Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsoron Matarsa Ya Hana Shi Ƙarin Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalam alaikum warahmatullah. Malam ina da yaya yanada mata amma wlhi ba ta bashi hakkin aurensa kuma ya nuna zai yi aure amma ta tada masa hankali taki yarda, shi kuma mun rasa meyasa yakejin tsoronta ya kasa yin auren saboda bataso, kuma wlhi yanzu dai har yana ƙoƙarin saɓawa Allah saboda ba ta bashi hakkinsa, shi ne yakeson atemaka masa da shawara da kuma addu'o'i, yanason yin aure amma tsoron matar ya hana shi ya yi kuma yana cikin wani yanayi na buƙatar auren. dan Allah a temakeshi.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To shi Wannan Wanne irin Namiji ne da yake Tsoron matarsa Haka? 🤔 Ya Sake ta Mana. Idan ya sake ta ai ya Huta da jin Tsoron ta ko? Idan kuma ba zai Iya Sakinta ba. To Kar Ma ya sake yayi Wani Aure. Sabida duk Matar da ya Aura, Wannan Auren ba zai zaunu ba. Ko Kuma wadda Aka Aura ɗin ta Zauna a Cikin Takura da Kunci da Wulakanci. Domin sai Abin da Wannan da yake Jin Tsoron ta tsara Masa shi Za ayi a Cikin Wannan Gidan. Kuma ba zata ta Tsara Abin da Zai yiwa Wannan Kishiyar Na Ta daɗi ba.

Ni na san wadda Mijinta yana jin Tsoron ta. Kullum a dakinta take Kwana. Sauran Matansa Biyu Ba su da Rabon Kwana. Haka zalika Su ne za su yi Girki su zubo su kawo mata, idan zai bayar da Kuɗin Cefane, sai dai ya ba ta Ta basu.

A wannan Zamanin gaskiya ba Matar da zata yarda da haka. Sai wadda Iyayenta Suka Ce Takura Mata da zama a Gidan wannan Mijin. Domin Hakan tana Faruwa.

Sabida haka ke nan yin Aure a Wajensa ma Kashe kuɗi ne a Banza. Kar ma ya Tarki Yin Wani Aure, Matukar dai ba zai dena jin Tsoron ta ba. Matukar dai ba zai sake ta ba.

Idan kuma Sihiri ne tayi masa, sai ku Karya Wannan sihirin. Idan Kukayi Haka to Kun samar Masa lafiya.

Allah shi ne Masani.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments