KISHI RAHAMA NE KO AZABA // 22

    9) TAMBAYA: Lokacin da masoyi ko maigida ya matsa da tambayar inda matarsa ko masoyiyarsa take a duk dan bayan lokaci kadan dole wani tunani ya shigo "Ina kike ne yanzu?!" Bai nufin ko tana aikata wani abin Æ™i, amma fa ya matsa mata da tambaya, a Æ™arshe duk  abin da take yi dole ta dakatar ta koma gida, in dai ya ganta shi kenan. In da a ce ita ce za ta matsa masa da tambayar inda yake nan take zai dakatar da ita, wani namijin ma tsawa zai daka mata ya ce kar ta dame shi, ba ruwanta da inda ya shiga.

    Mace na da tabbacin in maigidanta ya tafi wurin 'yan-mata ba zai taba gaya mata gaskiya ba, amma mai kishi ba za ta iya yin haƙuri ba sai ta tambaye shi. Na dai san wata mai dan abin hannunta mai kishi ce, da zarar maigidan ya fita ta dunga kira ke nan ta ji inda ya shiga. In bai daga wayar ba wani sabon tashin hankali ne na masamman. Don titsiye shi za ta yi a ƙarshe za ta tsaya kai da fata sai ya gaya mata dalilin da ya sa bai daga wayarta ba, ko ƙarya ya yi mata ta zauna. Ni shawarata anan da ta haƙura da kiransa a wajen kawai.

    Da mace za ta matsa da tambayar inda maigidanta yake wasu za su ce kishi ne, namiji bai dace ya matsa haka. Domin za a sami Æ™amshin zargi a ciki. In ya ji matarsa na biye-biye wannan daban, mataki zai dauka babba ma kuwa, in ya hana ta ba ta ji maganarsa ba sai ya sauwaÆ™e mata ko kuma kowa ya kama gabansa.  abin da ya sa aka bambanta shi namiji, kamar yadda ta sani, yana da damar Æ™ara wata matar, ita kuma kishi ya sa take Æ™oÆ™arin hanawa.

    Amma kamar mace ba ta da damar ƙara wani mijin sai in za ta yi alfahasha, tunanin haka kuwa zargi ne. Duk yadda ya kai da ƙaunarta ya yi haƙuri in ta dawo ya zaunar da ita ya karanto mata abubuwan da ba ya so, ciki har da fita waje ba tare da izininsa ba, ko zuwa wani wuri ba tare da yardarsa ba. Idan ta saba sai ya titsiye ta, kodai ya yi mata haƙuri, ko ya haƙura da ita, ko kuma ya ladabta ta. Ita kuwa ta jure in ba haka ba dayan abubuwa biyu zai faru ba shakka.

    Kodai ya hude ta da fada kuma ya taka mata burki, ko kuma ya fito firi-falo ya ce mata aure zai ƙara, ƙila kuma da yana dan jin tsoron yadda zai gaya mata, ko kuma ya ma fara tunanin zai haƙura saboda neman zaman lafiya a gidansa. Yanzu ta ba shi damar da zai gaya mata cikin sauƙi. Duk wani kishin da mace za ta yi ba zai hana namiji ya ƙara aure ba matuƙar ya yi niyyar hakan, sauƙin hali da biyayya da haƙuri sun fi hana kishiya sama da yadda kishi ke hanawa. Na ga wace ta ba ta aurarrakin da mijin yake nemowa da dama.

    A tunaninta shi ke nan tunda ta ba ta an gama, shi kuwa da ya ga yana nemowa a gidan mutunci tana batawa a ƙarshe ya je wargazajjen gida ya nemo a ka ba shi, da shirinta amaryar ta shigo don ta san komai, ita kuwa uwargidan da ta sami labarin ga yadda amaryar take sai ta yi la'asar amma ina, bakin alƙalami ya riga ya bushe, da taga ta fi ƙarfinta dole haka ta tsallake yaranta ta bar gidan. Ni ba zan ce kar mace ta yi ta bibiyar mijinta ta san inda yake ba, amma bibiyar ta zama ta kulawa ce ba ta kishi ba. Shi ma maigida in ya dawo bai ga matarsa ba yana haƙƙin ya tambayi inda take ko inda ta je, amma ba yadda zai kai ga zargi ba.

    10) SHIGA TSAKANI: Daga abubuwan dake kai mutum ga mummunan kishi har da ƙoƙarin raba wani da makusantansa, kamar 'yan uwa da abokai ko ƙawaye, dama mace kan iya yin haka ne in ta riga ta mallake mijin ta hanyoyin da suke yi kamar tsafi, ko dama auren jari aka yi, ko ta ci sa'ar yaudararsa da sunan ƙauna, ko in dama bi-ta-zaizai ne shi, in ta ga ta fi ƙarfinsa sai ta yi ƙoƙarin shiga tsakaninsa da duk wanda zai ba ta mata wannan shirin da ta yi, mutane kuma za su kalli hakan ne da sunan kishi.

    Abokai dai za su yi ƙoƙarin zuga shi ya ƙara aure, haka 'yan uwansa mata, ita kuwa za ta shiga tsakaninsa da su, yadda za ta ci gaba da zama ita kadai. Haka wasu mazan kan ƙirƙira wa kansu irin wannan kishin, su hana mace ma'amalla da duk 'yan uwanta, ba ta da ikon fita waje ko zuwa wani wuri sai dai su tafi tare, irin wunin da mata kan yi wa ƙawayensu wurin sha'anin biki ko suna sai su hana. Hatta gidan uwayenta bai yarda ta tafi ba. Na ga macen da 'yan uwanta suke ce ta zo a yi hoto ta ce "Rufa min asiri, kuna son na dawo gida bayan an cire min haƙora kenan!" Ta san halin mijinta, ba ruwansa da wani abu wai shi muharrami.

    Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.