Ticker

6/recent/ticker-posts

Gargajiya: Nazarin Daɗewar Addini da Kaɗaita Ubangiji a Tsakanin Al'ummar Karai-Karai (4)

 Idan masu karanta tsakuren wannan bayani dake biye da ni ba su manta ba na kawo bayanin asalin inda kalmar Yahweh da ake ji Karai-Karai na faɗa ta samo asali tare kuma da ma'anarta. Abinda muka tsaya ƙoƙarin samu kuma a rubutu na ukun shi ne hujjar da za ta tabbatar mana da cewa wancan kalmar Yahweh din da na kawo mana tarihinta ɗin irinta ne kuma Yahweh ɗin da Karai-Karai suke amfani da ita ba wai abin ya faru ba ne a bisa tsautsayi ko kamanceceniya ta furuci irin na harshe kamar dai yadda ake samu a wasu lokutan. Wannan dalili ne kuma yasa tun fiz azal nace zan kasa bayanan zuwa matakai uku, inda kuma zuwa yanzu na riga na gama da mataki na ɗaya yanzu mataki na biyun zan kawo kuma shi zai ƙara ƙarfafa na farin yayin da shi kuma na ukun zai ƙarfafa na biyu.

Gargajiya: Nazarin Daɗewar Addini da Kaɗaita Ubangiji a Tsakanin Al'ummar Karai-Karai (4)

Musaddam Idriss Musa
07067132948

Karai-Karai

Duban Bakarkarai ta fuskar al'adarsa

Idan a na so a gane fasahar mutane da kuma kyan al'adarsu da ma tarihin su ko wayewar su a na duba ne izuwa ga al'adun su kamar shigar su, irin yadda suke tafiyar da rayuwarsu da kuma abu mafi muhimmanci irin nau'in sunayensu da suke amfani da su a matsayin sunayen su na gargajiya.

Shakka babu, sunayen gargajiya na Karai-Karai idan aka nutsu aka bi kowanne za a kai ga matakin gano ta inda ya samo asali har ma da ma'anarsa saɓanin sunayen da ake samu a cikin wasu al'ummun wanda duban abu kawai ake yi ko sauyawar yanayi sai a sakawa jariri misalan haka sun haɗa da sunaye irin su Damina daga ƙabilar Fulani da kuma Rumfa daga Hausawa za a ga cewa wannan sunaye ne da babu wani bukatar neman son jin ma'anar me suke nufi kuma akasari sauran sunayen gargajiya na al'ummu sun tafi ne a bisa irin haka. Dukda cewa su ma al'ummar Karai-Karai ɗin ba wai babu irin nau'in waɗannan sunayen ba ne misali wanda ya ci suna Shua /Shu'wa/  yana nufin kyakkyawa ne shi lokacin da aka haife shi yana jariri da dai sauran misalai.

Sai dai a nan sunayen da nake magana akan su, irin sunayen nan ne da tsofaffin dattawa na da daga cikin al'ummar Karai-Karai wanda yawanci zuwa yanzu da wuya a cikin Karai-Karai ɗari ka samu mai irin sunan guda saboda tasirin sauyin sunaye da aka samu wanda addinin Musulunci a yanzu ya zo mana da shi. Misalan irin waɗannan sunayen sun haɗa; Ari, Jalam, Aisa, Udeh, Maleka, Usaku, Dale, Saban da sauransu. Zai yi wahala a yanzu ƙwarai ka samu wani cikin matasan Karai-Karai da zai yi maka bayani akan ma'anar irin waɗannan sunaye kai harda ma wasu dattawan da dama ba don komai ba sai don nisan daɗewar zamanin samuwar su da kuma fara amfani da su amma abu mafi muhimmanci a nan shi ne fahimtar cewa waɗannan sunaye sun bayyana a jerin daɗaɗɗun sunayen shuɗaɗɗen harshen Hibraniyanci da na kawo batunsa a baya wanda hakan ƙwarai ya kamata a ce ya matuƙar bada mamaki saboda a iya sanin mu babu wata ƙabila a nan Najeriya da tayi tarayya wajen kamanceceniyar sunaye da al'ummar Karai-Karai balle ya zama dama a na da shirin sake jinsa a wata duniyar mai nisa irin haka, wato abin nufi, da ka ji ance Saban ko Usaku ko Jalam ka san cewa wannan mai sunan Bakarkarai ne idan ma ba Bakarkarai ba ne to takwaransa ne Bakarkarai ɗin shiyasa ya ci wannan sunan. Saboda haka, samuwar sunayen gargajiya na Karai-Karai a cikin daɗaɗɗen zamani irin wancan tun ƙarni na 6 babbar alama ce da ke bayyana abubuwa da dama ciki harda:

1. Tabbatar da al'ummar a matsayin waɗanda suka daɗe a doron ƙasa

2. Tabbatar da wanzuwar alaƙar su da mutanen gabas ta tsakiya a wani shuɗaɗɗen zamani

3. Tabbatar da kalmar Yahweh a matsayin sunan Ubangiji na Karai-Karai

4. Tabbatar da kyakkyawan baya da al'ummar take da shi

5. Tabbatar da sahihancin tarihinta.

 

Don haka a yanzu bari mu yi duba ga irin ma'anar da waɗannan sunayen suke da shi a harshen Hibraniyanci.

1. Suna Jalam a harshen Hibraniyanci na nufin mai zurfin ciki

2. Suna Malo yana nufin mai nasara

3. Suna Ari yana nufin Zakin Allah

4. Suna Udeh kuma na nufin Mai yabon Ubangiji

Ba iya nan ne kawai abin mamakin ba, hatta suna Maleka abinda yake nufi shi Ɗan aiken Ubangiji (wato mala'ikan da aikowa da sako) . Iya waɗannan bayanan kaɗai sun isa zama alama ta buɗe hanya ga mai karatu wajen sanin su wane ne Karai-Karai a zamanin shekarun da can ta fuskar addini.

Sai dai kum ƙarin abin mamakin duk yana gaba domin ba a ji komai ba idan ba san sirrin da ke tattare da fasalin ginin ganowowin garin Jalam ba wanda shi ne cikon bayani na ukun da nace zan kawo wato duban rayuwar Bakarkarai ta fuskar muhallinsa

Masu sha'awar wannan bayanin suna iya tuntuɓata don mallakar littafin Nazarin Rayuwar Karai-Karai da Addininsu na Gargajiya.

Post a Comment

0 Comments