Ticker

6/recent/ticker-posts

SHIN YA HALATTA MUTUM YA KALLI AL'AURAN MATARSA?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Allahu Akbar Allah ya karawa babban malaminmu lafiya da sawan rai amen Allah ya kara ilimi da basira Allah ya yasa agama duniya lafiya amen.

Tambaya anan shi ne malam ya halatta mutum ya kalli al'auran matanshi kuma wani mutum amajalisarmu yana cewa duk mai kallon al'auran matan shi wai tun anan duniya zai samu masalar ido kuma Ba zai tafi lahira da ido Ba to malan me gaskiyar maganan Allah ya bada ikon amsawa

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Kallon al'aurar matar da ba taka ba, Wannan kai tsaye Haramun ne. Amma matarka ya halatta ka kalli al'aurarta. Kalli yadda manzon Allah ﷺ yake wanka tare da Nana Aisha mana a matsayin mata da miji, a banɗaki ɗaya a mukayi ɗaya a lokaci ɗaya. Amma dai kallon tsiraicin mace, matar aure ko Bazawara ko budurwa ko wata daban duk wannan bai kamata ba.

Malam usaimin acikin FATAWAL JANAZA ya ce idan mace ta kai shekara biyar ko wani abun da ya yi kama da haka, koda wankan gawa bai halatta namiji ya yi Mata ba, sai in har babu macen da za ta yi mata. Sai dai Kallon tsiraicin matar da ba taka ba zai iya haddasa Maka matsalar ido, kamar yadda suka gaya maka. Amma matarka ta halak ya halatta.

Allah shi ne masani.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

 

 

 

Post a Comment

0 Comments