Ticker

6/recent/ticker-posts

WANENE ABOKINKA?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assslamu alaikum. Malam ina da abokai da yawa, amma ina so ka ba ni shawara?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, To ɗan'uwa Aboki yana da mutukar mahimmanci a rayuwar mutum, idan ya zama abokinka mutum ne mai himma, sai kai ma ka samu himma kamar yadda ake cewa zama da madaukin kanwa yana kawo farin kai, haka nan idan ya zama mutumin banza sai ya yi maka tasiri.

Abu Musa Al’ash’ari ya rawaito hadisi daga Annabi ﷺ yana cewa (misalin aboki na gari da abokin banza, kamar misalin mai ɗaukar turare ne da mai hura zuga-zugi, mai ɗaukar turare ko dai ya shafa maka ko ka sayi turare a wurinsa ko kuma ka ji kamshi mai daɗi a wurinsa, mai hura zuga- zugi kuma ko ya kona maka kaya ko ka ji wari a wurinsa) Bukhari ne ya rawaito.

Kuma wani malami yana cewa: idan ka kasance a cikin mutane, to ka yi abota da zaɓaɓɓen su, kada ka yi abota da halakakke saiku halaka tare.

Idan kana so ka san waye mutum, to ka tambayi abokinsa, saboda kowanne aboki da abokinsa yake koyi.

Wani kuma yana cewa: Kar ka aboci malalaci a kowanne hali, da yawa mutumin kirki yana lalacewa ne idan ya haɗu da mara kirki.

Dakiki yana saurin tasiri akan mai kokari, ba ka ganin garwashe idan aka saka shi a toka shi ma sai ya zama toka.

Da fatan za ka kula da abin da ya gabata.

Allah na mafi sani

Amsawa🏻

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

 

Post a Comment

0 Comments