Saurayinta ya zo gaishe da iyayenta, aka Kai shi wajen tarɓar baƙi. Sun fara hira ke nan, sai ƴar aikin gidan ta kawo musu Lemo da Pizza.
Ya sanya hannu ya ɓantari Pizza ya fara ci. Ta ce, Ka ji daɗinta kuwa? Ya ce, sosai ma kuwa.
Ta ce, Ni nayita, na sha wahala sosai, duk don na burgeka. Umma ce ta kai ni wajen wasu ƙwararru, ta kashe kuɗi masu yawa suka koya mini, kuma fa na koya ne saboda kai kaɗai..!!
Ya ce, wallahi ta yi daɗi sosai, nagode da wannan hidima da kika yi, lalle in na aureki bani da matsalar abinci, na yi murna sosai, tabbas kin ƙware wajen sarrafa abinci...!!!
Bayan ya tafi, ta je ta samu Babarta ta ce, a ina kuka samo Pizza mai daɗi haka? Babarta ta ce, ai saurayinki ne ya kawo ta, shi ne na gutsuro muku.....!!!!😀
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.