Ticker

6/recent/ticker-posts

Yau Take Arafah

✍️Prof Mansur Sokoto, mni

Daga rubutun

Alhamis 8 Dhul Hajj 1442H (07/07/2021)

1. Yau talata 9 ga Dhul Hajji ita ce ranar Arafa.

2. Ita ce rana ta 9 daga cikin kwanukan shekara mafi daraja da falala a wurin Allah.

3. A ranar Arafat ne Allah ya kammala saukar da Alkur’ani ga Manzonsa a wurin Hajjin bankwana.

4. A wannan ranar Allah yana gafarta zunubai, ya yafe kurakurai, ya karba addu'oin bayinsa.

5. Allah ya rantse da wannan rana a inda ya ce:

  (واليوم الموعود *  وشاهد ومشهود)

 Al-Yaumul Mau'úd shi ne yinin alkiyama, Sháhid shi ne ranar Arafa, Mashhúd shi ne ranar Jum'ah. 

6. Kuma Allah ya rantse da ranar Arafa inda yake cewa: "والشفع والوتر" Shafa'i shi ne ranar layya, witiri shi ne ranar Arafa.

7. Hadisi ya inganta daga Manzon Allah (S) cewa, "babu wani yini wanda yake mafifici a wurin Allah fiye da yinin Arafa. Allah yana saukowa zuwa saman duniya sai ya yi kuri da mutanen kasa, ga mutanen sama". Sahihu Ibn Hibban 3583. Akwai hadisai da dama ingantattu a kan wannan. Duba Sahihu Muslim 1348 da Musnad Ahmad 8033.

8. A ranar Arafa ana son yawaita zikiri da addu'a. Kuma mafificiyar addu'a a ranar ita ce: "LA ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WALHUL HAMD, WAHUWA ALA KULLI SHAI'IN QADEER".

Ana kuma son a yawaita fadin: "SUBHANALLAH, WALHAMDU LILLAH, WA LA ILAHA ILLALLAH, WALLAHU AKBAR".

9. Magabata sun kasance a ranar Arafa suna aikata ayyuka iri daban daban na neman lada don samun gafarar Allah mahalicci.

10. An sunnanta yin azumi ga wanda ba ya aikin Hajji a wannan rana. Kuma ana fatar Allah zai yafe ma wanda ya yi shi zunubin bara da na bana.

11. Ana son mutum ya umurci iyalansa da yayansa - har kanana - su yi azumin ranar saboda gamewar falala da gafara.

12. Mutum yana iya yin azumin Arafa ko da ana bin sa bashin azumi. Idan kuma ya yi ramko a ranar babu laifi; ana sa ran zai samu karin falala saboda darajar wannan rana.

13. Babu laifi matafiyi ya yi azumin wannan rana idan ba zai sha wahala a kai ba.

14. Daga sallar asuba ta ranar Arafa ana so yin kabbarori bayan sallah "ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLALLAHU, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR,  WA LILLAHIL HAMD" daga nan har zuwa sallar la'asar a rana ta uku bayan sallah.

15. Daga cikin abubuwan da Annabi (S) ya roka a wannan rana akwai: gafara da jinkai da afuwa, da shiriya da tsarkin zuciya da sutura da wadatar arziki da lafiya da kamun kai da kariya da nasara da aminci da mafi girma kuma uwa uba; samun aljanna firdausi. Don haka ana son mutum ya dukufa da tsarkin zuciya da magiya ga ubangiji musamman a yammacin wannan rana domin neman bukatunsa na duniya da lahira da neman gafara ga kansa da iyayensa da iyalansa da kasarsa da al'ummar musulmi.

16. Akwai matukar hatsari ga yin sabon Allah a ranar Arafa saboda girmanta da darajarta a wurin Allah.

17. Alhazai a wannan rana suna cikin gafarar Allah, kuma Allah yana shaida ma Mala'iku haka.

18. Wanda bai samu tsayin Arafa ba, ya tsaya a kan iyakokin Allah. Wanda ba zai samu yanka dabba a gobe ba, ya yanka son zuciyarsa.

19. Rana ta 10 ita ce ranar Idi babba, kuma ranar layya. Ta fi duk sauran ranaku muhimmanci kuma babu abinda Allah ke so a ranar kamar kwararar da jinin dabbobi ana kiran sunansa.

20. Ranaku 3 bayan Sallah su ne Ayyamut Tashriq. Ana son musulmi ya darajta su, ya ci abinci, ya ziyarci yan uwa, ya caba ado, ya yi sadaka da sashen naman da ya yanka.

Allah ya yi mana muwafaqa da samun gafara, ya saukar mana da aminci da zaman lafiya da yalwantar arziki a kasarmu, ya daukaka addinin Musulunci da Musulmi.

Post a Comment

0 Comments