Ticker

6/recent/ticker-posts

Tabon Salla a Goshi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

assalamu alaikum warahamatulahi wabarakatuhu, malam ina yi maka fatan alkairi Allah ya kara lafiya da basira, Allah kuma ya ba kasarmu zaman lafiya, ina tambaya malam, wai meye gaskiyar magana a kan abin da yake futowa mutum a goshin sa yai baki, wasu sun ce wai idan ya fito maka da yawa wai kana sallah cikakkiya, wai idan kuma kaɗan ne to sallarka ba ta cikaba, to dan Allah ina son karin bayani shin ya gaskiyar lamarin yake? Na gode Allah ya biya ku.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salám, ‘yar uwa tabon sallah a goshi ba shi ne ma'aunin gane cewa sallar mutum tana cika ko ba ta cika ba, za a iya samun wanda ke da tabon sallah amma wata ƙil da za a bibiyi sallarsa za a samu ba ta samun kamala, za kuma a iya samun wanda ba shi da tabon sallah amma kuma idan da za a bibiyi sallarsa sai a samu tana samun cikakkiyar kamala.

Saboda haka ‘yar uwa Allah ya san haƙiƙanin mai cika sallah kamar yadda Sharia ke so, da kuma wanda ba ya cikawa. Fitowar tabon sallah a gaɓoɓi ba shi ke nuna sallar mutum cikakkiya ba ce, sai dai kawai alama ce da ke nuna mutum mai sallah ne, kuma falala ce daga Allah idan an nesanci yin riya da shi.

Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Za ku iya bi ta Links ɗin mu...

TABON SALLAH: TABON SUJJADA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Me yake saka goshin mutum ya yi baƙi musamman Musulmi abunda muke kira (taɓon sallah) da hausa?

𝐀𝐌𝐒𝐀

Duk wanda yake sallah akan tabarmar roba, siminti ko carpet mai ƙarfi to fatar goshinsa zayyi baƙi saboda nauyin kansa a lokacin da yaje yin sujuda a cikin sallah

Duk wanda yake sallah akan carpet mai laushi, goshinsa ba zayyi wannan baƙin ba

Sheikh Abdulrahman Sudais shi ne shugaban masallatan Makkah da Madina kuma babban limamin masallacin harami, amma saboda yana sallah akan carpet mai laushi goshinsa bayyi wannan taɓon ba.

A taƙaice dai wannan baƙin taɓon da ke futowa a goshin mafiyawan Musulmi masu yin ibadah, alamace da ke nuna cewa; mutum yana ɗora goshinsa akan abu mai ƙarfi a lokacin yin sujuda.

Kar wani wanda yake da taɓon sallah a goshinsa ya ɗauka ya fi sauran al'umma imani da tsoron Allah.

WALLAHU A'ALAM

Alhassan Mai Lafia

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

1 Comments

  1. Assalamu alaikum malam menene hukuncin kin raba dado

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.