𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Malam yarinya ne aka aurar da ita batayi wata bakwai ba 7 ta haihu cikakkiyar yarinya yar wata tara (9) to malam meye hukuncin auren kuma ya hallaccin jaririyar a musulunci?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikum salam, In har an San tanada ciki aka yi auran wannan hukuncinsa a fili yake, kuma auran bai inganta ba a zance mafi inganci, amma in haihuwa ta yi bayan wata bakwai, kuma ba'a santa da ciki ba to Ɗansa ne, saboda ayar suratu Lukman da tá suratul Ahkafi sun nuna cewa ana iya haife ciki a watanni shida.
Auran da aka yi da cikin shege ba tare da an sani ba ya inganta, saidai ba za'a danganta cikin zuwa mijin ba, tunda ba shi ya yi ba.
In har ya san tana da ciki bayan sun yi aure bai halatta ya take ta ba har saí ta haihu, saboda fadin Annabi ﷺ "Duk wanda ya yi imani dá Allah da ranar Lahira to kar ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" kamar yadda Abu-dawud ya rawaito.
In ta haihu za su iya cigaba dá mu'amalarsu ta aure, musamman in bai sani ba saí da aka daura auren.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.