Ticker

6/recent/ticker-posts

Wani Lokaci Ne Ya Kamata Mace ta yi Sallar Azahar A Ranar Jumma'a?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam kamar da wanne lokaci ne ya kamata ace mace ta yi sallar azuhur a ranar juma'a, shin za ta yi ne kafin a yi juma'a ko kuma sai bayan an idar da juma'a sannan za ta yi sallar azuhur ɗin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Shi dai lokacin sallar azuhur yana shiga ne daga lokacin da rana ta yi zawali (ta karkace daga tsakiyar sama) to amma mutanen da sallar juma'a ba ta wajaba a kansu ba kamar irin su: matafiyi, Bawa, mace, maras lafiya, da dai sauran ma'abota uzuri, shin wai za su yi sallarsu ne da zarar lokaci ya shiga ko kuma dole za su jira har sai an dawo daga juma'a?

Maganar da take tabbatacciya a shari'ance kawai za su yi sallarsu a duk lokacin da sukaga dama, ko dai suyi azuhur ɗinsu tun kafin a yi juma'a, ko su yi ta a lokacin da a ke yin sallar juma'ar, ko kuma suyi sallarsu bayan an taso daga juma'a, duk hukuncin ɗaya ne ba wani bambanci, amma yin sallah a farkon lokaci yafi lada.

Sannan kuma ya halatta mace ta halarci sallar juma'a tare da liman sai dai in ana jin tsoron faruwar wata fitina a dalilin zuwanta ɗin, to sai ta yi sallar azuhur ɗinta a gida kawai.

​​шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'α'αʟαм

 ​Mυѕтαρнα Uѕмαn

 ​08032531505​

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄��𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments