Ticker

6/recent/ticker-posts

ZAMA DA MIJIN DA YAKE NEMAN MATA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam Shin yana halatta macce ta cigaba da zama da mijin dake neman mata, kuma har cikin gidanta yake kawo matan banzar, idan ta fita unguwa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, Ayi masa Nasiha, in bai ji ba, za ta iya neman rabuwa da shi, saboda Allah ya shar’anta saki ne saboda tunkude cuta daga Ma’aurata ko ɗaya daga cikinsu, kamar yadda Allah yake cewa a cikin Suratun Nisa’i:

وإن يتفرقا يغن الله كلا من سعته

Wannan halayyar kuma bayan kasancewarta haramun a Musulunci, akwai cutar da abokin zama a cikinta.

Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

 

Post a Comment

0 Comments