Hukuncin Sumbata (Kiss) Da Runguma Tsakanin Saurayi Da Budurwa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Malam Watane tana Tambaya in sun haɗu da saurayinta sai sun yi kissing suna hugging amma basa saduwa kuma tana so tadena wannan aikin amma takasa yaza ta yi Malam nagode

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus salam, Dukkan godiya ta tabbata ga Allah.

     Zina (yin fasikanci) ba wai yana nufin saduwa kawai ba, a'a, akwai zinar hannu, wato taɓa abinda yake haramun, da zinar idanu, wacce take ta kallon haram, duk da cewa zina wacce aka yi ta da al'aura, ita ce zina wadda ake azabtar da wanda suka yi ta da azabar haddi.

     An karbo daga Abu Hurairata Allah Ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Allah ya shar’anta wa kowane ɗan Adam rabonsa na zina, wanda ba makawa zai aikata. Zinar idanu ita ce kallo, zinar harshe ita ce magana, mutum yana iya buri da sha’awa, al’aura kuma ita ke tabbatar da haka ko kuma ta musanta”. (Bukhari ya ruwaito shi, 5889; da Muslim, 2657).

    Ba ya halatta ga musulmi ya yi kwadayin abubuwan da za su kai shi ga zina, kamar sumba, kadaitaka, taɓawa ko kallo, domin duk waɗannan haramun ne kuma suna kai ga mafi girman sharrin zina.

     Allaah (تعالى ) yana cewa:

    وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا

    Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya. (wato duk abin da ya ketare iyakokinsa: zunubi mai girma, kuma muguwar hanya ce wadda take kai mutum wuta face sai idan Allah Ya gafarta ma mutum). Suratul Isra’i 32].

     Duban abin da yake haramun ne yana daga cikin kiban Shaiɗan, wanda ke kai mutum ga halaƙa, ko da bai yi da gangan ba tun farko. Allaah (تعالى ) yana cewa:

    Ka ce wa muminai maza su runtse daga ganinsu (daga kallon haram), kuma su tsare farjojinsu (daga haram). Wancan ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne Allah, ga abin da suke aikatãwa Masani ne.

     Kuma ka ce wa muminai mata su runtse daga ganinsu (daga kallon haram), kuma su tsare farjojinsu (daga haram)”. [suratul Al-Nur 30-31]

     Ka yi tunani a kan yadda Allah ya haɗa lamarin runtse ido da mas’alar kiyaye farji (kare farjinta) a cikin waɗannan ayoyi, da yadda aka fara ambaton runtse ido, kafin kare al’aura, domin ido yana rinjayar zuciya wajen aikata zunubi.

     Shaikh Abdul'Azeez bn Baaz (rahimahullah) yana cewa: A cikin waɗannan ayoyi guda biyu, Allah ya umurci muminai maza da mata da su runtse idanuwansu, su kiyaye farjinsu, saboda tsananin girman zina da abin da yake haifar da fasadi mai girma a tsakanin musulmi. Barin kallonsa ga abinda yake haram yana daga cikin abubuwan da ke haifar da cuta a cikin zuciya da faruwar ayyukan fasikanci, yayin da runtse ido yana daga cikin hanyoyin kiyaye kai daga hakan. Don haka Allah (تعالى ) yake cewa:

     “Ka ce wa muminai maza su runtse daga ganinsu (daga kallon haram), kuma su tsare farjojinsu (daga haram). Wancan ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa." [Suratul Nur 30].

    Runtse ido da kiyaye farjin shi ne mafi tsarki ga mumini duniya da Lahira, amma mutum ya bar kallonsa cikin walwala da rashin kiyaye farjinsa suna daga cikin manya-manyan sababi na halaƙa da azaba a duniya da kuma Lahira. Muna rokon Allah ya kara mana kare mu.

     Allah ya gaya mana cewa shi Masani ne ga abin da mutane suke aikatawa, kuma babu wani abu da yake ɓoye a gare shi. Wannan gargadi ne ga muminai a lokacin da suke aikata abin da Allah ya haramta da nisantar abin da Allah Ya shar'anta musu, kuma tunatarwa ce a gare shi cewa Allah yana ganinsa, kuma ya san dukkan abin da yake aikatawa, na alheri ko waninsa. Kamar yadda Allah (تعالى ) yake cewa:

     "ALLAH yana sanin ha'incin idanu, da abin da ƙirji ke ɓoyewa". [Surat Ghafir 19]

     Ƙarshen magana Daga bakin al-Tabarruj wa Khataruhu.

     Wajibi ne musulmi ya ji tsoron Ubangijinsa a ɓoye da bayyane, kuma ya nisantar da abin da Allah Ya haramta na kadaita shi da wani ma'abocin jinsi, kamar kallo, ko musafaha, ko sumbata da sauran ayyuka na haram waɗanda ke kai ga aikata fasikanci (zina).

     Kada a yaudari juna da tunanin cewa ai ba zina ake ba, kawai dai sumbata ne da runguma, kuma shi wanda aka yaudara ya tsaya a kan wannan cewa ba komai bane, ko soyayya ce ko aure za muyi, ya sani irin wannan laifin ke kai ga aikata babbar zina, kuma a karshe a zo a yi abinda za a zo ana da - na - sani.

    Kuma a yi duk iya kokari wajen nesanta kai daga wannan mummunar dabi'ar da kazantar, domin kazanta ce mace ta sa bakinta akan bakin saurayin da bata aura ba, bama ta gama sanin rayuwarsa ba, kuma zunubi ne mai girman gaske da ke kai mutum ga azabar Allah maɗaukaki.

    Kuma babbar hanyar nesanta kai daga wannan mummunar dabi’un shi ne rabuwa da wanda ake yi dashi, da guje masa, da rashin haɗuwa dashi, da kuma tuba na gaskiya da istigfari, kuma mutum ya ɗaure ya yi aure sai ya huta daga irin waɗannan kananan zunuban da sukan kai mutum zuwa shiga wuta, Allah ya tsare mu. Akwai rubutun mu akan HANYOYIN GARKUWA DAGA ZINA in shaa Allah za su taimaka wajen magance wannan dabi'a.

     Wanda ya aikata ɗaya daga cikin waɗannan ayyukan to ya tuba ga Allah, domin duk wanda ya tuba Allah zai karɓi tubarsa, wanda ya tuba kamar wanda bai yi zunubi ba ne.

     Ɗaya daga cikin mafi girman kaffarar irin waɗannan zunubai shi ne yawaita salloli biyar akan lokaci. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Salloli biyar, da daga wata Juma’a zuwa wata, da kuma watan ramadan zuwa wani, suna kankare zunubban da suka shiga tsakani, matukar dai an nisanci manyan zunubai”. Muslim ne ya rawaito shi, 1/209

     Kuma Allah ne Mafi sani.

    ✍️Shashen Fatawowi Bisa Ƙur'ani da Sunnah, A Bisa Fahimtar Magabata Kwarai.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.