𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
Alaikum malam, barka da kokari. Malam shin ya halasta macce ta je scanning ɗin
ciki, sannan ta tambayi likita mace za ta haifa ko namiji saboda suna son yin
sayayyar kaya kafin ta haihu? Na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
salam, ‘yar uwa ya halasta mace ta je scanninig ɗin cikinta a asibiti, har ma
ta tambaya shin mace za ta haifa ko namiji? Wannan ba wani abin da ke haramta
shi, saboda ilimi ne na gwaje-gwaje da aune-aune da Allah ya hore wa mutane su
domin amfaninsu. Sukan dace da faɗin daidai, sannan kuma sukan yi kuskure. Kuma
wannan ba ilimin gaibu ba ne, saboda gaibu babu wanda ya san shi sai Allah
kamar yadda ayoyin Alƙur'ani suka tabbatar.
Na taɓa
tattaunawa da wani ɗalibin ilimin likitanci game da faɗin kwanakin da ake sa
ran mai ciki za ta haihu da masu yin scanning sukan rubuta, sai yake ce min ai
ba ma na'urar ce take lissafawa ba, masu yin scanning ɗin ne kan tambayi mai
cikin lokacin da ta daina ganin al'adarta ta ƙarshe, sai su lissafa daga
lokacin zuwa wata tara, sai su ba da sakamakon lissafin nasu a matsayin lokacin
da ake sa ran mace za ta haifo cikin.
Ko kuma su
yi lissafi da adadin weeks ɗin da cikin ya yi kamar yadda na'ura ta nuna masu,
sai su lissafa zuwa lokacin da ake sa ran cikin da ya yi wannan makonni (weeks)
zai fita, sai su rubuta a sakamakon scanninig ɗin. To haka dai ya taɓa ce min
amma ban san haƙiƙanin lamarin ba. To ko ma dai mene ne babu laifi don mace mai
ciki ta je scanning ɗin ciki, saboda hakan na taimaka wa likitoci su san
matsayin da ciki yake na kwanciya daidai ko akasin haka, da wasu abubuwan
makamantan haka.
Allah S.W.T
ne mafi sani.
Jamilu
Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.