Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mace Za Ta Bayyana Karatu A Sallah Kamar Yadda Namiji Ke Bayyanawa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Shin mace idan za ta yi sallah wacce ake bayyana karatu ita ma ya halatta ta bayyana?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, Tabbas idan mace za ta yi sallar da ake bayyana karatu ita ma za ta bayyana ne kamar yadda Annabi ﷺ yake bayyanawa, haka kuma idan sallar da ake ɓoye karatu ne ita ma za ta ɓoye ne, kamar yadda Annabi ﷺ yake ɓoyewa, saboda "Manzon Allah ﷺ ya ce: Ku yi sallah kamar yadda kuka ga ina yin sallah". Bukhariy ya ruwaito a hadisi mai lamba ta: 7246.

A nan sai malamai suka ce babu bambanci a tsakanin sallar namiji da tamace, saboda ba a sami wani nassi ingantacce da ya zo daga Manzon Allah ﷺ da ke nuna cewa sallar mace ta sha bamban da sallar namiji ba ta fuskar bayyana karatu ko ɓoyewa, don haka kenan yadda namiji ke bayyana karatu a sallah haka mace za ta yi babu abin da ya bambanta su, wannan zance shi ne mafi zama daidai saboda wancan hadisi da ya gabata.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments