Kundin bincike da aka gabatar a Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Tsangayar Fasaha Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, don samun shaidar kammala digiri na ɗaya (BA.HAUSA), 2021.
Tasirin Magurzar Auduga A
Garin Mayanci
NA
MANNIR SANI
GODIYA
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin
sarki wanda ya bani dama da kuma iko na gudanar da wannan bincike tare da yabo
gun fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW), ina godiya ga Allah bisa baiwa da
iko da ya bani na kammala wannan karatu a matakin Digiri na farko, da fatan
Allah ya sa karatun ya zama mai amfani a gare ni da kuma al'umma baki ɗaya, amin.
Godiya ta
musamman ga Dr Musa Fadama Gummi wanda
ya ɗauki nauyin duba wannan aiki nawa. Domin ba zan manta da irin ɗawainiyar da
wahalhalu da ya sha wajen yi min gyare-gyare tare da kuma shawarwari, da fatan
Allah ya saka masa da alkhairi. Ba zan manta da ƙoƙarin da sauran malamai na
suka yi a kaina ba kamar irinsu, Prof. Aliyu Muhammad Bunza, da Prof. Magaji
Tsoho Yakawada, da Prof. Muhammad Lawal Amin, da Prof. Balarabe Abdullahi, da
Prof. Aliyu Musa, da Dr. Adamu Rabi'u Bakura, da Dr. Nazir Abbas Ibrahim, da
Dr. Rabi'u Muhammad Tahir, da malam Aliyu Rabi'u Ɗangulbi, da malam Isah Sarkin
Fada, da malam Musa Abdullahi, da malam Bashir Abdullahi, da malam Abu-ubaida
Sani, da malam Muhammad Umar Arabi, da malama Halima Mansur Kurawa da sauran
malamaina waɗanda ban ambaci sunansu ba. Da fatan Allah ya saka masu da
alkhairi bisa irin tarbiyar da suka
bamu, sun ɗauke mu tamkar 'ya'yan da suka haifa a cikinsu. Allah ya sanya
albarka a cikin rayuwarsu.
Godiya ta
musamman ga mahaifina Alhaji Sani Alhassan mai fulla da mahaifiyata Hajiya
Fatima Usman bisa irin ɗawainiyar da suka yi da ni tun daga yarinta ta har kawo
yanzu, ina mai roƙon Allah ya sama rayuwar su albarka, amin! Ba zan taɓa
mantawa da yaya na Abdullahi Sani da antina Zulaihat Sani ba saboda irin
ƙoƙarin da suka yi da ni, tare da addu'o'in da suka yi ta min don samun nasara
a rayuwata. Haka kuma ina ƙara godiya da abokina Usman Abubakar Ittaqillaha da
sauran abokaina kuma aminaina bisa irin taimako da addu'o'i da suka yi min don
ganin na samu nasarar kammala wannan karatu, da fatar Allah ya saka masu da
mafificin lada ya kuma albarkaci rayuwarsu baki ɗaya.
Daga ƙarshe ina
miƙa godiyata ga sauran 'yan uwana ɗalibai da muka kammala karatu tare a wannan
zango kamar irinsu Abdulrashid Isma'il, da Sadam Yusuf, da Mahadi Almustafa, da
Abbas Muhammad Husain, da Aminu Muhammad, da Lawali Ya'u, Abdulrahaman Tukur da
Bashir Lawali, Umar Muhammad, da Ridwan Mahmud, da Amir Tujjani Lawal da Jamilu
Ibrahim da hajiya Rabi S/Zamfara da hajiya Saudatu Ɗalhatu, da hajiya Binta
Gambo, da Asiya sulaiman da sauran dukkan ɗalibai na wannan sashe da fatar
Allah yasa kowa ya kammala wannan makaranta lafiya, Ameen
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan bincike mai suna 'Tasirin
magurzar auduga a garin Mayanci' ga mahaifina Alhaji Sani alhassan mai fulla da
mahaifiyata Hajiya Fatima Usman da yaya na Abdullahi Sani da antina Zulaihat
Sani. Tare da su kuma akwai sauran 'yan uwa da abokan arziki.
TSAKURE
Wannan kundi na bincike ya ƙunshi taƙaitaccen tarihin
garin Mayanci, da kuma ma'anar auduga da ire-iren auduga da yadda ake noma
auduga. Wannan bincike ya bayyana ma'anar tattalin arziki da hanyoyin tattalin
arziki, haka kuma wannan bincike ya bayyana irin tasirin da magurzar audugar ta
yi ga mutanen garin Mayanci da kuma baƙin da suka shigo garin sanadiyyar
magurzar audugar. A ƙarƙashin wannan aiki an bayyana ma'anar Zamantakewa da
kuma ire-iren Zamantakewa a garin Mayanci.
BABI NA ƊAYA
1.0 GABATARWA
Dukkan yabo
da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, mahaliccin kowa da komai.
Tsira da aminci Allah su tabbata ga shugaban halitta, Annabi Muhammad (S A w),
da sahabbansa da alayensa da waɗanda suka bi shi da kyautatawa har zuwa ranar
sakamako.
Wannan aiki
namu mai taken "Tasirin magurzar auduga a garin Mayanci", aiki ne da
zai binciko ire-iren tasirin da aka samu a ɓangaren zamantakewa da kuma
tattalin arziki a garin Mayanci.
Garin Mayanci
ya kafu a shekara ta (1825), ƙarƙashin jagoranci Na'ali Damamisau da jama'arsa,
garin Mayanci yana cikin ƙasar Maru ta jahar Zamfara.
Noman auduga sana'a ce mai matuƙar muhimmanci
ga rayuwar 'yan Najeriya musamman manomin auduga ko mai sayar da irin auduga ko
mai fataucin auduga da masu masaƙu da masana'antun yin sutura.
Farfesa
Umar, ya ce noman auduga abu ne da ke taimakawa wajen biyan buƙatun 'yan'adam
saboda ɗan'adam yana buƙatar abinci da matsugunni da sutura, kuma auduga tana ɗaya
daga cikin abin da ke biyan buƙatar ɗan'adam ta fannin sutura, kuma a gidaje ma
auduga na biyan buƙata. Saboda mafi yawa daga cikin wuraren da ake tsugunar da
'yan gudun hijira kamar su tamfol- tamfol da auduga ake yin su.
1.1 MANUFAR BINCIKE
Duk wani abin
da ɗan'adam ya ƙuduri aiwatarwa a rayuwarsa, za a tarar cewa, lallai, akwai
wata manufa da ta wajabta a aiwatar da wannan abin.
Masu iya magana kan ce 'kowane allazi da nasa amanu,
idan muka lura da wannan zance za mu fahinci cewa babu wani bincike da za a
aiwatar ba tare da manufar gudanar da shi ba. Don haka manufofin gudanar da
wannan bincike su ne; domin samun takardar shaidar kammala karatun digirin farko,
haka kuma fito da yadda yanayin tasirin yake, yana ɗaya daga cikin manufofin
wannan bincike. Haka kuma manufar wannan bincike fitowa tare da nuna
muhimmancin noma auduga a wajen al'umma da kuma tasirin ta.
1.2 HASASHEN BINCIKE
Ƙamusun Hausa
(2006:197) ya bayyana wannan kalma da cewa "Hasashe kalma ce da ta ke
nufin kintace, ko kirdadon wani abu da zai auku".
Da haka za
a iya cewa hasashe na nufin kintace ko kuma tsammani.
Saboda haka kamar yadda taken wannan bincike ya nuna "Tasirin
Magurzar Auduga A Garin Mayanci" Hasashen shi ne.
- Gabatar da wannan aiki zai wayar da kan al'umma,
dalili shi ne, mutane da dama ba su da masaniyar cewa: wannan magurzar auduga
ta garin Mayanci ta yi tasiri a fannoni da dama.
- kuma ana hasashen aikin ya zama wata manazarta ga
masu bincike.
- Bugu da ƙari ana hasashen wannan aiki ya zama wani
madubi na hangen abin da ya kamata ayi koyi da shi.
- Mai wannan bincike na hasashen cewa, wannan aiki zai
samu karɓuwa a duniyar ilimi musamman ga manazartar sana'o'in Hausawa.
1.3 FARFAJIYAR BINCIKE
Farfajiyar
bincike na nufin muhallin bincike, shi kuwa muhalli a wani ƙamus na Newman
(1997) an bayyana ma'anar muhalli da: "muhalli shi ne kewayen da kake
zama".
Shi kuwa
Soba, (2015) a cikin littafinsa mai suna "Muhalli a idon Hausawa don
makarantun gaba da Sakandare". Ya ba da ma'anar muhalli da harshen Larabci
tana nufin "Bagire" ko "Wuri" kamar yadda suke amfani da
ita a fagen ilimi".
A fagen
bincike kuwa, ana kallon farfajiya ko muhallin bincike da iya wurin da binciken
da muke gudanarwa ya taƙaita, wato fannin da muke bincike a kai.
Wannan aiki
namu mun gudanar da shi ne a ɓangaren Al'adu. A cikin al'adun ma, mun gudanar
da aikin ne a ɓangaren zamantakewa da tattalin arziki, mun mai da hankali ne ga
sauye-sauyen da aka samu a ɓangaren zamantakewa da kuma tattalin arziki a garin
mayanci kawai. Wannan shi ne ainihin farfajiyar bincikenmu.
1.4 MATSALOLIN BINCIKE
Aikin
bincike kowane iri yana da matsalolin da mai gudanar da shi ke cin karo da su,
wasu kafin ya fara gudanar da bincike, wasu kuma ana ciki ake karo da su. Kafin
mu kawo matsalolin ya kamata mu bayar da ma'anar ita kanta matsalar.
Soba, S.A
(2016) ya bayyana ma'anar matsala da cewa "Matsala tana iya zama tawaya ga
duk wani abu da mutum yake yi, ko zai yi".
Ita kuma
Sa'adatu Labaran da wata (2017) a cikin kundin bincikensu na digiri na farko
mai taken "Gudunmuwar wayar salula wajen bunƙasa aikin gidajen Rediyo da
Talabijin a jihar Zamfara" sun bayyana ma'anar matsala da cewa:
"Matsala wani mawuyacin abu ne wanda ke da wahalar magancewa".
Bisa la'akari da waɗannan ma'anoni da ke sama, za mu
iya cewa matsala wata tarnaƙi ce wadda ke tasowa mai wahalar magancewa.
Kamar yadda
muka ga ma'anar matsaloli daban-daban a sama, to a aikin bincike, mai bincike
na duban matsalolin bincikensa ta fuskoki biyu kamar haka:-
1. Matsalolin da suka taso.
2. Matsalolin da aka fuskanta.
Matsalolin
da suka taso su ne matsalolin da mai bincike kan ci karo da su kafin ya fara
gudanar da binciken nasa. Matsalolin da suka taso a fagen wannan bincike su
ne:-
a. Matsalolin samun batu, watau sanin abin da mutum
zai yi bincike a kansa: - Wannan matsala ce babba, domin kuwa sai an yi bincike
an yi nazari tare da tambayar masana kafin a samu takamaiman abin da mutum zai
yi bincike kansa, wannan na ɗaukar dogon lokaci.
b. Wata matsalar ita ce, amincewa da batun da aka
gabatar, shi ma wannan matsala ce babba, domin kuwa mutum zai shiga ruɗani da
faɗuwar gaba tare da tunanin za a yarda da batun da ya kawo ko ba za a yarda da
shi ba? Wani lokaci a kan bai wa mutum batun da ya gabatar, wani lokaci a kan
canza ko a yi masa ragi ko ƙari.
c. Ƙarancin kayan bincike na aiki kamar litattafai,
kundaye, mujallu, da sauransu. Wannan ma wata matsala ce domin akwai ƙarancin
kayan bincike na aikin.
Alhamdulillah, duk da waɗannan matsalolin da suka taso mana a wannan
bincike, mun samu shawo kansu, ga shi har an bamu damar cigaba da bincike.
Matsalolin
da aka fuskanta kuwa matsaloli ne da masu bincike ke cin karo da su yayin da
suke gudanar da aikin nasu na bincike. Matsalolin da muka fuskanta wajen
gudanar da wannan aiki namu sun haɗa da: -
a. Matsalar ƙarancin littattafai a fannin da muke yin
nazari a kansa:- Wannan matsala ce da muke fuskanta, domin kuwa mukan yi yawo
sosai daga nan zuwa can domin neman wani aiki da ke da 'yar alaƙa da namu. Wani
lokaci kuwa sai mun fassara wasu bayanai daga harshen Ingilishi zuwa harshen
Hausa.
b. Matsalar rashin isasshen lokaci: - mun fuskanci
matsalar rashin isasshen lokaci, don kuwa aikin bincike aiki ne mai buƙatar
lokaci.
c. Matsalar samo bayanai: Ita ma wannan matsala ce da
muka fuskanta, domin bincikenmu yana buƙatar ganawa da mutane daban-daban wajen
samun bayani. Wani ba zai ba mu lokacinsa ba wani kuwa sai mun yi ta kaiwa da
komowa kafin mu samu ganawa da shi. Wannan ma kan ɗauki dogon lokaci.
d. Matsalar kuɗi: kuɗi masu gida rana inji Bahaushe,
wannan babbar matsala ce ga duk mai aikin bincike. Domin kuwa, bincike aiki ne
da ke buƙatar zirga-zirga tun daga ganawa da masana, ziyarce-ziyarce, sayen
litattafai da kuma buga shi kansa aikin ga kuma tsadar kayan masarufi a ƙasar
tamu.
e. Matsalar wutar lantarki: Wannan ma matsala ce ga
masu aikin bincike, kasancewar da rana ne mutum ke ƙoƙarin samo bayanai idan
dare ya yi zai fi samun natsuwar da zai shirya bayanan da ya samu, sai kuma ka
ga an ɗauke wutar lantarki, sai dai ka yi amfani da fitila ko kyandir, mutum
bai samun ci gaba da aikin nasa cikin daɗi da walwala, domin haske rahama ne.
Waɗannan sune kaɗan daga matsalolin da muka fuskanta a wannan bincike.
1.5 MUHIMMANCIN BINCIKE
Muhimmancin
yin bincike a kan wata matsala da ba a san ta ba, ko ƙari ga wani abu wanda aka
sani domin bayar da gudummawa ko warware wata matsala da ta zama damuwa ga
al'umma. Bunza A.M (2017).
Don haka
bincike yana da muhimmanci sosai ga al'umma don duk al'ummar da suka fiye
gudanar da bincike to za a samu sun fi ci gaba ga al'amurransu na rayuwar yau
da kullum.
Muhimmancin wannan bincike zai iya kasancewa kamar
haka:
- Wannan bincike zai taimaka ga al'umma domin sanin
yadda magurzar auduga tayi tasiri ga al'ummar garin Mayanci.
- Wannan bincike zai taimaka wurin sanin tattalin
arzikin al'ummar garin Mayanci.
- Zai zama wani muhimmin kundi wanda zai taimaka ma Ɗaliban
ilimi da masu bincike a kan harshen Hausa.
- Wannan bincike yana da matuƙar muhimmanci sosai, saboda zai taimaka ƙwarai da gaske ga
'yan uwa ɗalibai da manazarta.
- Wannan bincike zai taskance tarihin garin Mayanci.
1.6 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE
Kamar yadda
yake a al'adar kowane bincike, akwai hanyoyin da akan bi domin samun nasarar
gudanar da shi. Haka shi ma wannan bincike yana da hanyoyi da aka yi amfani da
su domin samun nasarar gudanar da shi.
Tattaunawa
tare da neman shawarar masana da manazarta falsafa kan wannan bincike da duba
kundayen digiri na farko, da na biyu da na uku, da Wallafaffun littafai da kuma
maƙalu waɗanda suke da alaƙa ta kusa da nesa da wannan bincike, a ɗakin karatu
na sashe da kuma babban ɗakin karatu na jami'a, da ma sauran ɗakunan karatu da
aikin ya samu kansa ciki.
Daɗindaɗawa,
an yi amfani da wasu hanyoyi domin gudanar da wannan bincike da aka nazarci waɗanda
suke da alaƙa da wannan bincike kamar tattaunawa da masana a wannan fannin.
1.7 NAƊEWA
Daga ƙarshe
wannan babin gabatarwa ce game da wannan aikin bincike, domin haskakawa ga mai
karatu, wanda yazo da gabatarwa, manufar bincike, hasashen bincike, farfajiyar
bincike, matsalolin bincike, muhimmancin bincike, hanyoyin gudanar da bincike,
daga ƙarshe babi ya zo da naɗewa.
BABI NA BIYU
BITAR AYYUKAN DA SUKA
GABATA
2.0 GABATARWA
Masana da manazarta sun yi ayyuka masu ɗimbin yawa a
lokutta daban-daban masu alaƙa da wannan aiki namu. Saboda haka a wannan babi
zamu duba ayyuka da suka gabata masu alaƙa da wannan aiki namu. Zamu duba
kundayen bincike, bugaggun littattafai da kuma mujallu da muƙalu.
2.1.1 KUNDAYEN BINCIKE
Akwai
kundayen bincike da dama masu alaƙa da wannan aiki namu. Akwai kundin bincike
na:
Bunguɗu,
A.I. da wasu (1999),[1] mai taken: "Bincike a
kan Sana'o'in Kaɗi da Daddawa da Mazanƙwaila da Tukanen laka na Da da na Zamani
a Ƙasar Hausa". Manazarta sun yi ƙoƙari ƙwarai da gaske wajen bayyana
ma'anar kaɗi, kayan aikinta, yadda ake gudanar da ita. Ma'anar daddawa yadda
ake yin daddawa, kayan aikinta, ma'anar mazanƙwaila, yadda ake yin mazanƙwaila,
kayan aikinta, ma'anar tukanen laka na da da na zamani da kuma tasirin zamani
akan dukkan Sana'o'in. Wannan aiki yana da alaƙa da namu aiki ta fuskar
tattalin arziki. Bambancin da ke tsakanin namu aiki da nasu shi ne, nasu aiki
yana magana akan ƙasar Hausa baki ɗaya, yayin da wannan aiki ke magana akan
"Tasirin magurzar auduga a garin Mayanci". Ya keɓanta ne a kan garin
Mayanci ne. Haka kuma basu yi magana a kan zamantakewa ba.
Maru, I.U.
da wasu (2012),[2]
a kundin bincikensu mai suna "Sana'o'in Daddawa a Jihar Zamfara"
manazarta sun yi bayani a kan ma'anar sana'ar daddawa da yadda ake yinta, kayan
aikinta tare da muhimmancinta. Wannan aiki yana da alaƙa da namu aiki ta fuskar
tattalin arziki. Bambancin da ke tsakanin aikinsu da namu aikin shi ne; Namu
aiki yana Magana ne a kan sauyin zamantakewa da tattalin arziki a garin
Mayanci. Yayin da nasu aiki ke magana ne a wani ɓangare daga cikin hanyoyin
tattalin arziki wato sana'ar Daddawa a jihar Zamfara, sai dai basu taɓo ɓangaren
zamantakewa ba.
Ita ma
Nafisa, U.D. (2016),[3] a kundin bincikenta mai
taken: "Sana'o'in Ga-aiki na Matan Hausawa da Gudunmuwarsu Wajen Tattalin
Arzikin Matan Hausawa" Manazarciyar ta yi ƙoƙari wajen bayyana wasu daga
cikin sana'o'in mata kamar ƙuli-ƙuli da saƙa, da Ɓula da Talla da Daddawa da
kitso da Adashe da kiwon kaji da awaki da sauransu. Tare da ma'anonin sana'o'in
da kuma muhimmancinsu da yadda ake gudanar da su. Wannan aiki yana da alaƙa da
namu aiki ta fuskar tattalin arziki. Bambancin da ke tsakanin nata aikin da
namu aikin shi ne: Nata aikin ya keɓanta ne a kan matan Hausawa, yayin da
wannan aiki ke magana a kan garin Mayanci.
Wani
bambancin da ke tsakanin nata aikin da wannan aiki shi ne: Wannan aiki bai
tsaya a kan tattalin arziki kaɗai ba, don kuwa ya taɓo har da tasiri da
sauye-sauyen zamantakewa, yayin da nata aikin bai taɓa wannan ɓangaren ba.
2.1.2 BUGAGGUN LITTATTAFAI
Akwai
Wallafaffun littattafai da dama masu alaƙa da wannan aiki. Daga ciki akwai
littafin:
Alhassan H.
Da wasu (1982),[4]
a cikin littafinsa mai suna "Zaman Hausawa". Lagos. Islamic
Publication Bureau. Marubutan sun yi ƙoƙarin kawo wasu sana'o'in Hausawa waɗanda
suka haɗa da noma da ƙira da fawa da farauta da kiwo da saƙa da kaɗi da rini da
fatauci da sarautu da muƙamai da sauransu.
Aikin nasu
yana da alaƙa da wannan aiki, ta fuskar tattalin arziki, bambancin da ke
tsakanin nasu aiki da wannan aiki shi ne: Nasu aikin na magana ne a kan Hausawa
baki ɗaya, yayin da wannan aiki na magana ne a kan tasirin magurzar auduga a
garin Mayanci, wato ya keɓanta ne a kan wannan gari na Mayanci.
B.U.K (1981),[5] a wannan littafi da ta
rubuta mai suna: Rayuwar Hausawa. Acikin littafin an yi ƙoƙarin bayyana ma'anar
Aure da muhimmancinsa da shugabancin a gida. Wannan aikin yana da alaƙa da
wannan ta fuskar zamantakewa. Bambancin da ke tsakaninsa da wannan aiki shi ne:
Wannan aiki bai tsaya a kan zamantakewa kaɗai ba ya taɓo har da ɓangaren
tattalin arziki, yayin da nata aiki ya tsaya ne a kan rayuwar Hausa ne kawai ta
fuskar zamantakewa. Wannan zai taimaka wajen gudanar da wannan aikin.
Garba, U.G.
(2012),[6]a littafinsa mai suna:
Bukukuwan Hausawa. Marubucin ya yi ƙoƙari ƙwarai da gaske don kuwa ya yi magana
a kan sana'o'i daban-daban kama daga fatauci da noma da farauta da gini da
wanzanci, da sauransu. Wannan aiki yana da alaƙa da namu aiki ta fuskar
tattalin arziki. Bambancin da ke tsakanin namu aiki da nasa aiki shi ne: nasa
aiki na magana ne a kan Hausawa baki ɗaya, yayin da wannan aiki kuwa ya keɓanta
ne a kan wasu Hausawa, wato tasirin magurzar auduga a garin Mayanci. Wani
bambanci da ke a tsakaninsu shi ne wannan aiki bai tsaya a kan tattalin arziki
kaɗai ba, ya taɓo harda zamantakewa, yayin da nasa aiki kuwa ya tsaya ne a kan
tattalin arziki kaɗai.
2.1.3 MUJALLU DA MAƘALU
Akwai
mujallu da maƙalu da dama masu alaƙa da wannan bincike kamar haka:
Farfesa
Dadari (2018) a maƙalarsa mai taken: "Auduga ta fi kowane Amfanin Gona
Samar da Aikin Yi A Duniya" wadda ya gabatar a wajen wani taron duniya,
kan bunƙasa noman auduga da ƙungiyar ƙasashen musulmai ta duniya OIC, ta shirya
a ƙasar Turkiya. Farfesa ya yi ƙoƙari ƙwarai da gaske Wajen bayani a kan
bunƙasa noman auduga musamman a ƙasashen da musulmai suka fi yawa. Wannan aiki
yana da alaƙa da namu aiki ta fuskar bunƙasa noman auduga. Bambancin da ke
tsakanin nasa aiki da namu aiki shi ne: namu aiki yana magana ne a kan tasirin
magurzar auduga a garin Mayanci, shi kuma nasa aiki ya tsaya ne a kan bunƙasa
noman auduga a ƙasashen musulmai.
Maryam, M.Y.
(2015),[7] a maƙalarta mai taken:
"Sana'o'in Hausawa na gargajiya da tasirinsu a zamananci" wadda ta
gabatar a cikin mujallar garkuwan Adabin Hausa. Marubuciyar ta yi ƙoƙari ƙwarai
da gaske Wajen fito da sana'o'in Hausawa na gargajiya kamar noma da kiwo da
fatauci da saƙa da ƙura da jima da sauransu. Wannan aiki yana da alaƙa da namu
aiki ta fuskar tattalin arziki. Bambancin da ke tsakanin namu aiki da nata aiki
shi ne: Nata aiki na magana ne a kan sana'o'in Hausawa na gargajiyar Bahaushe
baki ɗaya, yayin da namu aiki yake magana a kan tasirin magurzar auduga a garin
Mayanci.
Shi kuwa Dalijan,
B.M. (2016),[8]
a maƙalarsa mai taken. "Zamantakewar Hausawa a jiya", wadda ya
gabatar a cikin mujallar Argungu Journal of Language Studies, marubucin ya yi
ƙoƙari ƙwarai da gaske Wajen bayani a kan zamantakewar Hausawa ta fuskar iyali
da tasirin iyali ga Hausawa da zamantakewar iyali a aikin gona, da zamantakewar
Hausawa a zaman gandu, da zamantakewa ta fuskar zumunta, da zamantakewa ta
fuskar maƙwabtaka, da sauransu. Wannan aiki yana da alaƙa da namu aiki ta
fuskar zamantakewa. Bambancin da ke tsakaninsu shi ne: wannan aikin yana magana
ne a kan zamantakewar Hausawa gaba ɗaya. Yayin da namu aiki ke magana a kan
tasirin magurzar auduga a garin Mayanci.
2.2.1 HUJJAR CIGABA DA BINCIKE
Bincike a
kan "Tasirin Magurzar Auduga A Garin Mayanci" Yana da hujjar da za a
cigaba da shi. Hakan ya tabbata ne bayan aiwatar da bitar ayyukan magabata da
aka yi, da sauran ayyukan da suka gabaci wannan bincik. Ba shakka masana da
dama sun yi rubuce-rubuce a kan magurzar auduga da sauran abubuwan da suka
danganta da ita. Ɗalibai ma sun rubuta kundaye daban-daban. Amma duk da haka
wannan bincike yana da mashiga da hujjar da za a cigaba da shi domin ba a ba shi muhimmanci ba a baya sosai.
NAƊEWA
Wannan babin
ya fara ne da gabatarwa tare da bayyana irin ayyukan da aka yi bita a binciken
da ya gabata, domin waiwaye kan ayyuka masu alaƙa da wannan aiki da suka haɗa
da, kundayen bincike, bugaggun littattafai, mujallu da maƙalu, sai kuma hujjar
cigaba da bincike, daga ƙarshe babi yazo da naɗewa.
BABI NA UKU
3.0 SHIMFIƊA
A wannan babi
za a yi ƙoƙarin nazartar tarihin magurzar auduga a garin Mayanci da ma'anar
auduga da ire-iren auduga da wuraren da magurzar auduga ta yi tasiri da ma'anar
tattalin arziki da hanyoyin tattalin arziki da noma da kiwo da kasuwanci.
3.1 TAƘAITACCEN TARIHIN GARIN MAYANCI
Garin Mayanci
ya kafu a shekara ta 1825, ƙarƙashin jagorancin Na'ali Damamisau da jama'arsa,
waɗanda suka fito daga wani ƙauye da ake kira Birnin Fulani da ke Maru. Sun ya
da zango a wani wuri da ake kira Garagin Yahaya da ke yankin ƙaramar hukumar
Talatar Mafara ta yanzu tare da dabbobinsu, daga baya suka koma Mayanci a
shekarar 1825[9]
Kafin kafuwar
Mayanci ana kiranta da suna "Mayauta" wato wurin yini, ita wannan
Mayautar wuri ne da ake kiwon dabbobi, kuma akwai namun daji a wannan wurin da
sauransu. Bayan Na'ali Damamisau da jama'arsa sun dawo garin Mayauta (Mayanci),
da yake lokacin yaƙe-yaƙe ne na kare kai da iyali, Na'ali ya yi nasarar kashe
zakin da ya addabe su wanda an ce da zakin ya yi wata ƙara lokacin mutuwarsa
har mutanen Murai sai da suka ji ƙararsa. Bayan sun sami kwanciyar hankali ne
suka canza wa wannan gari suna daga Mayauta zuwa mayanci.[10]
Kafuwar garin
Mayanci daga 1825 zuwa yanzu an yi sarakuna goma sha bakwai, ga su kamar haka
tare da shekarun da suka yi mulki:
1. Na'ali Damamisau 1825-1847
2. Ba'atsoro Buba Ɗan Na'ali 1847-1866
3. S/Kanoma Zaki 1866-1882
4. Rafi Bawa 1882-1890
5. Doshiro Gajere mai dubara 1890-1904
6. Muhammad Bube 1904-1916
7. Ɓaidu kutsa Gatan Mani 1916-1924
8. Ɓawo zarumi 1924-1936
9. Dodo El-Umar 1936-1939
10. Tsoro Mai Taƙama 1939-1941
11. Mai Yaƙi Muhammad 1941-1951
12. Ibrahim Maru 1951-1959
13. Baƙo Tsoho 1959-1963
14. Bube Abubakar Maru 1963-1967
15. Abdullahi Ibrahim Maru 1967-1971
16. Alh. Muhammad Mai Nasara 1971-1980
17. Alh. Ƙasimu Atiku Liman.[11] 4/6/1980-
3.2 TAƘAITACCEN TARIHIN
MAGURZAR AUDUGA TA GARIN MAYANCI
Farkon
magurzar auduga ba Mayanci aka kafa ta ba an kafa ta ne a Moriki ta jihar
Zamfara; A Moriki ba a noman sasai don haka, wurin bai dace ba, sai Turawa suka
sake dubawa inda ƙasa mai kyau data dace da noman auduga, sai suka ga Mayanci
ya kamata sai suka ɗauko ta daga Moriki suka kawo ta garin Mayanci.
3.3 MA'ANAR AUDUGA
Auduga wata
tsiro ce da ake nomawa a gona wadda tana da matuƙar amfani sosai domin kuwa
yawancin sutura (tufafi) daga auduga ake yin ta.
3.4 IRE-IREN AUDUGA
1. Audugar pima: Ita ce auduga mafi kyau a duniya,
tana da zare mai tsawo da kuma taushi da ƙarfi.[13]
2. Audugar upland: Ita wata auduga ce mai ƙaramin
zare, ana kuma amfani da ita wajen samar da kaya masu inganci.
3. Audugar Misira (Egypt): Ita auduga ce kamar ta
pima, tana da zare mai tsawo sai dai ba ta da laushi ƙwarai.
3.5 YADDA AKE NOMA AUDUGA
Da farko idan
za ka noma auduga za ka fara yin kaibe ga gonar, idan an yi kaibe sai a zo ayi
huɗa bayan an gama huɗa sai ayi shuka irin da ake yin shukar da shi ne (Gurya),
bayan ɗan lokaci sai aje a nome hakin da ya fito bayan an nome sai a yi feshin
magani kuma a watsa taki, ana iya yi mata noma biyu zuwa uku. Idan ta girma tana
yin tsawo duk ice guda kana iya samun ɗiya fiye da hamsin, idan ta ƙosa sai
ƙululun ya buɗe sai a sa hannu ana cire kaɗar ana sa wa cikin buhu saboda ba a
so ta yi dauɗa, cirewar da ake yi da hannu shi ne ake kira taɓi. Ana fara noman
auduga daga watan Mayu, ana ibar ta har a yi taɓin ta watan Oktoba. [14]
3.6 WURAREN DA TURAWA SUKA KAWO
INJININ GURZAR AUDUGA A NAJERIYA
1. Mayanci
2. Gusau
3. Funtua
4. Kwanta gora
5. Zaria
6. Malumfashi
7. Gombe
8. Jos
3.7 MA'ANAR TATTALIN ARZIKI
Masana da
dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma'anar tattalin arziki, daga ciki
akwai:-
CNHN
(2006:432 da 19) ya bayyana waɗannan kalmomi (tattali da arziki) da
cewa: "Tattali" na nufin tanadi ko kula ko adana wani abu ko ajiye
wani abu don yin amfani da shi nan gaba. A hannu ɗaya kalmar
"arziki" na nufin tajirci ko dukiya ko samu ko hali ko kuɗi
ko wadata ko sukuni ko daula ko abin hannu ko hannu-da-shuni. Duba daga waɗannan
ma'anonin kalmomi guda biyu, idan aka gwama su wuri ɗaya watau "tattalin
arziki", waɗannan kalmomin na iya ɗaukar
ma'anar abin da mutum ya mallaka tare da ririta shi da kuma amfani da shi ta
hanyar da ta dace a cikin basira.
Ibrahim,
M.S. (1982:7),[15]
ya bayyana cewa: "Tattalin arziki tsari ne na sarrafa albarkatun ƙasa da
sauran ni'imomin da Allah ya yi wa ɗan Adam domin samar da
muhimman abubuwan buƙata da rarraba su ga jama'a masu buƙata".
A ra'ayin
Umar, M.B. (1983:5),[16]cewa ya yi: "Tattalin
arziki tsari ne na inganta da bunƙasa hanyoyin shigar da kuɗi
da sauran abubuwan buƙatun ɗan Adam musamman abinci da sutura da
muhalli". Wannan ma'anar nuni take da cewa, duk wata hanya ta samun kuɗin
shiga da samar da abubuwan more rayuwa ita ce hanyar tattalin arziki".
Dalijan ya
ruwaito Auta na cewa: "Tattalin arziki tsari ne na sarrafa wasu abubuwa
domin samun abubuwan buƙatan rayuwa". (Dalijan, B.M.2012:39).[17]
Shi kuwa
Rambo, (2017) a wata maƙala da ya gabatar mai taken: "Gudunmuwar Sassaƙa
ga bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Kabi" da kuma "Gudunmuwar Sana'ar noma wajen haɓaka
tattalin arzikin Hausawa" a Jami'ar Usman Ɗan Fodiyo, Sakkwato ya ruwaito
Shinkafi, (2016:6) da Smith (1976), da mill (1844), da Marshall (1890) da J.B.
(1802) da Robbins (1932) da kuma Umar (1983) duk sun aminta da cewa:
"Tattalin arziki gaba ɗayansa abu ne da ya tattaru ga
ƙoƙarin kula da albarkatun ƙasa da sauran ni'imomin da Allah ya yi wa mutum ta
yadda za su bunƙasa su sarrafa su, da samar da abubuwan da mutum ke bukata
domin rayuwar jama'a ta gudana cikin sauƙi".
Kabakawa
U.B. (2012:37),[18]cewa
ya yi: "Tattalin arziki ya ƙunshi tsarin samar da abubuwan buƙata da yadda
ake rarraba su tsakanin jama'a da kuma sigar yadda ake amfani da su".
A ra'ayin
Auta A.L.(2006:196),[19] ya bayyana kalmar
tattalin arziki da cewa: "Abubuwa guda uku ne suka zama shika-shikan ginuwar
tattalin arzikin Bahaushe da suka haɗa da sana'o'i da kasuwanci
da ƙwadago, ga sarakuna kuma a dauri ga haraji da jangali da sauransu".
Bisa ga waɗannan
ma'anoni da ke sama, ana iya cewa, sha'anin tattalin arziki lamari ne da ya jiɓinci
duk wata hanya ta cigaban rayuwar al'umma baki ɗaya. Wannan kuwa ya shafi
yanayin walwalarsu ta fuskar iliminsu da siyasarsu da kasuwancinsu da dai
sauransu.
3.8 HANYOYIN TATTALIN ARZIKI
Akwai hanyoyin tattalin arziki da dama , sai dai a wannan aikin namu mun
kasa hanyoyin tattalin arziki zuwa gida biyar, wato noma, kiwo, kasuwanci,
Sana'o'i, kamar sana'ar Jima, Sana'ar farauta, sana'ar Tuwo, sana'ar katifa da
filo da kuma aikin gwamnati a matsayin hanyoyin tattalin arziki.
3.9 SANA'A
Sana’a kalma
ce da aka aro ta daga Larabci wadda a larabcin ta ke nufin aiki, a Hausa kuma
take daukar ma’ana ta samar da wani abin amfani ta hanyar hikima a Hausance.
Misali, sana’ar Ƙira, Jima, Noma, Wanzanci, Fawa, da sauransu.
Masana da dama
sun bayyana ra'ayoyinsu akan abin da ake nufi da sana'a. Daga cikin masana
akwai Galadanci M.K.M da wasu (1992) sun bayyana ma'anar sana'a da cewa
"Sana'a ita ce abin da mutum yake yi don samun biyan buƙatun rayuwarsa ta
yau da kullum.
Ɗan hassan
Sanyinna da wasu (2017) suna ganin cewa" sana'a hanya ce ta ba ni gishiri
in ba ka manda da kuma hanyar mai da taro sisi cikin hikimar, azanci da basirar
da Allah ya albarkaci bil'adam da ita, wadda ake gudanarwa tsakanin jinsin
bil'adama da ke raye a doron ƙasa.
Shi kuma
Sharifai (1990) yana ganin cewa sana'a ita ce "duk wata hanya da mutun
yake bi don nema ko samun abinci, abinci yana zuwa ta hanyar kuɗi ko wani abin
da rayuwa za ta dogaro da kai. Kuma wannan hanya, ta zama wadda aka gada ce tun
iyaye da kakanni, ba wata baƙuwar al'umma ce ta kawo ta ba".
A ra’ayin
Yahaya, I.Y, da Gusau, S.M. da Yar aduwa, T.M (2001:48) sun bayyana cewa:
"Sana’a wata aba ce wadda mutum ya kan yi da nufin samun abin masarufi don
gudanar da harkokin rayuwa. Aba ce wadda ta danganci tono albarkatun ƙasa da
sarrafa hanyoyin kimiya da fasaha da
sayarwa da ciniki da sauransu".
SANA'AR JIMA
Dangane da
wannan ma'ana ta jima an samu masana da suka yi ƙoƙarin bayyana ma'anar jima
daga ciki akwai:
Yahaya I.Y
(1987) ya bayyana ma'anar jima da cewa jima na nufin sarrafa fatun kowaɗenne
irin dabbobi dangane da tsaftace su, tsarkake su, don karkatar da su ta hanyoyi
daban-daban na moriyar al'umma da buƙatu na yau da kullum na ɗan'adam
SANA'AR FARAUTA
Habib
Alhassan da wasu (1982) sun bada ma'anar farauta da cewa: "Itace sana'ar
kama naman daji don ƙarin abinci da kariya.
Farauta ita
ce sana'ar kama naman daji don ƙarin abinci da kariya. (Zurmi, 2010) inda ya
cigaba da bayyana cewa farauta kusan itace sana'a ta farko da ɗan'adam ya fara
da tunanin neman abinci da kare kai.
ƘANA NAN SANA'O'I
Ƙana nan
sana'o'i masu sai da dawo-dawo masu sai da gala masu sai da tuwo masu sai da
ruwa a lokacin da ana aikin gurzar auduga zaka cimma bakin ma'aikatar kowane
irin abinci zaka samu, wasu masu abincin daga wasu garuruwa suke zuwa su kafa
runfunansu na sana'a, mafiya yawan wa'inda zaka gani sabon garin Mayanci
dalilin zuwan su wannan wurin shi ne kafuwar magurzar audugar ta garin Mayanci.
SANA'AR KATIFA
Sana'ar
katifa, ana samun damejin auduga wadda ke fita cikin injin, kuma ana samun ta a
masaƙa wato idan aka cire auduga wadda ke yin zare sai a fitar da wadda ba ta
da kyau wato wadda ba ta aiki wurin saƙa ita ce ake sana'ar filo da katifa da
ita.
3.10 NOMA
Noma na duƙe
tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar. Wannan shi ne kirarin sana'ar
noma. Sana'ar noma ta bambanta da sauran sana'o'in Hausawa. Ba kamar sauran
sana'o'i ba da kusan kowace sana'a akwai mutane da aka sani da ita, noma
sana'ar kowane mahaluki ce. Duk wanda aka ga yana sana'ar fawa ko sana'ar ƙira
to lalle ya gada ne daga gidansu. Amma noma sana'ar kowa da kowa ce a al'ummar
Hausawa. Da sarakai da malamai da attajiri da talakawa kowa ya gaji sana'ar noma.
(R.M Zarruk da wasu, 1987).
Shi kuwa
Gwanki (2016), ya bayyana ma'anar noma da cewa: "Noma wata hanyar sana'a
ce domin samun abinci da kuɗin shiga". Ya ci gaba da cewa : " Noma
wata babbar hanya ce ta samun ƙaruwar tattalin arziki da al'umma suka raja'a a
kanta". A tamu fahimta kuwa, Noma wata hanya ce ta samun abinci da kuɗin
shiga domin dogaro da kai, da kariyar wulaƙanci.
NOMAN AUDUGA
Noman auduga
sana'a ce mai matuƙar muhimmanci ga rayuwar 'yan Najeriya musamman manomin
auduga ko mai sayar da irin auduga ko mai fataucin auduga da masu masaƙu da
masana'antun yin sutura.
Farfesa
Umar, ya ce noman auduga abu ne da ke taimakawa wajen biyan buƙatun 'yan'adam
saboda ɗan'adam yana buƙatar abinci da matsugunni da sutura, kuma auduga tana ɗaya
daga cikin abin da ke biyan buƙatar ɗan'adam ta fannin sutura, kuma a gidaje ma
auduga na biyan buƙata. Saboda mafi yawa daga cikin wuraren da ake tsugunar da
'yan gudun hijira kamar su tamfol- tamfol da auduga ake yin su.
Noman auduga
ya zama wajibi a duniya domin shi ne yake bayar da kaya mafi daraja a duniya.
Auduga tana bayar da ayukkan yi fiye da kowanne kayayyakin amfanin gona, a
duniya. Domin manyan masuƙu sun dogara ne da auduga a duniya. Domin masaƙa ɗaya
za ta iya ɗaukar mutum dubu hamsin aiki. Bayan ga masu sayar da kayayyakin da
masaƙun suke sakawa da dillalai da masu dako da teloli duk waɗannan guraben
ayyuka suna tasowa ne daga noman auduga.
Noman auduga
tsohon lamari ne ana yin sa, tun lokacin da ba a iya gurzar da inji. Mahaifanmu
shekara hamsin da suka wuce, sukan gurza auduga, su fitar da irinta daban, ita
daban su markaɗe ta, a yi ta hanyar gargajiya daga baya aka samu na'urar
zamani. A baya-bayan nan ne aka samu taɓarɓarewar noman, inda ya yi ƙasa,
saboda matsalolin rashin samun iri ingantacce. Bayan farashin ta ya yi ƙasa uwa
uba ga rashin tallafi daga gwamnati.
3.11 KIWO
R.M. Zarruk
da wasu (1987),[20]
sun bayyana Ma'anar kiwo da cewa: "Kiwo na kowa da kowa ne, wato ba a
gadonsa. Kuma shi kiwo ba manya manyan maza kaɗai aka san su da shi ba,
har ma mata da yara suna sana'ar kiwo. Akwai kiwon dabbobi kamar su akuya da
tunkiya da raƙumi ko shanu da doki da sauransu. Wasu sukan tara garke na
dabbobi kamar awaki, ko tumaki, ko shanu ko raƙumma da dai sauransu. Wasu kuma
kan tanadi kiwon kaji ko agwagi ko kuma zabi. Idan suka yi yawa akan tanadi mai
aikin kiwo musamman lokacin da damina ta faɗi aka yi shuka. Amma idan
rani ya yi kowa kan saki dabbobinsa domin babu tsoron za su shiga gonakin
mutane su yi ɓarna. Su kuma kaji da agwagi babu wani abin damuwa
wajen kiwonsu, domin a nan gida ko kuwa sauran gidaje na unguwar suke kiwonsu
ko ma a kwararo.
Alhassan da
wasu (1982),[21]
cewa suka yi: "Kiwo shi ne tsare dabba, ko tsuntsu da tattalinsu don a
mallake su, saboda wani amfani ga mutum". Ya ci gaba da cewa: "Kusan
kowane gida ana yin kiwo, don da wuya a sami gidan da ba a kiwon dabbobi ko
tsuntsaye a ƙasar Hausa".
A tawa
fahimta kuwa, kiwo na nufin tsare wata dabba kamar akuya, shanu, kare, jaki,
doki da sauransu tare da kula da su domin wata buƙata.
Dangane da
ire-iren kiwo da yadda ake yinsa kuwa, Alhassan ya kawo ire-iren kiwo zuwa gida
uku kamar haka:
1. Kiwon isa: shi ne kiwon dokin hawa, da alfadari, waɗanda
masu gari da wasu attajiran gari suka fi yi.
2. Kiwon fatauci: shi ne kiwon da ake yi na shanu, da
tumaki da awaki, da tsuntsaye, watau kiwon da ake yi ana ware wasu ana sayarwa
don biyan buƙata.
3. Kiwon raha: shi ne kamar kiwon kare, da kyanwa, ko
zomayen gida, ko tsuntsaye, masu ban sha'awa, kamar ɗawisu, da aku da kanari da
sauransu.
Ya ci gaba
da cewa: "Kowa shi ke kiwonsa da kansa, ko kuma ya sa yaransa, sai dai a
wasu wurare, idan awaki da tumaki suka yawaita, a kan yi yarjejeniya da asako
(mai kiwo), watau wanda kowa da kowa zai sako masa awakinsa ko tumakinsa, don
ya kiwata masa su. Aikin asako (ga kiwo) aiki ne jawur, domin idan an fito tun
daga fitowar rana har faɗuwarta yana ta fama da shawo kan
dabbobi, ka da su shiga gonakin mutane. Sa'annan ga zafin rana da ƙaya.
Ana ba shi
ladan aikinsa, a cikin wani ƙayyadadden lokaci ne, da kuɗi
ko da abinci, ko ma da 'ya'yan dabbobin da yake kiwata wa jama'a.
3.12 KASUWANCI
Masana da
dama sun bayyana fahimtarsu dangane da abin da ake kira kasuwanci, daga ciki
akwai:-
R.M. Zarruk
da wasu (1987),[22]
sun bayyana ma'anar kasuwanci da cewa: "A saya a sayar shi ne
kasuwanci". Wato a nan mutum ya fitar da kuɗinsa ya sayi ƙadara sannan
wani lokaci ya fitar da wannan ƙadarar ya sayar, shi ne kasuwanci. Mai irin
wannan harkar shi ake kira ɗan kasuwa, idan mace ce kuwa akan
kira ta 'yar kasuwa'.
Kasuwanci a
cewar su, ba ya yiyuwa sai da jari. Jari shi ne ake amfani da shi don sayen
ƙaddarar da za a sayar. Ɗan kasuwa dole ya riƙe jari domin ya riƙa jujjuya shi.
Wato ya kan yi amfani da jarin domin sarin kayan sayarwa. Sannan idan ya sayar
da su, sai ya ƙidaya ya ga irin ribar da ya samu. Amma idan ɗankasuwa
ya dinga faɗuwa a harkar saye da sayarwarsa jarinsa kullum raguwa
yake har ma ya kai ga halin jarin ya ɓata, irin wannan hali akan
ce mutum ya kare. Wato ba shi da sauran jari a hannunsa.
A tawa
fahimta kuwa, kasuwanci na nufin saye da sayarwa ko dai ta hanyar amfani da kuɗi
ko kuma sarrafa wani abu a sayar domin samun kuɗin shiga da biyan buƙatun
yau da kullum. Abin nufi a nan shi ne kasuwanci na yiyuwa ne ta hanyar amfani
da kuɗi ko ƙirƙiro da wata hanya wadda ka ke samun kuɗin
shiga ta hanyar bani gishiri in baka manda.
Dangane da
yadda ake kasuwanci kuwa, shi ne kasuwanci ba ya yiyuwa sai da jari, domin idan
baka da jari to kasuwanci baya yiyuwa. Kasuwanci kan faru ne ta hanyar ciniki
da sallama, tsakanin mai saye da mai sayay. Haka kuma ana kasuwanci ta hanyar
karɓar
kaya daga babban dila idan mutum ya sayar sai ya cire kuɗin
dila ya kai masa sauran ribar kuwa nasa ne.
Akwai
ire-iren kasuwanci da dama kamar haka:-
1. Kasuwancin sakai:- Shi ne kasuwancin da ya shafi
sayar da abinci kamar gero, dawa, masara, shinkafa, dankali da sauransu.
2.
Kasuwancin Tireda:- Shi ne kasuwancin da ake yi ta hanyar sayar da abubuwa
kamar haka: Gishiri, magi, sabulun wanka da na
wanki da dai sauran makamantansu.
3. Kasuwanci Tugu:- Kasuwanci ne na sayen dabbobi,
sannan a sayar. Ana kiran mai wannan kasuwanci da suna ɗan tugu ko mai tugu.
3.13 NAƊEWA
Wannan babin
ya fara ne da gabatarwa tare da bayyana taƙaitaccen tarihin garin mayanci da
kuma tarihin kafuwar magurzar auduga a garin Mayanci, ma'anar auduga, ire-iren
auduga, ma'anar tattalin arziki, hanyoyin tattalin arziki, noma, kiwo,
kasuwanci daga ƙarshe babi yazo da naɗewa.
BABI NA HUDU
4.0 SHIMFIƊA
Tasiri wata
alama ce ko yanayin wani abu a kan wani abu, ta hanyar fitowa fili yadda za a
iya ganinsa ko a taɓa shi ko a ji shi a jiki a sanadiyyar mu'amala ko
zamantakewar abu a tare da wani.
MAGURZAR AUDUGA TA MAYANCI
DA TASIRINTA
4.1 MA'ANAR TASIRI
Masana da
dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma'anar tasiri.
Maryam, M.Y.
(2015):[23] Ta ce tasiri na nufin
al'ada da wani yakan yi da can ba a san shi da ita ba. A taƙaice tasiri na
nufin shaƙuwa da kan faru a sakamakon hulɗa, ko zamantakewa ko wata
mu'amala ta yau da kullum wadda sakamakon hakan sai ta haifar da wata baƙuwar
al'ada.
Uwaisu
(2009): Ya bayyana kalmar tasiri da cewa asalinta daga harshen Larabci aka
arota wadda ke nufin mamaye wani abu ko wata al'ada. A Hausa kalmar tasiri tana nufin yadda wani
abu ya mamaye ko ya canza wani abu ko kuma al'adar da wani yake yi da da can ba
a san shi da ita ba.
4.2 MAGURZAR AUDUGA TA MAYANCI DA
TASIRINTA
Magurzar
auduga ta garin Mayanci ta yi tasiri a fannin wurare da dama amma ga wasu daga
cikin su kamar haka:
1. Tasiri a fannin yanayin al'adu.
2. Tasiri a fannin Kiwo.
3. Tasiri a fannin Ɗauka ka darajar garin.
4. Tasiri a fannin Rage zaman banza.
5. Tasiri a fannin ƙarfafama manoma su noma auduga.
6. Tasiri a fannin hana zaman banza.
7. Tasiri a fannin Bunƙasa tattalin arzikin.
8. Tasiri a fannin Zamantakewa. da sauransu.
9. Tasiri a fannin kasuwanci.
10. Tasiri a fannin kyautatawa al'umma.
4.2.1 Tasiri a fannin yanayin al'adu. Kamin bayyanar
kamfanin na auduga yanayin rayuwar su ta auratayya, noma, kiwo, da sauransu.
Hatta da nau'i na sunaye da yanayin rayuwa na gaba ɗaya irin canje-canjen da
aka samu sabbi sanadiyyar zuwan baƙi, wannan babban tasiri ne ga mutanen garin
Mayanci.
4.2.2. Tasiri a fannin Kiwo. A wancen lokacin Fulani
da Hausawa abin da kawai suka dogara da shi kamin zuwan magurzar auduga a garin
Mayanci shi ne ciyawa, Dussa, da sauransu, amma lokacin da aka samu magurzar
auduga sai kiwo ya ƙara bunƙasa saboda amfani da ake yi da an gurya ana ciyar da dabbobi da shi, sabo da haka
idan ka kiwata "sa" da an guryan nan ya zama bijimi in ka kai shi
kasuwa maimakon in ya shekare ƙila a
saye shi fam guda a wancan lokacin kana iya sayar da shi fam uku ta sanadiyyar
kiwata shi da 'yan guryannan da aka yi. Kenan an sami tasiri na amfani da
wannan sinadari na wannan 'ya'yan gurya ga dabbobi.
4.2.3 Tasiri a fannin Rage zaman banza. Idan muka yi
la'akari kafin a yi wannan kamfanin na magurzar auduga na garin Mayanci mutanen
garin daga noma sai kiwo sai tafiya wurin ci rani suke yi, amma lokacin da
wannan magurzar ta zo garin Mayanci sai ta samar masu da aikin yi, suka daina
zuwa ci rani ta sanadiyyar aikin yi ya samu a garinsu.
4.2.4. Tasiri a fannin ɗaukaka darajar garin Mayanci.
Magurzar auduga ta yi tasiri wurin ɗaukaka darajar garin Mayanci, a lokacin nan
arewa maso yamma babu wani gari da ake gurzar auduga in ba Mayanci ba, saboda
haka a wancen lokacin garin Mayanci ya bunƙasa ƙwarai da gaske domin wasu ma
mazauna garin Mayanci dalilin gurzar auduga ya kawo su har suka gidandance a
garin.
4.2.5. Tasiri a fannin ƙarfafama manowa su noma
auduga. Zuwan wannan magurzar auduga a garin Mayanci, ta yi tasiri ga manoman
auduga domin a wancan lokacin kyauta ake bada irin auduga na shuka. Wani ɗaki
ne ake buɗewa da ake ajiyar irin auduga da lokacin noma ya yi sai a buɗe wannan
ɗaki da ka zo ka shiga ka ɗebo wanda zai isheka shukawa, kyauta ba tare da ka
bada ko sisi ba. Kenan zuwan wannan magurzar auduga ta yi tasiri ƙwarai da
gaske wurin ƙarfafama manoma su noma auduga, wannan ya faɗa bunƙasa noman na
auduga.[24]
4.3. MA'ANAR ZAMANTAKEWA
Masana da
dama sun bayyana ra'ayinsu dangane da ma'anar zamantakewa kamar haka:
Dalijan B.M.
(2016),[25] a wata maƙala da ya
gabatar mai taken "Zamantakewar Hausa a jiya" ya bayyana ma'anar
zamantakewa da "Asalin kalmar zamantakewa daga zama ne. wato abin da ake
nufi anan shi ne zama tare ko dai ta fuskar zumunta ko maƙwabta ko sana'a ko
wurin aiki ko kuma ta sauran hidimomin duniya da sauransu". Ya ci gaba da
cewa: "Zamantakewa kuma na iya nufin halin zaman tare na al'ummar Hausawa".
Zamantakewa
na nufin kamar yadda sunan ya nuna daga kalmar zama wato abin nufi a nan shi ne
zaman tare, ya Allah ko dai ta fuskar zumunta ko maƙwabtaka, ko kuma ta fuskar
yanayin sana'a, ko da yake ma'anar takan iya wuce wannan idan aka yi la'akari
da ire-iren dangantakar da ake samu tsakanin al'umma, misali Zamantakewa
tsakanin shugabanni da mabiyansu, malamai da almajiransu, mata da mazajensu,
iyaye da yaransu.
4.3.1 IRE-IREN ZAMANTAKEWA
Akwai
ire-iren Zamantakewa da dama a garin Mayanci, za mu yi bayani a kan wasu daga
ciki.
1- Zamantakewar Aure
2- Zamantakewa Tsakanin Malami Da Ɗalibai
3- Zamantakewar Zumunta
4- Zamantakewar Maƙabta
5- Zamantakewa Tsakanin Shugabanni Da Talakawa.
4.3.1.1 ZAMANTAKEWAR AURE
Aure dai wata
alaƙa ce halattacciya, wadda ta halatta zaman tare tsakanin ma'aurata guda
biyu, wato miji da mata. Ana yinsa ne saboda abin da aka haifa ya sami asali,
da mutunci da kiyayewar uwaye. (Gusau,2012).
A
Zamantakewar aure, zama ne na taimakekeniya tsakanin mata da miji, ta hanyar da
mata ke yi wa mijinta biyayya tare da tattala duk wani abu da ya kawo gida,
haka ma takan kyautatawa iyayen mijinta da dukkan 'yan'uwansa, shi kuma mijin
zai kiyaye dukkan haƙƙoƙin matarsa tare da kyautata mata da iyayenta da kuma
sauran danganta.
Wannan
magurza ta yi tasiri ƙwarai da gaske dangane da Zamantakewa aure, domin kuwa
baƙin da suka shigo garin Mayanci ta sanadiyyar zuwan magurzar auduga sun yi ta
yin auratayya tsakaninsu wanda sakamakon auratayyar nan ya zama dalilin yaɗuwar
iyali tsakanin su har suka zama abu ɗaya.
4.3.1.2 ZAMANTAKEWAR ZUMUNTA
Zumunta ita
ce a sami wata alaƙa ta jini a tsakanin 'yan'uwa. Waɗannan 'yan'uwa su ne ake
kira dangi a Bahaushiyar al'ada. Dangi kuwa su ne 'yan'uwa na kusa da na nesa.
Bahaushe mutum ne mai son Zumunci, har ma a cikin karin magana yana cewa:
"Zumunta a ƙafa take" wani lokaci kuma: "Ɗan'uwa rabin
jiki".
Magurzar
auduga ta garin Mayanci ta yi tasiri ƙwarai da gaske ɓangaren Zumunci, domin
kuwa baƙin da suka shigo ci rani saboda zuwan wannan magurzar har suka
gidandance a garin, mazauna garin na asali sun ɗauke su 'yan'uwan juna. Kenan
wannan magurza ta yi tasiri ƙwarai da gaske ɓangaren Zumunci.
4.3.1.3 ZAMANTAKEWAR MAƘWABTA
Maƙwabtaka na
nufin zama kusa a wajen muhalli na gida ko wajen sana'a ko kuma ta hanyar
ma'aikata (Daliban, 2016).
Ya ci gaba da
cewa: " Idan akwai zama mai kyau na maƙwabtaka, lalurar da ta shafi
maƙwabcinka tamkar kai ta shafa. Hasali ma akwai karin maganar da ta ce:
"Abin da ya taɓa hanci idanu ruwa suke yi". Sa'annan kuma an ce
maƙwabcinka a lahira shi ke ba da shedu ga maƙwabcinsa.
Idan muka yi
la'akari da irin wannan rayuwa ta maƙwabtaka, wannan magurza ta yi tasiri
ƙwarai da gaske dan gane da maƙwabtaka, domin ta haifar da abubuwa masu kyau,
kuma na alheri da ƙulla kyakkyawar dangantaka, kenan wannan magurza ta taka
muhimmiyar rawa wajen Zamantakewar maƙwabtaka. Idan akwai zaman lafiya da
kwanciyar hankali da aminci tsakanin maƙwabta, kowane irin alheri yana samuwa
ba a kan aikin gona kaɗai ba, har ma da dukkan sauran al'amurran rayuwar
duniya.
4.4 NAƊEWA
Wannan babi
ya fara ne da gabatarwa tare da bayyana ma'anar tasiri da kuma irin tasirin da
magurzar tayi ga mutanen garin Mayanci, ma'anar Zamantakewa, ire-iren
Zamantakewa, sauye-sauyen Zamantakewa, dalilan da suke haifar da sauye-sauye,
amfanin sauye-sauye, yadda za a magance matsalolin, daga ƙarshe babi yazo da naɗewa.
BABI NA BIYAR
5.0 SHIMFIƊA
Hausawa na
cewa "komi nisan jifa ƙasa zata faɗi", suka ƙara da cewa
"komi ya yi farko zai yi ƙarshe". Da wannan zantukan hikima nake
cewa, a wannan babi ne wannan bincike da aka gudanar a kan "Tasirin
magurzar auduga a garin Mayanci" ya zo ƙarshe. Wato a nan ne za a yi
taƙaitaccen bayanin yadda wannan bincike ya gudana. Da kuma irin abubuwan da
wannan bincike ya gano ko kuma ya cimmawa na sakamako
5.1 SAKAMAKON BINCIKE
A wannan
bincike da aka gudanar an fito da muhimman abubuwa a matsayin sakamakon wannan
bincike kamar haka:
1- Bincike ya gano muna cewa a lokacin da aka kafa
magurzar auduga a garin Mayanci kowa ya dogara da kansa ne, saboda haka bincike
ya gano muna cewa rushewar wannan magurza ya kawo taɓarɓarewar tattalin arziki
na rashin aikin yi ga mutanen garin.
2- Bincike ya gano muna irin yadda Zamantakewa take a
garin Mayanci jiya da kuma yadda take a yau, haka ma bincike ya gano muna
sauye-sauyen da aka samu na Zamantakewa a garin Mayanci da kuma amfanin
sauye-sauyen da kuma yadda za a magance matsalolin.
3- Bincike ya gano muna irin tasirin da magurzar
auduga tayi ga mutanen garin Mayanci har ma da baƙin da suka shigo ci rani
saboda zuwan magurzar auduga a garin Mayanci.
4- Wannan bincike ya gano muna cewa garin Mayanci ya
bunƙasa ne sanadiyyar zuwan magurzar auduga ta garin Mayanci.
5.2 SHAWARWARI
Shawara
muhimmiyar aba ce, Hausawa na cewa: "Mai shawara aikinsa ba ya ɓaci"
tabbas wannan karin magana haka take. Duk da kasancewar mu ɗalibai
masu nazarin harshen Hausa ba za mu rasa shawarwarin da za mu bai wa malamai da
'yan'uwanmu ɗalibai ba.
Shawara ta
farko ita ce ina ba hukuma da duk wasu masu ruwa da tsaki shawara a kan ya
kamata a farfaɗo da magurzar auduga ta garin Mayanci, saboda tana samarda aikin
yi tana samar da rage zaman banza ga ɗin bin matasa.
Shawara ta
biyu ita ce ina ba hukuma shawara da ta ƙara farfaɗo da noman auduga, domin ko
an farfaɗo da magurzar audugar ta garin Mayanci idan babu audugar da zasu
sarrafa abun ba zai yiyu ba.
Shawara ta
uku ita ce ina ba da shawara ya kamata a farfaɗo da masaƙu irin na garin Gusau
domin duk audugar da ake gurzawa a garin Mayanci ita ce ake sarrafawa a masaƙa
ta garin Gusau.
Shawara ta huɗu
ita ce ina ba hukuma shawara da 'yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a kan yanzu
zaman banza ya yi yawa tsakanin matasa, dan Allah su farfaɗo da magurzar auduga
ta garin Mayanci, saboda in aka farfaɗo da ita zata samar da aikin yi ga ɗimbin
matasa na garin Mayanci.
Shawara ta
ƙarshe ita ce zuwa ga gwamnati da tayi ƙoƙarin farfaɗo da wa'inna masana'antu
domin ƙara bunƙasa tattalin arziki na garin Mayanci dama ƙasa baki ɗaya.
Haka kuma ya kamata gwamnati ta daure ta riƙa ɗaukar nauyin wasu ɗalibai
tana tura su jami'o'i daban-daban domin yin nazarin harshen Hausa. Wannan zai
ba wa mutane sha'awar yin nazari a kan wannan fanni.
5.3 NAƊEWA
Dukkan yabo
da godiya sun tabbata ga Ubangiji Buwayayye, gagara misali, mamallakin kowa da
komai, wanda cikin ikonsa da yardarsa ya ƙaddaremu da kammala wannan bincike.
Haƙiƙa Bahaushe yana cewa: "Komai nisan dare gari zai waye", haka
"komai ya yi farko to tabbas zai yi ƙarshe".
A nan ne Allah
ya kawomu ƙarshen wannan bincike wanda muka gudanar domin cika wani sharaɗi
daga cikin sharuɗɗan wannan karatu namu na neman takardar shaidar digiri na
farko mai taken: "Tasirin magurzar auduga a garin Mayanci".
MANAZARTA
Alhassan, H. Da wasu (1982) "Zaman
Hausawa". Lagos. Islamic
Aliyu, (2010): "Zumunci a Jiya da Yau".
Kundin Digiri na Farko,
Sashen
Harsunan Najeriya da Afrika. Zariya: Jami'ar
Ahmadu
Bello. Argungu Journal of Language Studies
(2016).
Auta, A.L. (2006): "Tattalin Arzikin Al'umma da
Nazarin Sana'o'i
da
Kasuwancin Hausawa" a cikin Algaita Journal of
Current
Research in Hausa Studies. M.A.Z. Sani da Aliyu
Mu'azu da
Ahmadu Shehu, (Editoci). Zaria: Ahmadu Bello
University
Press Limited.
B.U.K. (1981): "Rayuwar Hausawa"
Morinson and Gibb Ltd,
London and
Edinburgh.
Bunguɗu, A.I. da Wasu (1999):
"Sana'o'in Kaɗi, Mazanƙwaila,
Tukanen
Laka na da da na Zamani". Kundin Bincike na
N.C.E.
Sashen Hausa. Sokoto, Shehu Shagari College of
Education.
Bunza, A.M. (2016): "Gadon Feɗe Al'ada." Lagos, Tiwal Nigeria
Ltd.
C.N.H.N. Kano, (2006) "Ƙamusun Hausa"
Zariya. Ahmadu Bello Dalijan, B.M. (2012) "Noma da Ginuwar Tattalin
Arzikin Hausawa
na
Gargajiya". Kundin neman digiri na biyu. Sashen
Harsunan
Najeriya. Sakkwato: Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Dalijan, B.M. (2016): "Zamantakewar Hausawa a
Jiya" A K.M. da
Sarki, A.U. da wasu
(Editoci) School of Language. Argungu,
Adamu Augie College of Education.
Garba, U.G. (2012): "Bukukuwan Hausawa".
Olfaith Prints Gusau.
Harsunan
Najeriya, Kano, Jami'ar Bayaro.
Ibrahim, M.S. (1982): "Tattalin Arzikin
Hausawa". Cibiyar Nazarin
Harsunan
Najeriya, Kano, Jami’ar Bayaro.
Ibrahim, Y.Y. da wasu (1992): "Darussan Hausa Don
Manyan
Makarantun Sakandare na 2". Ibadan; University Press Plc.
Ibrahim, Y.Y. da wasu (1992): "Darussan Hausa
Don Manyan
Makarantun Sakandare na 3”. Ibadan;
University press Plc.
Kabakawa, U.B. (2012) "Mahangar Makaɗan
Baka Dangane da
Tattalin Arzikin Hausawa. Kundin Digiri na
Biyu, Sashen
koyar da
Harsunan Najeriya. Sakkwato: Jami'ar Usmanu
Ɗanfodiyo.
Ka'oje, B.A. da Argungu A.I. (2016): "Sarauta a ƙasar
Hausa jiya
da
Yau". A cikin Argungu Journal of Language Studies, Utono, K.M. da Sarki,
A.U. da wasu (Editoci) School of Language.
Argungu,
Adamu Augie College of Education.
Maru, I.U. da wasu (2012): "Sana'ar Daddawa a
Jahar Zamfara".
Kundin
Bincike na NCE, Sashen Hausa. Maru, Kwalejin
Ilimi.
Maryam, M.Y. (2015): "Sana'o'in Hausawa na
gargajiya da
Tasirinsu
a Zamananci". A cikin Mujallar Garkuwan Adabin
Hausa.
Gusau, S.M. da M.A.Z. Sani da wasu (Editoci).
Ahmadu
Bello University Press Limited, Zariya.
Mayanci, Y.A. (2010): "Sunayen Sarakunan
Mayanci". Gusau,
ADCAP
Press. Muhammad (2016): "Gudunmuwar Sana'ar
Ƙira Wajen
Samar da Kayayyakin Hausawa na Gargajiya",
A cikin
Argungu Journal of Language Studies Utono, K.M.
da Wasu
(Editoci) School of Language. Argungu, Adamu
Augie
College of Education.
N.T.I. (2013): "Pivotal Teacher Training
Program" Course Book on
Hausa
Language. Kaduna, National Teachers Institute.
Nafisa, U.D. (2016): "Sana'o'in Ga-aiki na Matan
Hausawa".
Kundin
Digiri na Farko, Sashen Harsunan Najeriya.
Sakkwato:
Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Nuhu, (2012): Jima a Jiya da Yau; Yanayinta da
Sauye-sauyenta a
Ƙasar
Hausa". Kundin Digiri na Farko, Sashen Harsunan
Najeriya
da na Afirka. Zariya: Jami'ar Ahmadu Bello.
Publication
Bureau.
R.M. Zarruk da wasu (1987): "Sabuwar Hanyar
Nazarin Hausa
Don Ƙananan Makarantun Sakandare na 2". Ibadan.
University
Press Plc.
Rambo, R.A. (2017): "Gudunmuwar Sassaƙa ga Bunƙasa
Tattalin
Arzikin
Hausawa da Gudunmuwar Sana'ar Noma Wajen Ha
ɓaka
Tattalin Arzikin Hausawa". Sashen Harsunan Najeriya.
Sakkwato:
Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Sulaiman da wasu (2010): "Zamantakewar a Ƙasar
Hausa; Jiya da
Yau".
Kundin Bincike na farko, Sashen koyar da Harsunan
Najeriya.
Sakkwato: Jami'ar Usman Ɗanfofiyo.
Umar, M.B. (1983): "Tasirin Tattalin Arzikin Hausawa
na
Gargajiya,
Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya. Kano.
Jami'ar
Bayero University Press
Yakasai, S.B. (2002): "Modern Comprehensive
Hausa Language"
For Senior
Secondary Schools.
SUNAYEN WAƊANDA AKA YI
FIRA DA SU
Barau Morai Mayanci, (Hira ranar 5/05/2020).
Bashiru Sani, (Hira ranar 5/05/2020).
Garba, H. Da Wasu, (Hira ranar
5/6/2020).
Halilu liman da wasu, (Hira ranar
04/05/2020).
Haruna S.N. Mayanci, (Hira ranar
28/08/2020).
[1]
Bunguɗu, A.I. da wasu (1999): "Sana'o'in kaɗi, Mazanƙwaila, Tukanen Laka
na da da na Zamani". Kundin Bincike na N.C.E. Sashen Hausa. Sokoto, Shehu
Shagari College of Education.
[2]
Maru, I.U. da wasu (2012): Sana'ar Daddawa a Jihar Zamfara". Kundin
Bincike na NCE, Sashen Hausa. Maru, Kwalejin Ilimi.
[3]
Nafisa, U.D. (2016): "Sana'o'in Ga-aiki na Matan Hausawa". Kundin
Digiri na Farko, Sashen Harsunan Najeriya. Sakkwato, Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.
[4]
Alhassan, H. Da Wasu (1982) "Zaman Hausawa". Lagos. Islamic
Publication Bureau.
[5]
B.U.K. (1981): "Rayuwar Hausawa" Morinson and Gibb Ltd, London and
Edinburgh.
[6]
Garba, U.G. (2012): "Bukukuwan Hausawa". Olfaith Prints Gusau.
[7]
Maryam, M.Y. (2015): "Sana'o'in Hausawa na Gargajiya da Tasirinsu a
Zamananci". A cikin Mujallar Garkuwan Adabin Hausa. Gusau, S.M. da M.A.Z.
Sani da Wasu (Editoci). Ahmadu Bello University Press Limited, Zariya.
[8] Dalijan, B.M. (2016): "Zamantakewar
Hausawa a jiya" A cikin Argungu Journal of Language Studies, Utono K.M. da
Sarki, A.U. da wasu (Editoci) School of Language. Argungu, Adamu Augie College
of Education.
[9]
Alhaji, Ƙ.A.L.M. Tarihin Garin Mayanci; Zamantakewa da Tattalin Arziki. (Hira
ranar Laraba 03/05/2020).
[10]
Barau Morai Mayanci, (Hira Ranar 05/05/2020).
[11]
Mayanci, Y.A.(2010): " Sunayen Sarakunan Mayanci". Gusau, ADCAP
Press.
[12]
Barau Morai Mayanci, (Hira Ranar 05/05/2020).
[13]
Bashir Sani, (Hira Ranar 05/05/2020).
[14]
Haruna S.N. Mayanci (Hira ranar 28/08/2020).
[15]
Ibrahim, M.S. (1982:7): "Tattalin Arzikin Hausawa". Cibiyar Nazarin
Harsunan Najeriya, Kano, Jami'ar Bayero.
[16]
Umar, M.B. (1983:5): "Tasirin Tattalin Arzikin Hausawa na Gargajiya,
Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya. Kano. Jami'ar Bayero.
[17]
Daliban, B.M. (2012:39): "Zamantakewar Hausawa a Jiya" A cikin
Argungu Journal of Language Studies, Utono K.M. da Sarki, A.U. da Wasu
(Editoci) School of Language. Argungu, Adamu Augie College of Education.
[18]
Kabakawa, U.B.(2012:37): "Mahangar Makaɗan Baka Dangane da Tattalin
Arzikin Hausawa. Kundin Digiri na Biyu, Sashen koyar da Harsunan Najeriya.
Sakkwato, Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.
[19] Auta, A.L.(2006:196), "Tattalin Arzikin
Al'umma da Nazarin Sana'o'i da Kasuwancin Hausawa" a cikin Algaita Journal
of Current Research in Hausa Studies. M.A.Z. Sani da Aliyu Mu'azu da Ahmadu
Shehu, (Editoci). Zariya: Ahmadu Bello University Press Limited.
[20]
R.M. Zarruk da wasu (1987): Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun
Sakandare na 2. Ibadan. University Press Plc.
[21]
Alhassan, H. Da Wasu (1982) "Zamantakewar Hausawa". Lagos. Islamic
Publication Bureau.
[22]
R.M. Zarruk da Wasu (1987): Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun
Sakandare na 2. Ibadan. University Press Plc.
[23] Maryam, M.Y. (2015): "Sana'o'in Hausawa na Gargajiya da Tasirinsu a Zamananci". A cikin Mujallar Garkuwan Adabin Hausa. Gusau, S.M. da M.A.Z. Sani da Wasu (Editoci). Ahmadu Bello University Press Limited, Zariya.
[24]
Garba, L. Mayanci, (Hira ranar 05/06/2020).
Halilu Liman da Wasu (Hira ranar 28/08/2020).
[25]
Dalijan, B.M. (2016): "Zamantakewar Hausawa a Jiya" A cikin Argungu
Journal of Language Studies, Utono K.M. da Sarki, A.U. da Wasu (Editoci) School
of Language. Argungu, Adamu Augie College of Education.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.