𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaykum. Allah ya kara
wa malam lafiya da nisan kwana. Malam !tambayata malam ita ce: Mahaifiya ce da
'yarta aka samu akasi aka samu matsala sai ita 'yar take cewa za ta je ta samu
mahaifin maman nata ta fada masa abin da ya faru tsakaninta da mahaifiyar tata,
sai mahaifiyar ta ce in kin fasa zuwa Allah ya tsine miki malam mene ne
hukuncin tsinuwar? Malam kuma fa ba ta je wajen baban mamar tata ba malam, mene
ne mafita?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam, amin na gode
da wannan addu'a. ‘yar'uwa abin da wannan ɗiya ta yi kuskure ne babba, bai dace
mutum ya kai ƙarar mahaifansa ba ko da a wurin iyayen mahaifan ne, saboda yin
haƙuri da abin da iyaye suke wa mutum ya fi masa alheri duk yadda ya kai ga
rashin jin daɗin wannan abu, inda za a iya ɗaga ƙafa a kai ƙarar mahaifa wurin
iyayensu shi ne inda iyayen suke take wa ‘ya’yansu wani haƙƙi na Shari'a da ba
zai yiwu a bar abin a haka ba, ko suke saɓa wa Allah kuma aka tsoraci kada hakan
ya kai su shiga wuta, misali iyaye Musulman da ba sa kiyaye Sallar Farillah, ko
wasu haƙƙoƙin Allah makamantan haka, su ma ɗin ba kai ƙarar su za a fara yi ba,
za a yi ta nuna masu haɗarin haka ɗin ne ta hikima da girmamawa, idan ya gagara
ne sai a kai wurin waɗanda ake ganin ya dace.
Yanzu wannan tsinuwa da ta yi wa ɗiyar
ba a sani ba ko manufar tsinuwar har zuci ne ba, ko kuma a fatar baki ne kawai
don ta hana ta zuwa wurin mahaifan nata ba, to mafita a nan ita ce ta je ta ƙasƙantar
da kanta a wurin mahaifiyar ta ba ta haƙurin wannan ɓata mata rai da ta yi,
idan kuma ba za ta iya zuwa ita kaɗai ba, to ta nemi waɗanda mahaifiyar take ganin
girmansu su je tare a ba ta haƙuri, wannan shi ne mafita, kuma in Allah ya so
za ta janye wannan kalma a kan ɗiyar.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan
Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.