawuri an yi
ta amma Kwantagora aka tura shi. A Katsina akwai Sarkin Sudan.
Daular
Gobir A Zamunan Daulolin Sudaniyya
Daular Gobir ba mutun
tsugune ba ce a cikin daulolin Sudaniyya a tarihance da sarauce da al’adance.
Ficen ta cikin daulolin zamunanta abin kulawa ne a wannan ɗan
bincike. Tarihin Daular Gobir yana da alaƙa da
rukunin daulolin da na kasa zuwa kashi biyu: Na farko su ne daulolin Sudaniyya
wajen ƙasar Hausa irin su ɗaular Nupe
(ta Nufawa) da Oyo (ta Yarbawa) da Azbin (ta Azbinawa) da Borgu (ta Bargawa) da
Borno (ta Kanuri) da Songhai (Shangawa da Dandawa da Kyangawa) da Mali (ta
Wangarawa) da Ghana (ta Asante) da Illo (ta Dandawa) da Fadan Gurma (ta Gurmawa
a Borkina Fasso). Daular Gobir ta yi zamunna ta waɗannan
daulolin kuma akwai zumuntan tarihi da al’adu da siyasar sarauta da za a samu
wuraren da suka haɗu da Gobir jefi-jefi.
Ɓangaren
daulolin Sudaniyya na biyu su ne daulolin da farfajiyar ƙasa
ɗaya mai
harshe da al’adu da siyasar sarauta da ta zamantakewa iri ɗaya.
Daulolin da ke da wannan sun haɗa da: Daular Kano da Daular Zamfara da
Daular Kabi da Daular Katsina da Daular Zazzau da Daular Yawuri. A talitalin
tarihin daulolin ƙasar Hausa, babu
labarin wani abu ‘Sokoto/Sakkwato’ sai dai Gobir. Bayan bayyanar Sakkwato a
matsayin cibiyar tsare-tsaren jihadi da ilmantarwa, aka samu Daula biyu: Daular
Sakkwato da Daular Gobir. Duk da haka, idan ana zancen harshe, da an ce
Sakkwatanci, ‘Gobirci’ ake nufi, domin cikin ƙasarsu
Sakkwato ta tsira. A tarihance da al’adance, idan ana zancen ƙasar
Hausa, Gobir ce ake bayani domin gabacinta a tarihance. Basakkwace na nufin
Bagobiri domin sai an yi shuka ake zancen tumu. Daulolin da muka ambata na
farko da ba cikin farfajiyar ƙasar Hausa
ba, duk abin da ya shafi ƙasar Hausa
da Hausawa a wajensu ƙasar Gobir
da Gobirawa ake zance domin gabaci a tarihi da al’adu[3].
Tushen
Kalmar Gobir
Binciken wannan
takarda da barhon al’ada ake feɗe shi. Duk da haka, masu Tarihi da
Imin Harshe da Walwala (Sociology) da Mutuntakar ɗan Adam
(Folklore) da Kimiyyar Al’ada (Anthropology) da Kimiyyar Siyasa (Political
Science) duk a kogi ɗaya suke su. Makaman kamun kifinsu da dabarun
kamun kifinsu kawai zai sha bamban, amma kifi iri ɗaya suke
kamowa. Wanda duk aka fi ƙwazon keta
gurbi da kurmundi dole a fi shi kamo manyan kifi ƙwangaggi.
A bitar ayyukan magabata masana Gobir da mutanenta babu silalen batu da ba su
bi ba domin tantance kalmar ‘Gobir’. Daga cikin abubuwan da suka shahara akwai:
1. Asalin
kalmar ‘Gubur’[4] wani gari
ne tsakanin Makka da Madina da suka yo hijira sunan garinsu ya bi su daga
‘Gubur’ zuwa ‘Gobir’ wasula kawai suka sassaɓa baƙaƙe
na nan tangam! A nahawun Larabci, harafin ‘wau’ (ﻭ) yana kusa da wasalin rufu’a (ﻭ )
don haka ‘Gu’ a Larabci na komawa ‘Go’ a Bahaushen lafazi domin a ajami ma ana
rubuta ta (ﻏﻮﺑﺮ). Sai dai wasalin rufu’a na gaba ga
harafin ‘b’ da ya ba da ‘bur’ ya koma ‘bir’ a Hausa, nan barafasa take. Da yake
wannan Balaraben ra’ayi ne, za mu ce ƙila ana
nashe wasulan kalmar ta koma ‘Gbr’ kamar yadda Masar/Misira ƙwararru
ke furta ta da rubuta ta ‘Msr’. Duk da haka, a cikin tarihi da tarihihin ƙasar
Makka da Madina ina aka samu ɗuriyar ‘Gubur’? akwai kufan bayanin
wannan garin a Saudiyya ta yanzu? A ina suka samu labarin farfajiyar Ƙasar
Gobir?
2. Ra’ayi na
biyu na cewa: Kalmar Gobir ko Gubur daga harshen Ƙibɗanci yake.
Ƙibɗawan Masar an ce,
wai, su suka haɓaka ƙasar
Gobir. An ce, ‘yan kasuwa ne da manoma suka tarar da ƙasar cike
da ma’adanin tagulla (Copper) a harshensu ‘Gubur’ ko ‘Gobir’ na nufin ‘tagulla’[5]. Ana ciro
tagullar wajajen Agadez/Takedda a yi fataucinta zuwa Zaghai da Katsina ta
hannun Wangarawa. Wannan tunanin ya manta da cewa, Ƙibɗawa yawo
suka zo kuma sun tarar da wasu mutane a wurin da suka zo. Su mutanen me suke
kiran kansu? Su ke hulɗa da tagulla ko Ƙibɗawa da
Azbinawa da Wangarawa? Me suke cewa ‘tagulla’ da harshensu? Tsakanin baƙo
da ɗan gari,
wa ya cancanci a karɓi sunan gari bakinsa? Wannan tunanin ya rage
wa Gobirawa tsawo. A gafarce ni, ban yarda da shi ba.
3. Ra’ayi na
uku na cewa: Ƙibɗawan Masar suka sama
wa babban birnin Gobir suna wato Birnin Lalle domin a harshensu Lalle (Lenna)
shi ne ‘Gobir’ a Hausa Lalle.[6] Idan haka
ne kuwa, an taras da Gobirawa da sunansu da sunan ƙasarsu,
domin da ciyayi/ciyawar lalle aka taras da su, ba zuwa aka yi da it aba. In
‘Gobir’ na nufin lalle, me ya sa ba a ce birnin Gobir ba ake ce Birnin Lalle?
Ko da Ƙibɗawan suka zo da
lalle, wa suka taras a wurin? Wannan ra’ayi na jin kunyar ɗaliban
ilimi ainun. Lallai dai abin ƙawar
duniya ne, Gobir da abinta aka gane ta. Wannan ra’ayi ya ƙarantar
da Gobir.
4. Ra’ayi na
huɗu na cewa:
Shahararren masani tarihi kuma ɗan yawon buɗe ido (ko
leƙen asiri) mai suna Ibn Batuta a tsakiyar ƙarni
na goma sha huɗu (ƙn,
14) da ya ratso ƙasar Azbin ya ce, ya
tarar da wata ƙasa wai ita ‘Kubar’[7]. Wannan
hasashen ya nuna Azbin daban Gobir daban, kuma sun yi zamuna ɗaya. Wa ya
rigayi wani? Bayanin bai kakkaɓe ƙurar ba.
Kalmar ‘Kubar’ matuƙar haka ya rubuta ta
to, ta saɓa wa
‘Goboru’ da ‘Gubur’ ko kusa ba ta yi kusa da ‘Lalle’ ba. Ga wa ya ji wannan
kalmar ta ‘Kubur’ ga Azbinawa (domin ƙasar Azbin
ya ratso, bai ce ya ratso ƙasar Gobir
ba)? Rashin samun haƙiƙanin
ina ya karɓo kalmar
ya sa ba za a shiga ɗaki da maganar ba. Idan za a yi adalci, za a
ce Ibn Batuta baƙon Gobirawa ne, domin
ko da iska ya zo ya tarar da Kaba na rawa.
Tankaɗe
Da Rairayar Kalmar Gobir
A tunanin al’ada, mai
ɗaki shi ya
san wurin da ɗakinsa ke
tarara. Masana adabi suka ƙara da
cewa, ko mai baibaya ya san wurin da ya taushe matararar ruwa. Daga cikin
abubuwan da ya kyautu a tsettsefe a riwayoyin kalmar ‘Gobir’ su ne:
1. Akwai
batun cewa Larabcin daga ‘Gubur’ yake sunan wani gari tsakanin Makka da Madina.
Wannan tunain na da ƙanshin addini da jawo
ɗaukakar
Larabawa a idon Musulmin Afirka. Da yawan al’ummomin Afirka suna laɓewa gare
shi domin samun karɓuwa da fice. Gobir ba ta buƙatar
wannan, don babu daular da ta yi mata mulkin mallaka kuma da addini aka tarar
da ita.
2. Ra’ayin
cewa daga harshen Ƙibɗawa ne na
kalmar tagulla da lalle ya kasa fito da harshen asali na waɗanda ake
kira Gobirawa. Ya manta da ɗan Adam ba ya walwala ba da harshe ba,
kuma masu tunani sun ce an tarar da wasu a ƙasar. Dole
a zargi ƙabilanci da wariyar fata a cikin ra’ayin.
3. Idan muka
nazarci kalmomin duka: ‘Gubur’ da ‘Gobir’ da ‘Kubar’ duk gaɓoɓi
biyu-biyu gare su. Tushen kalmomin kuwa daga ‘Gub’ da ‘Gob’ da ‘Kub’ ne, a
ginin kalmomin Hausa sun hau tsarin cikakkiyar gaɓa mai ‘baƙi
da wasali da baƙi’ (BWB). Masu
riwayar ba su ko ambaci Hausa daga tushen sunan ba. Bugu da ƙari,
a tsarin gaɓoɓin
kalmomin Hausa, dukkan kalmomin da rufaffiyar gaɓa suke a ƙarshe,
‘bur’ da ‘bir’ da ‘bar’. Idan za mu ɗora wannan hasashe
kan tasarifin kalmomin Hausa na saka kalmar ‘ba’ a farkon sunan ƙabila
da ‘wa’ a ƙarshen sunan, za mu samu:
Gubur Bagubur - Bagobiri
Bagubura - Bagobira
Guburrawa - Gobirawa
Gobir Bagobir(i) - Bagobiri
Bagobir(a) - Bagobira
Gobir(awa) - Gobirawa
Kubar Bakubar - Bagobiri
Bakubar - Bagobira
Kubar - Gobirawa
Wataƙila
ra’ayin ‘Gobir’ ya fi hawa mizanin Bahaushen ma’auni na lafazin kalmomin. A
nawa tunani, irin ɗaukakar da Gobir ta yi ba daga waje sunanta
ya fito ba, daga cikinsu ne suka ƙago abin
su da aka ga sun yi fice, kowa ya tofa albarkacin bakinsa.
Sake
Duban Kalmar Gobir A Farfajiyar Al’ada
Masu ruwaito asalin
Gobir da Gobirawa sun baro wani ɗan giɓi na
‘harshe’. Zancen Larabawan Makka da Madina da Ƙibɗawan
Misira da Larabawan Yemen da Turkawan Daular Ottoman ya kasa samun tasiri ga
harshen Gobirawa na tun fil azal. Har yanzu ba mu ji ɗuriyar waɗannan
harsuna ba ko a cikin tsohuwar Hausar ƙasar Gobir
da wasu daga cikin karuruwan harshenta. Ba Azbinawa ba ne, duk da zamantakewar
su da al’adunsu d harsunansu daban. Don wani abu baƙo kawai da
muka samu daga cikin fadar masarautar Gobir a bukukuwansu na salla, daga cikin
masu barka da salla za a fara gabatar da masu yi wa sarakunan Gobir kirari ɗaya bayan ɗaya daga
sarki na farko har ya zuwa mai ci. Bayan sun gama, sai wasu mutane biyu su zo,
su yi magana da baƙon harshe, ɗaya na
fassara da Hausa. Wannan salon suna kiransa Warkarci[8]. Gabatar
da masu yi wa sarakunan Gobir take da Hausa shi ne hujjar cewa, harshen Daular
Gobir da mutanenta Hausa ce. Samun wani/wasu baƙin harsuna
a Daular Gobir ba abin mamaki ba ne idan aka lura da daɗewarta da ƙarfinta
da faɗinta da
al’ummomin da ke maƙwabtaka da ita da
masu ziyararta da waɗanda ta ci da yaƙoƙinta.
In dai Warkaru ba harshen Azbin ba ne
da aka ce can Daular Gobir ta fara zama, to ina zaton surkullen zantawa da
iskoki ne na sirrin ƙasa a siyasance.
A tsarin al’adar
garuruwan ƙasar Hausa, sunayensu ba su rasa alaƙa
da mutanensu ko yanayin ƙasar ko
garin ko albarkatun ƙasar ko tsirrai ko
itace ko ma’adanan da ake samu ko gulabe da tsaunuka da dabbobi da ƙwari
da ke wurin. Mu tsura wa ƙasar Gobir
ido sosai mu dubi waɗannan misalai:
1. Sabon Birni: Ya nuna an baro
tsohon birni
2. Birnin
Lalle: Birni ne
da ke da ciyawar lalle
3. Unguwar
Lalle: Unguwa ce da aka
samo sunan daga lalle
4. Kalgo: Daga tsiron Kalgo
5. Kwaren
Gamba: Saboda hakin
Gamba
Aiki na kan masana da
manazarta da mu ɗalibai mu sake nazarin mazaunin Gobirawa na
farko domin mu nazarci yanayin wurin. Haka kuma, mu ɗan yi yunƙurin
gano su Gobirawan farko da aka tarar yaya suke kiran kansu? Ko da ma sunanta
‘Goobir’ masu sauraron suna da ba ‘yan asali ba ke furta ta daban-daban? Anya
ba wajen rubuta ta ne ake samun matsala ba daga ajamin sunan ko rubutun Turawan
farko? Me zai hana mu sake bitar waɗannan ‘yan
hasashe-hasashe mu ga ko akwai abin cewa:
1. Gobarau: Masallacin Gobarau
na Katsina ficen da ya yi duniyar tarihin Sudaniyya kuma da wannan suna
‘Gobarau’. Daɗewar
Musulunci a Daular Gobir da shiga da ficen baƙi cikinta
abin duba ne. Wannan na buƙatar a
dubi tarihin Gobarau da kafuwar Daular Gobir. A sake duba wasalin /u/ da
harafin /w/ ‘yan tagwaye ne, daga nannage n /u/ aka samu /w/, don haka Turawa
ke ce da harafin ‘double u’ wai ‘u’
gida biyu. Ke nan da ‘raw’ da ‘rau’ Hasan da Husaini ne. Gobirawa – Gobarau –
Gobarawa.
2. Goriba/Goruba: Farfajiyar Azbin da
Kabi da Katsina da Gobir marayar icen ‘Goriba’ ce. Yanayin ƙasar
na yi wa icen daidai. Idan da tabbacin itacen Goruba bargaja a wuraren zamansu
na farko ƙila a ce daga ‘Goriba’ a sami ‘Goribu’ –
Goribau – Goribawa – Gobirawa.
3. Gobara: A mahangar al’ada,
mutum/wani abu na tashi da sunan asali a tsakiyar rayuwa a ƙaga
masa wani suna ga abin da aka shaida gare shi. A al’adance, rinjayar da wuta za
ta yi wa mahashinta sai ya nemo agaji a taimake shi a kashe ta, shi ake ce wa
‘gobara’. Wutar gobara wani yaƙi ne da
gudan gari dole ya tashi-tsaye. Ga al’ada, idan Ƙudahi ko
Jan-Kiyashi ko Sunge ko Cinnaka suka yi tururuwa da yawa suka fito rami, akan
ce sun yi ‘gobara’. Bagobiri ga yaƙi,
‘gobara’ ne, duk ƙasar da suka kai wa
hari sai mazajenta sun nemi agajin dugadugansu. Idan aka kai musu hari, ƙwai
da ƙwarƙwatansu ke
fitowa, a mutum har liman.
Ƙoƙarin
laƙa wa Gobir sunan da ba na harshen kakanninta
ba rage mata lamba ne, a sake lale. Anya! Ƙoƙarce-ƙoƙarcen
danganta asalin Gobirawa da wasu baƙin ƙabilu
irin su Ƙibɗawa da Turkawa da
Fir’auna babu hasada a ciki? Kada a manta yaƙi kashi
biyu yake, yaƙin takobi da na alƙalami.
Daular
Gobir da Gobirawa a Farfajiyar Daulolin Sudaniyya
Daular Gobir a
fuskokin daulolin Sudaniyya kamar madubi take kuma ita ce daular da ta samu
suna ɗaya
gawurtacce da duniyar Sudaniyya ta yi canjaras a kansa. Ga ɗan misali
da za mu ga irin nauyin Gobir cikin adabinmu:
1. Kano: Jalla babbar Hausa, gari ba Kano ba
dajin Allah, ko
Kano ba
gari ba dajin Allah. Duk da wannan kirari na yawan ƙasarta, Ɗantanoma
mawaƙin Sarkin Kabi Sama ya ce:
Jagora: An ce ba a wa Kano takakaka
:Sama ya
tattake ta
:Don mun zo
Kano da dambun masu
:Ba mu samo
gaba ba.
2.
Katsina: Bukkar kara
3. Kabi/Argungu: Birnin kara da gambun ƙarfe
Na Kanta
ba ku da raggo
4. Sakkwato: Birnin Shehu, ta Bello mai da ƙasari
zuma
5.
Yawuri:
In ka san Yawuri ka san
geshe?
6.
Zamfara: Zurfin ciki / Gusau ta Sambo Dandin
Hausa
7.
Zazzau:
A taƙaitace,
a tsarin kowace daula, kowace ƙasa akwai
take da kirari. A can da, da kiɗa da rawa ake yin taken da arashi da
kirari ana yi wa abokan hamayya habaici. Da aka ci gaba ne aka bai wa sojoji da
‘yan sanda busa bigala da atisayen
barazanan tuna baya. Wanda duk kakanninsa ba su kare ɗiyaucinsu
ba, ba ya da wani taken da zai gaya wa duniyar zamaninsa. Daular Gobir a nan ta
ci zarar sauran dauloli takarorinta. Da an ambaci Gobir da yaƙi
za a yi mata kirari
·
Gobir ta Bawa gidan faɗa.
·
Gobir ta Bawa kowa Sarki.
An ce,
rawar atisayen dakaru Gobir a fagen daga shi ne[9]:
:Ƙashin
gwuiwan kura
:Ba lasan karnai ba
:A ba manya fili
:Ba don Allah na ba
:Ina mutuwa tayyi! Ina
mutuwa tayyi!
:Ta sheƙo
ga ‘ya’ya (tsoho)
Zaruntakar Gobirawa
ta yi kusa da ta Larabawa in ba ta yi daidai ba. An ce, Khalid bn Walid in sun
je fagen jihadi sukan gaya wa abokan karawa cewa: “Ga waɗanda ke buƙatar
mutuwa fiye da yadda suke son rayuwarku”.[10] Tirƙashi,
maganin maƙi gudu ban kashi!
Mazakutar Gobirawa a
kowane fagen nuna bajinta suka shiga sai sun yi fice kuma da jarumtaka ake
rarrabe Bagobirin asali da Bagobirin rantsuwa. Dubi yadda makaɗa Ɗan’anace
ke wasa wani Bagobiri a fagen dambe:
Jagora: Yaƙi sabon
Bagobiri
:Mai kayan faɗa
:In nig ga mutum da jan
ido
:Tsoro nai nikai
Makaɗa Narambaɗa Tubali,
makaɗin Daular
Sakkwato da ya yi wa Sarkin Gobir Salihu waƙa ga
gindin da ya ɗora ta a
kai:
Gindi: Ya buwai maza Salihu
:Ko yanzu a bar wargi
:Ba su ima Ɗan’inna
:Halin Ummaru na yay yi
Jagora: Kai
a Ummaru yau
Yara: Kai a ɗan Adata
Jangwarzo
Jagora: Batun
da kas sani na
:Shi na za ni tusa ma
:Da gabas da yamma
Yara: Shawai bai zan done ga kowa ba
Jagora: Nan
ƙasag ga kog gwada wargi
Yara: Ummaru ya bi sai
Abin mamaki, hatta a
fagen siyasar zamani za a yabi Bagobiri sai an tuzgo da famar yaƙi
da suka gada daga kakanni. Sani Aliyu Ɗandawo da
ya yi wa Gwamna Attahiru Bafarawa waƙa ga
gindin da ya ɗora ta:
Jagora: Dogo bari in ma kiɗin nan na
yaƙi
:Attahiru ya yi kokuwa
ya yi kaye.
Wani makaɗin fadar
Sabon Birni ya fito da ficen Gobirawa cikin waƙarsa kamar
haka:
Jagora: Gobirawa kun sha kunun baƙar
zuciya
Yara: Nan gidan duniya babu in da ba a
san ku ba.
A masarautar Gobir,
da duk wurin da Bagobiri yake a duniya, yana bugun gaba da Sarki Malam Bawa
wanda aka fi sani da Jangwarzo. Daga cikin malaman zamaninsa wani malami ya
rubuta waƙar yabon Bawa Jangwarzo (1790) yana cewa:
Ba da razana kigon tama
Ɗan Alasan
mai tambari
Ba da razana ƙyauren
gari
Bawa kai na Magajin Gari
……………………………
Ba batun yaƙi
munka zo ba
Gaisuwar mutuwa munka zo
Da batun yaƙi
munka zo
Wurno ba ta yini ko ta
kwan
Shiki da dole tawayen
gari
Ƙanƙanan
kajinmu na
Wa ɗan Gudale
wa ɗan Tubali
Manya-manyan kajinka na
Kar ka tam musu sai ran
buki
Wannan waƙar
rubutacciya ce bisa ga tsarin gwauruwar waƙa (‘yar ƙwar
ɗaya) kuma
kwamacala ba da tsayayyen amsa amo ba. Duk yabon da aka yi wa Sarki Malam Bawa
Jangwarzo kan yaƙi ne da fama.
Kar
Ta San Kar
A da, gabanin
bayyanar hasken saukakkin addinai, ƙarfin
kowace daula ya danganta ga irin ƙarfin
sojanta da tanadinta na tsaro. Gobir da Gobirawa sun yi sunan yaƙi
ainun, sai dai abin kula shi ne, mayaƙi ba dole
kowane karo shi ke yin nasara ba. Yadda Hausawa ke cewa, ‘Ba a san maci tuwo ba
sai miya ta ƙare’, ba a san gwarzo ga yaƙi
ba sai an ci shi ya mayar da fansa ko ya ci nasara ko ya sake faɗuwa. Ga
al’adar Gobirawa, cin su da yaƙi ba abin
bugun gaba ba ne, domin su da yaƙi tobasai
ne ƙuƙe-na-ƙuƙe
sai abokin yaƙi ya gaji ya mayar da yaƙin
wasa.[11]
Daular Gobir ta kara
da Katsina ta ci an ci ta. Ta kara da Kano da Zazzau da Zamfarawa ta ci an ci
ta. Ta shigo Borno da Rano da Haɗijiya yaƙin zube ba
ni ƙwarya. Ita da Daular Sakkwato takobi bai taɓa kwana
kube ba. Ta yi arangama da Azbinawa har suka sauya mazauninsu suka dawo wurin
da suke yanzu. Da Adar da Zabarma ba ta bari suka huta ba sai da ta ɓatar musu
da lisafi. Gobir ta taya Daular Nupe ta ci zarra. Ta darzaza Oyo dole Yarbawa
suka zaɓi
tobasantaka. Tattare da tsananin tsaron Bargawa, Gobir ba ta bar su ba sai da
aka ƙwama ta girgiza su. Daular Songhai ta Askiya
sun kauru da juna, Fulanin da ke Fadan Gurma (Gurmawa) sai da Gobir ta firgita
su. Daular Mali ta Wangarawa, Gobir na da tarihin yaƙi da su na
bisa kan mai uwa da wabi. Babu wata daula daga cikin daulolin Sudaniyya da ba
ta san da Gobir da Gobirawa ba a fagen luguden takubba da ruwan masu ba. Waɗannan yaƙe-yaƙe
da babu wata daula daga cikin daulolin Sudaniyya da ta yi kama da irinsu. Kuma
ta tsayu da ƙafafunta, su suka bai wa Gobir da Gobirawa
fitaccen suna da babu mai irinsa.[12]
Fice da dabarun yaƙin
Gobir ya sa suka dinga sassauya cibiyoyin daular mulkinsu. Daga cikin cibiyoyin
da aka yi akwai, Birnin Lalle da Tsibiri da Sabon Birni da Alkalawa da Birnin
Magale da wani gari kusa da Gidan Rumji na cikin Jamhuriyyar Nijar, an ce
kangonsa na nan.[13] Wannan
dawara da kai da kawo ya ba Gobirawa damar barbazuwa cikin duniyar Sudaniyya,
har ya kasance babu wata daula daga cikin daulolin Sudaniyya da babu Bagobiri a
ciki. Abin ban sha’awa, ba a san su ‘yan gudun hijira ba, sai dai a ce, ja da
baya ga rago ba tsoro ba ne, duk cikin shirin yaƙi ne. A
cikin kowace daula Gobirawa suka shiga baƙunci an
san kar ta san kar.
Hasken
Gobir Da Gobirawa A Masarautun Ƙasar Hausa
Bayan da yaƙe-yaƙen
jihadi suka lafa, Bature ya yi ɗan zamaninsa ya wuce. Ƙasa
ta koma hannun masu abu, kowa ya koma ƙasa da
aiki ƙoƙarin gina
abin da aka rusa da farfaɗo da abubuwan da suka salwanta. Kowace
daula masarautunta suka himmatu da abin da suka himmatu a kansa. Tasirin yaƙe-yaƙen
da Gobirawa suka yi, da dabarun tsaronsu da tattalin arziki da siyasar mulki ta
ci gaba da naso manyan daulolin ƙasar
Hausa. Bazuwar Gobirawa da kafuwar garuruwansu da tsabbacewarsu nesa ga waɗanda ba su
yarda da su ba ya haifar da wani sabon salon a tsarin sarautun daulolinmu.[14]
Rushewar Alkalawa da
gugwar jihadi da ta raba masarautar Gobir kashi biyu Sarkin Gobir na Sabon
Birni (da ya miƙa wuya) da Sarkin
Gobir na Tsibiri (da ya zaɓi ‘yanci).[15] Garuruwan
Gobirawa, mutanensu suna nan tangam kamar komai bai faru ba. Don haka, dole aka
bar su da sunansu da sarautunsu. Dubi waɗannan
sarautun don tabbatarwa:
i.
Sarkin Gobir Na Isa
ii.
Sarkin Gobir Na Gwadabawa
iii.
Sarkin Gobir Na Goronyo
iv.
Sarkin Gobir Na Kalgo (Ƙasar
Gwandu)
v.
Sarkin Gobir Na Bunguɗu
vi.
Sarkin Gobir Na Lailaba (Ƙasar
Kabi)
vii.
Sarkin Gobir Na Kwantagora
viii.
Sarkin Gobir Na Yawuri (a Kwantagora)
Waɗannan
sarautu ba ƙanana ba ne a ƙasashen da
suke. Abin ban sha’awa duk wani ɗan sarautar Sakkwato da Kabi da Gwandu
zai so a ba shi sarautar Sarkin Gobir domin wani matakin ci gaba a tsarin
masarautunsu.[16] Abin nufi
a nan shi ne:
i.
Mai sarautar sarkin Gobir Na Isa, sarautar
Sarkin Musulmi yake jira.[17]
ii.
Mai sarautar Sarkin Gobir Na Gwadabawa,
sarautar Sarkin Musulmi yake jira. Sarakuna biyu da suka fito daga can suka yi
sarautar Sarkin Musulmi.[18]
iii.
Mai sarautar Sarkin Gobir Na Kalgo, shi ake
ba Sarkin Gwandu in ta faɗi. Mafi yawan sarakunan Gwandu sai da
suka yi Sarkin Gobir Na Kalgo.[19]
iv.
Sarakunan Kabi uku suka yi sarautar Sarkin
Gobir Na Lailaba kuma duk sun yi Sarkin Kabin Argungu.[20]
Gobir
Fitilar Addinan Farfajiyar Sudaniyya
Tsayin dakan da Gobir
ta yi na ƙin miƙa wuya ga
mulkin gadon-na-gajeka da sunan addini ya sa wasu na bayan fage ke yi mata
kallon Maguzanci.[21] Ko shakka
babu, Gobir ta yi fice a kan addinan gargajiya na bori da camfi da ‘yan
tsafe-tsafen kare kai da kaya.[22] Mantuwar
da ake yi ita ce, waɗannan abubuwa sun wanzu tun gabanin saukakkin
addinai a Sudaniyya. Babu al’ummar da ba Bamuguza ba gabanin saukakkin addinai.
Don haka, kowace al’umma da irin nata bori da tsafe-tsafe.[23] Gobir ta
shahara a nan, domin ga al’ada komai Gobirawa suka tunkara gadan-gadan suke ba
su san ido ga kifi ido ga bado ba. Hidimar Iskoki na bori daga Masar da Morocco
da Tunis da Alges da Libya suka kwararo Gobir ba Gobir ta ƙago
su ba.[24]
Kasancewar Daular Gobir daɗaɗɗiya ta yi
fice da zarra cikin sha’anin bori a Sudaniyya.[25]
Saukakkin addinai na
Nasara da na Musulunci a Gobir suka fara yada zango. Gabanin jihadi babu daular
da ta fi Daular Gobir malamai a farfajiyar Sudaniyya. Masu jihadi manya daga
cikinsu suna da malamai Gobirawa kuma wasunsu ƙasar Gobir
suka yi karatu.[26] Mujaddadi
ya tabbar da akwai malamai masanan gaske Ƙasar Gobir
kuma Gobirawa. An ce, Mujaddadi na matashi ya je fadar Gobir ya yi wa malamansu
nasiha, suka yi masa tambaya ɗaya, suka ba shi shekara ɗaya, ya je
ya yi karatu ya gano bayaninta, ya dawo ya faɗa.[27] Ya yawace
ƙasa gaba ɗaya ya
rasa bayani. Yadda al’amarin yake shi ne, akwai wani bawan Allah mata-maza a
Birnin Alkalawa san da yake mace sunansa Sahura,
lokacin da yake namji sunansa Ummaru,
ya rasu a mulkin Sarkin Gobir Babaji. Ga tambayar da malaman Gobirawa suka yi
masa:
Da yana
mace Sahura ya yi aure ya haifi
‘ya’ya biyu, aka gane mata-maza ne aka sake shi. Ya je ya yi shigan maza Ummaru ya auri mata suka haifi ‘ya’ya
uku. Aka gane shi, aka sake shi. Ya je ya yi mafarkin maniyinsa ya ɗiga a
farjinsa ya haifi ɗa ɗaya. Sai ɗiyansa su
shida suka taru/rayu. Ya rasu ya bar dukiya mai yawa, yaya za a raba musu gado?
Abin ban sha’awa,
Sarkin Gobir Babari ya tura masana daga Alkalawa zuwa Tunis da Tarabulus da
Misra domin tuntuɓa.[28] Wa zai
musanta kasancewar masu wannan tambayar fitattun masana na ƙin
ƙarawa? Me ya sa suka yi tambaya ga fannin
gado? Ashe tuni Gobirawa ke da hulɗa da duniyar ilmin
Musulunci tun ba a taɓa mafalkin jihadi ƙasar
Hausa ba. Danƙari! Lallai Gobir mai hannu duka dama ce. Duk
wani mai ƙoƙarin kushe
Daular Gobir ko Gobirawa ta fuskar addini bai san ‘Ba a wane bakin banza ba’. Gaya masa ya sa himma, ruwa na ƙasa
sai ga wanda bai tona ba. A iya sanin Gobirawa Daularsu ta Musulunci ce, kuma
Musulmi ne Sarkinsu gaba da baya, kurakurai kuwa ba hujja ce ta kore addini ga
wanda ya miƙa wuya ba.[29] Da
Mujaddadi ya dawo ya ba su gari kan tambayar da suka yi masa, suka yi masa
fashin baƙinta dalla-dalla.[30] A tuna ba
tambayar ƙure ba ce, ba ta raini ba, domin abin ya
wakana a haƙiƙa ba ƙire
ba ne.[31]
Sakamakon
Bincike
Idan Bahaushe ya ce,
‘Ba a wane bakin banza’, a bi shi a
hankali a ga wane ne wanen da yake zance a kai? Da duk suna ya yi fice, akwai
wata ɗaukaka
tare da shi. Gobirawa sun samu ɗaukaka mai yawa a farfajiyar
Sudaniyya; an yi zamanin da ba wasu sai su, kuma ba sa magana a kaɗa kai.
Jihadin ƙarni na goma sha tara ya tarwatsa babbar
cibiyarsu Alkalawa. Mulkin Turawan Ingila ya zo ya sake girgiza su. Duk wannan
bai goge sunan Gobir ba, bai rage wa Gobirawa tsawo ba saboda irin salon
zamantakewarsu na a share jini a koma wasa. Ga ɗan
hasashen da wannan takarda ta leƙo:
1. Babu
daular da ta yi faɗi da yawa da ƙasaita a
daulolin Sudaniyya irin Daular Gobir.
2. Gobirawa
tantagaryar Hausawa ne duk wani yunƙuri na
samo musu suna a wajen daularsu, a bi shi a hankali ba a rasa bi-ta-da-ƙulli
a ciki.
3. Ci gaban
dukkanin ƙasar Sudaniyya Gobir ne tushensa ta fuskar
siyasa da tsaro da addini da wayewa domin ita ta fara yi wa baƙin
Sudaniyya masauki. Sarrafa bindiga da murƙushe juyin
mulki da tsaro, gare su aka koya.[32]
4. Gobir na
buƙatar sabon bincike don a inganta tarihinta, a
daidaita shi ya shiga cikin sahun fitattun daulolin duiya da ake darussansu a
tarihin duniya. Wannan na buƙatar
gidauniya ta musamman mai ofishi a masarautun Gobir.[33]
5. Ga
dukkanin abubuwan da suka bayyana Gobir ba ta aminta da tarihin Bayajidda ba.
6. Na fihimci
cewa babu wai, Gobirawa su suka kawo dabarun yaƙi a
farfajiyar Sudaniyya, kamar yaƙin taron dangi da Turawa ke bugun
gaba da shi; da salon a mutu har liman
wanda Larabawa ke bugun gaba da shi; da sasasantawa
ta fuskar auratayya wanda Fulani suka ara daga gare su. Don tabbatar da
wannan iƙirari, Saular Sakkwato ta kasha wa Daular
Gobir mutane ɗari (100)
da ta turo su taimaki Sarki Sama na Daular Kabi yaƙi (da su
Fulani). Aka kashe su a ganin Natsini, Gobir ta sake turo wasu nan da nan ƙarƙashin
Ɗangaladima Ali, suka kuma ci nasarar yaƙin
(Bagaye, 2018).
Naɗewa
Ban ce na ce komai
ba, amma na san waɗanda suka ce wani abu, na ce wani abu a kan
maganganunsu. Tattara tarihin al’umma ba aikin rukunin masana ɗaya ba ne,
taron dangi ake yi masa. Wanda ke tsinkayar Gobir da nisa, dubin tsoro ya yi
mata. Wanda ke kallonta kusa, bai yi mata duban natsuwa ba. Wanda ke jin
ka-ce-na-ce a kanta, bai fahimce ta ba, sai ya yi nutso cikin ayyukan da aka yi
a kanta na ilmi. Rubuce-rubucen da aka yi kan Gobir cikin Faransanci da
Ingilishi da Larabci ba su shiga sosai a makarantun ilmi na addini da boko ba.[34] Abin ban
sha’awa, ga Gobirawa da suturarsu da tsagarsu ta gado da sunayen kakanninsu har
yanzu ba su wofintar da su ba. Daulolin da Gobir ta ci yaƙi
ba su taɓa tunanin
mai da gami ba, waɗanda suka ci galaba a kanta har gobe ba su
son a yi zancen fansa, kaico!
Jagora: Ashe kura ko ta yi
kwance
:Ko an yanke
ba ta motsi
:Ɗan
akuya bai ƙetararta
:Yana aza
kura lahiya take
:Ba shi isa
kusa ba shi yarda
Manazarta
AbdulMalik,
M. (1966) Zuwan Turawa a Nijeriya ta
Arewa. Zaria: NNPC.
Adamu, M.
(1978) Hausa Factor in West African
History. Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Alƙali,
B. (1968) “Hausa Community in Crisis Kebbi in the 19th Century” MA
thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.
Augi, A.
(1979) “Migration of the Gobirawa: A Reconsideration”, Paper Presented at
Postgraduate Seminar Department of History, Zaria: Ahmadu Bello University.
Augi, A.
R. (1984) “The Gobir Factor in the Social and Political History of the Rima
Basin” (c. 1650 to 1808), PhD thesis, Zaria: Ahmadu Bellio University Vol. I.
Boyd, J.
(1982) “The Contribution of Nana Asma’u Fodio to the Jihadist Moɓement of
Shehu Usman Dan Fodio from 1820-1865”, MPhil thesis. London: Polytechnic of
North London.
Bunza, A.
M. (2009) Narambaɗa. Lagos:
Ibrash.
Bunza, A.
M. (2017) Dabarun Bincike A Nazarin
Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa. Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Gagare, B.
(1982) Ƙarshen Daular Alƙalawa. Lagos: Ma’aikatar
Al’adun Gargajiya Ta Tarayya.
Gatawa, M.
(1995) “Migration, Settlement and Integration: The Tuareg of Sabon Birni Local
Goɓernment
Area”, BA Project, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniersity.
Gobir, A.
S. H. (1982) Kunne Ya Girmi Kaka
Ingantaccen Tarihin Hausa. Presented to Alhaji Shehu Aliyu Shagari The
President of the Federal Republic of Nigeria on the Commemorating the First
Presidential Ɓisit to Sabon Birni on Monday 26th
July 1982. By Sarkin Gobir Alhaji Muhammadu Bawa.
Gobir, H.
and Boyd, J. (1981) “Salla in Sabon Birni in Gobir Customs and Tradition” in Zaruma Cultural Magazine, Sokoto.
Hama, B.
(1967) Histoire du Gobir at de Sokoto.
Niamey.
Hamdan, S.
& King, N. (1975) Ibn Batuta in Black
Africa. London.
Hisket, M.
(1975) History of Hausa Islamic Verse.
London.
Last, M.
(1985) “The Early Kingdoms of the Nigerian Saɓanna”in,
J.F.A. Ajayi & Micheal Crowder, Vol. One.
Maniya, M.
S. (2009) Tarihin Sahabban Shehu.
Sokoto: Al-Ameen Printing.
Meeek C.
K. (1971) The Northern Tribes of Nigeria.
London: Clarke, Doble and Brendon Ltd.
Miles, W.
F. S. (1994) Hausaland Diɓided
Colonialism and Independence in Nigeria and Niger. Cornell: University
Press.
Nadama, G.
(1977) “The Rise and Collapse of a Hausa State: A Social and Political History
of Zamfara”, PhD thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.
Richardson,
J. Travels in the Great Desert of Sahara
in the years 1845 and 1846, London: Vol. 11.
Sami, S. Traditional Titles in Northern Nigeria.
Smaldone,
J. P. (1977) Warfare in the Sokoto
Caliphate Historical and Social Perspectives. Cambridge: University Press.
Tarihin Daular Gobir
Tremearne,
M. A. J. N. (1914) The Ban of Bori Demons
and Demon-Dance in West and North Africa. London: Health Cranton and
Ouseley, Ltd.
Usman, Y.
B. (1974) The Transformation of Katsina.
Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Waɗanda Aka Tattauna Da Su
1. Professor
Murray Last, University College, London.
2. Malam
Yakubu Bagaye, BA, (Protocol) Sakataren Hulɗa da
Jama’a na Masarautar Kabi.
3. Dr. Yakubu
Aliyu Gobir, PhD, Dept. of Nig. Lang. UDUS.
4. Dr. Aliyu
Uba, PhD, Federal College of Education, Ondo.
5. Malal
Sayyadi Ruma, MA, Goɓernment House, Katsina.
6. Malam
Bature Dunkushi, (Teacher) Malamin Makaranta/ Ɗan
Sarauta.
7. Malam
Idris Geza, (Teacher) Malamin Makaranta/ Ɗan
Sarautar Geza, (Jikan Sarkin Shiko Manu).
8. Professor
Babajo, Umaru Musa ‘Yar’adua University, Katsina.
9. Malam
Umaru Ango, Gidan Tarihin, Sakkwato.
[1] Shahara
a duniyar mutane kamar Zulƙarnaini
da Ƙaruna
da Namarudu.
[2] Daga
cikin Iskoki akwai Ifritu da Dandanguna, uban Aljan da Hajon Ruwa.
[3] Daular
Gobir tana gaban Kabi da Katsina ta riga dauloli da yawa wayewar kai a duniya.
[4] A
dubi Augi, Migration of Gobirawa: A Reconsideration, paper ABU Zaria, 1979.
[5] A
dubi Last, The Early Kingdoms of the Nigerian Saɓanna, cikin J.F.A. Ajayi and M.
Crowder, History of West Africa, shafi na 11.
[6] Ra’ayin
Murray Last ne da na tattauna da shi ranar Talata, July 3, 2018 ta kibɗau ya turo mini da saƙon a rubuce.
[7] Hamdan,
S. Ibn Batuta in Black Africa, 1975.
[8] A
dubi Gobir, H. da Boyd, J. “Salla in Sabon Birni in Gobir Customs and Tradition”,
in Zaruma Magazine, 1981 shafi na 26.
[9] Cikin
waƙe-waƙen yaran ƙasar Gobir na dandali.
[10] A
dubi Hitti, P. K. History of the Arabs. London.
[11] Da
suka ga an buwaye su Katsina suka ce a mazaya a mayar da iri gida. Cikin
daulolin ƙasar
Hausa kowace na wasan tobasantaka da Gobir kan yaƙi.
[12] A
al’adance ko raki Bagobiri ya yi a kan ce assha! Baka gada ba ko ka ɓata iri.
[13] Kangon
kufan garin ke wurin bai ɓace ba, a dubi Tarihin
Daular Gobir.
[14] A
ko’ina suka yi gari suna son a naɗa
musu Sarkinsu. A tsakiyar wata ƙasa
za ka ga an ce Sarkin Gobir wane.
[15] Hatta
da su na Sabon Birni na miƙa
wuya suka yi ga Fulani ba ana dai zaman ‘yan marina.
[16] Ya
kasance wata al’ada cewa gabanin ka yi babbar Sarauta an so a ce ka yi Sarkin
Gobir a wuraren.
[17] Sarkin
Gobir Amadu da Narambaɗa ya yi wa kiɗa, ya yi takarar Sarkin
Musulmi tare da Sarkin Musulmi Abubakar na III bayan rasuwar Hassan Ɗan Mu’azu.
[18] A
Gwadabawa an yi Sarkin Gobir bakwai, biyu daga ciki suka yi Sarkin Musulmi wato
Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare (1915-1924) da Sarkin Musulmi Muhammadu
Tambari (1924-1931). An yi Sarkin Gobir Ahmadu (1924-1928), Sarkin Gobir
Muhammadu Adiyya (1929-1931), Sarkin Gobir Abdurahman Jatau (1931-1968), Sarkin
Gobir Muhammadu Bello (1968-1974), Sarkin Gobir Muhammadu Zayyana (1974-2013),
Sarkin Gobir Lawal Muhammadu Zayyana (2014-yau).
[19] Sarkin
Gwandu Haruna da Sarkin Gwandu Jakolo duk sun yi Sarautar Sarkin Gobir Na Kalgo.
[20] Muhammadun
Sama da Sarkin Kabi Muhammadu Mera duk sun yi Sarautar Sarkin Gobir.
[21] A
Sakkwato da Bafulatani ya ga Bagobiri sai ya ce: “Jikan Inna uwar bori.”
[22] Babu
wata daula da ta kuɓuta ga haka, Mujaddadi
ya ambaci waɗannan al’adu cikin Nurul
Albabi
da Wasiiƙatul Ikhwani da Bayaanil
Bidi’as Shaiɗaniyya.
[23] Zuru
akwai Magiro, Fulani na da nasu, Yawurawa na da, ga su nan dai.
[24] A
sabon binciken tsarin sunayen Iskoki da yadda ake yi musu hidima daga ƙasashen Larabawa suka
shigo ƙasar
Hausa. Musulunci ya yi naso ciki sosai.
[25] Da
Argugu da Gobir da Zamfara da Katsina bori ya bazu sosai da ƙyar Musulunci ya ci
nasara a kansa.
[26] Mujaddadi
Ɗanfodiyo
a gidan Sarautar Gobir ya yi karantarwa.
[27] A
lokacin sun ga ya yi musu ƙarami
ga shiga sha’anin manyan malamai.
[28] A
duba cikin Ƙarshen
Alewa Ƙasa. Shafi na 7.
[29] Ba
a kafirta mai salla domin aikata saɓo.
[30] A
cewar su: ɗiya da ya haifa yana
mace a ba su rabon mata, ɗiyan da ya haifa yana
namiji a ba su rabon maza, wanda ya haifa da kansa a ba shi rabon mace da
namiji.
[31] Abin
ya faru don haka ba son su ƙure
shi suke yi ba, so dai ake a gaya masa ya taka sannu da karatu.
[32] Gobir
ta taɓa Sarki Kututturu,
Sarkin ya mutu suka ƙi
su faɗa don kar yaƙi ya ci su. Aka ci gaba
da yaƙi
ba Sarki sai Kututturu.
[33] Sashen
Tarihi da Masarautar Gobir su kula.
[34] Siyasar
da ke tsakanin Daular Sakkwato da ta Gobir ba ya rasa hannu a ciki.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.