𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Aslm malm, tambayata anan shi ne ni da mijina ne babu jituwa ko na kaɗan, ni Kuma abin nadamuna narasa yanda zanyi da raina ina son aure saidai abin nason yafi karfina wanda gara nabar gidan kawai, dan Allah kabani shawara shekaramu goma Sha ɗaya da aure amma babu daɗi a tsakanin mu
Ban rasa Sha ba Kuma ban rasa ci ba Amma zamantakewan aure babu.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To menenen damuwar? Zaki fara duba Menene Matsalar da ta sa baki da jituwa a Tsakanin Ki da mijinki, Duk da baki Ambata mana ita Wannan damuwar ba. Amma dai zaki Kalli matsalar. Idan daga wajen ki ne. Sai ki san yadda zaki gyara. Idan kuma daga wajen sa ne. Sai ki bashi shawarwari ta hanyar Amfani da Lafuza Masu daɗin Sauraro. Ma'ana ta yadda zai saurareki kuma ya Fahimceki. Inaga idan kinbi wannan shawarar In shã Allahu za ku sami daidaito a Tsakanin ku. Kuma zamanku zai chanja Zane.
Allah shi ne Masani.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.