𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum. Malam ina maka fatan alkairi dan Allah a amsa min wannan tambayar.
Malam mace mai juna biyu tana fama da yawu, to ko da yaushe sai in da abin
taunawa a bakinta, ko sallah za ta yi, in kuma ba ta sa abu a bakinta ba to za
ta yi amai tana cikin yin sallar. To malam mene ne matsayin sallarta? nagode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salamu, Lallai cin abinci a cikin sallah yana ɓata sallah, kamar yadda duk
malaman Fiƙhu suka tabbatar, to amma shi ko amai ba ya ɓata sallah, saboda amai
ba najasa ba ne, don haka bai halasta ta yi sallah tana tauna komai a bakinta
ba, kawai ta yi sallarta a haka, ta sami kyallaye ko tsumma yalwatacce kuma mai
tsafta da idan amai ɗin ya zo mata za ta yi a ciki, ta share bakinta, ta kuma
ci gaba da yin sallarta, kuma sallarta ta inganta a hakan.
Allah ne
mafi sani.
Jamilu
Ibrahim Sarki, Zaria.✍🏻
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.