𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam. Allah ya yi wa mahaifina rasuwa ina bukatar addu'arku. Sannan zan iya yin layya da niyyar Allah ya kai Masa ladar layyar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam, ‘yar uwa muna yi wa mahaifinki addu'ar Allah ya jiƙan sa ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma lulluɓe shi da rahamarsa, da sauran duk Musulman da suka gaba ce mu.
Yi wa mamaci layya ba tare da ya yi wasiyya ba, yana daga cikin masá'il da malamai suka yi saɓani a kai, sai dai mafi yawan malamai sun karkata a kan halascin yi wa mamaci layyar.
Saboda ya tabbata Nana A'isha ta ruwaito hadisi cewa Manzon Allah ﷺ an zo masa da rago ya yi layya da shi, a lokacin da zai yi layyar sai ya ce:
"Bismillah, ya Allah ka karɓa daga Muhammad da Iyalan Muhammad da kuma al'ummar Muhammad". Muslim 1967.
Sanannen lamari ne cewa daga cikin al'ummar Annabi Muhammad ﷺ akwai mamata, sai ga shi Manzon Allah ﷺ ya sa su a cikin layyar da ya yi, a nan sai malamai suka ce wannan ya nuna halascin yi wa mamaci layya. Sannan malamai sun bayyana cewa mamaci na amfana da sadakar da aka yi masa, saboda haka layya ga mamaci sadaka ce daga cikin sadakoki, ana fatan in Allah ya yarda mamaci zai amfana da sakamakon sadakar.
Amma duk da haka ba a ruwaito cewa Annabi ﷺ ya duƙufa da yi wa mamata layya duk shekara ba, in da a ce abu ne da za a yi ta yi a duk shekara da an ruwaito cewa Annabi ﷺ ya duƙufa a kai, sai dai ya halasta a yi ba tare da dauwama a kan haka duk shekara ba.
Domin ƙarin bayani a duba ALMAJMÚ'U (8/406 - 407). Ko a duba Maɗálibu Ulin-Nuhá (2/472).
Allah S.W.T ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.