Ticker

6/recent/ticker-posts

Babbar Rana

Daga taskar sha’iri Sa’adu Malam Auwal, (Ɗanhausa, Zadawa)

Babbar Rana
Sa'adu Malam Auwal
(Ɗan Hausa Zadawa)

Rubutacciyar Waƙa

1.

Farko na saka sunan Allah

Wanda yai yo komai jumla

Rabbana ka tsare duk illa

Yarda in tsaro waƙena.

 

2.

Rabbana tsira da aminci

Ƙara ninkowa ga maceci

Shugaban nan mai adalci

Har da Ahlayen Manzona.

 

3.

Wassu baitoci na tsara

Ga shi na zo don in rera

Ga wagga rana da ta yi zarra

Juma'a Hajji babbar rana.

 

4.

Dole ne in cire takalma

Na iso fadar mai kima

Gaisuwar ladabi zan yi ma

Shehi, Farfesanmu gwanina.

 

5.

Sannu Farfesa Zulyadaini

Babu shakka ka wuce raini

Shehi ka zamto min tsani

Yarda in tsaro waƙena.

 

6.

'Yan uwa barkanmu da yamma

Ran ziyara duk mui himma

Juma'a kan zo da ganima

Kar a bar mu a baya zumaina.

 

7.

Nai kiran yaro har babba

Zantukana dukka mu duba

Mui ziyara za mu ci riba

'Yan uwa mu ƙaunaci juna.

 

8.

Juma'a babbar rana ce

Babu shakka duk ta zarce

Ranaku maganata sak ce

Na tuno a cikin Ƙur'ana.

 

9.

Suratul Jumu'ati akwai ta

Kan izu na biyar dubo ta

Yusabbihu ayar farkonta

Akwai batu da yawa ik'wana.

 

10.

Juma'ar da nake ta bayani

Ciki aka saukar Ƙur'ani

Ita ce kuma yaumud dini

Lahira kenan a batuna.

 

11.

Juma'a ranar taro ne

Duk Musulmi ba wani wane

Karkara kake ko birni ne

Don a yi bautar Rabbana.

 

12.

Na ji in ka rasu a cikinta

Juma'ar nan ko kwa darenta

Tambayarka akan ɗauke ta

Malamai sun mana bayana.

 

13.

'Yan uwa in mun idda sallar

Juma'a kar mui wani ɗar-dar

Je ziyara ba wanu gar-gar

Je ka gaishe baba da inna.

 

14.

To gidaje tashi ka zaga

Ka yi ziyara ba wata safga

Dukka dangi naku ka ƙirga

'Yan uwan nan Muslimuna.

 

15.

Zuciya ɗaya ba jayayya

Babu gaba babu ƙiyayya

To ga manya mu yi biyayya

Lahira mu shige Aljanna.

 

16.

Mu riƙe danƙo na zumunci

Gun maƙwabta mu yi karamci

Gun marayu mu yi halarci

Kar mu bar su cikin ruɗana.

 

17.

Shugabanni ku yi adalci

Talakawa mu bar lalaci

A kawar dukkan zalunci

Albarkar wannan rana.

 

18.

Sadaka ba wasa malam

Bayar abu na musamman

Rayuwa za ta yi kyawu na'am

To ka ji ɗabi'ar sunna.

 

19.

Ya Allah na roƙe ka

Ka kiyaye duk bayinka

Rayuwarmu ta yo kyau dukka

Don Annabi mai cetona.

 

20.

Allah sa ranar ƙarshenmu

Ta zamo kal hazal yaumu

Juma'at yaumul azeemu

Ya Rabbu ajeeb du'a'ina.

 

21.

To nan ne zan dasa aya

Sa'adun nan ne ya shirya

Ɗan Hausa Al-Gausiyya

Zadawa - Misau garina.

Post a Comment

0 Comments