Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halasta Mace Ta Zauna Da Mijin Da Ba Ta So?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah ta'ala wabarakatuhu, da fatan kun tashi lafiya, tambayata ita ce shin ya halatta a addini miji ya zauna da macen da ba ta son shi? Don yanzu shekara huɗu da aurensu amma har yanzu ba ta son shi, duk abun da za ta masa tana yi ne don kar Allah ya kama ta da laifin muzguna wa mijinta, wani lokaci ma hakan na gagararta kuma kullum sai ta roƙi Allah ya ba su zaman lafiya, amma mijin ma ba ya ganin hakan, in ya tashi ya rinƙa jefar ta da munanan kalamai, don Allah ga tambayata, mafita nake nema.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu Warahmatullah, ‘yar uwa ya halasta mace ta zauna da mijin da ba ta so idan ta san za ta iya kiyaye masa haƙƙinsa na aure, saboda matuƙar mace ba ta sauke haƙƙoƙin mijinta saboda ba ta son shi, to Allah zai kama ta da wannan haƙƙi da ta ƙi bayarwa ga mijinta.

Don haka nake ba ki shawara a kan ki yi haƙuri ki ci gaba da zama da wannan miji naki tun da ga shi har kin yi haƙurin zama tare da shi na tsawon shekaru huɗu, kuma ki riƙa ba shi dukkan haƙƙoƙin aure gwargwadon iko, in Allah ya so Allah zai daidaita tsakaninku matuƙar kika ji tsoron Allah a al'amarinki.

Ayar Alƙur'ani a suratul Baƙara, aya ta 216 ta tabbatar da cewa: Za ku iya ƙin abu amma ya zamo shi ne mafi alheri a gare ku, za kuma ku iya son abu ya zamo shi ne mafi sharri a gare ku, Allah ne masani, ku ba ku da sani.

Saboda haka ki cire wa kanki wannan ƙiyayya da kike ma wannan mijin, saboda wata ƙila mijin da kika so ki aura amma Allah bai ba ki shi ba, wata ƙila shi ne mafi sharri a gare ki, sai Allah ya tausaya maki ya ba ki wanda ba shi ba, duk abin da kika ga Allah ya ƙaddara maki, to kawai ki sallama wa Allah, ki ɗauka hakan shi ne alherin, shi Allah ya san hikima da dalilin yin hakan. Kuma in kin san akwai wata kalma maras kyau, ko wata ɗabi'a maras kyau da kike yi masa, to ki ji tsoron Allah ki daina, domin wata ƙila ita ce dalilin da ya sa shi ma yake muzguna maki ba don yana da nufin yin hakan ba tun asali.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam


Post a Comment

0 Comments