“Katsena boasts itself to be the seat of learning of Hausaland. It is probably a more ancient town than even Kano, and is built in the same style. I explained to the king (Sarki Abubakar) the conditions of British suzerainty, which he accepted with apparent cordiality" - Lord Lugard (1903).
Zawan Turawa
Katsina Da Irin Tarbar Da Akayi Masu A 1903
Yusuf Lawal Kankia
Makaman Kankiya
(Yulaks Ky)
Turawa sun zo Katsina kamar yadda suka je manyan garuruwan
Arewa da Ƙasar
Hausa. A wasu garuruwan an ja daga, a wasu garuruwan kuma komi ya tahi kodai
salun alin ko kuma bisa tilastawa.
Mu a Katsina saboda basira da kuma wayewa tun a wancan
lokacin ba'a yarda aka sakan ma Bature fuskar maida mutane bayi ba ko kuma ya
mulke su da tsiya. Sannan kuma ba'a yi faÉ—a
dashi ba sai dai akayi mashi karimci aka kuma nuna mashi gogewa da ilimi wadda
tasa yaji dadi kuma ya saki jiki sannan har ma ya saki ragamar mulkin ba kamar
sauran wurare ba.
Lokacin da Gwamna
Lugga da Jama'ar shi su Sittin suka baro Sakkwato zuwa Birnin Katsina sai
Sarkin Katsina Abubakar ya shirya masu tarba ta karimci. Wannan yasa basu yi
amfani da wani makami ba kan kowa. Sarkin Katsina ya tarbi Gwamna Lugga Watau
Governor, Lord Frederick Luggard tare da tawagar shi. A wannan hoto (pic1) za'a
iya ganin daga Hagu zuwa Dama: Governor Lugga, Sarkin Katsina Abubakar, Kauran
Katsina Isiyaku, Galadiman Katsina Sallau, 'YanÉ—akan
Katsina Mani, Marusan Katsina Altine. A layin baya kuma akwai: Durbin Katsina
Muhammadu Dikko (Kafin ya zama Sarkin Katsina) sai, Yariman Katsina Abdulkadir,
da Baturen Yandoka da sauran wasu.
Shi dai Gwamna Lugga ya shigo Katsina ne ta Kofar da ake
kira Kofar YanÉ—aka
(pic2) a ranar 28 ga watan Maris 1903. Wannan ita ce ranar da Turawan Ingilishi
suka amshi Katsina.
Daga nan kuma Sarki Abubakar yasa aka kai su masafki. An kai
su wani gida da ake kira "Gidan Yarima" (pic3) wanda aka gina shi a
shekarar 1809 bayan an gama jihadi. An kuma kara yima gidan gyare gyare a
shekarar 1888. Katsina ta burge kwarai yadda ta safkar da Turawan Mulkin
Mallaka a gidan da ya burge su har suka yaba. Hakazalika Katsina ta ciri tuta
akan yadda ta amshi turawan mulkin mallaka kuma su da kansu suka yaba da tsarin
da suka iske a Katsina wanda yake cike da basira. Gwamna Lugga ya yaba da ilimi
da kuma kaifin basira da tsari na Katsinawa a wancan lokacin.
Wannan yasa shi kanshi Gwamna Lugga yake cewa:
"Katsena boasts itself to be the seat of learning of Hausaland. It is probably a more ancient town than even Kano, and is built in the same style. I explained to the king (Sarki Abubakar) the conditions of British suzerainty, which he accepted with apparent cordiality" - Lord Lugard (1903).
Allah Ya ƙara ɗaukaka
mamu Jahar mu ta Katsina, da Masarautar mu da Kasa baki daya.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.